Connect with us

ADABI

MENE NE SANADI? Na Rabi’atu SK Mashi (10)

Published

on

Mikewa yayi daga kujerar da yake, ya dawo inda nake, gabana ya fara faduwa ganin ya zauna usa dani.
Wani irin murmushi akemun dana kasa gane fassararshi, ukar da kaina ma nayi, ina kasa hada idanuwana da nashi, saboda yayyarshi dake karuwa a cikin zuciyatah.
“Ba wani babban Abu nake so daga wurin ki ba, kiss kadai zakimun Habibatee” Wata irin razana nayi, bansan lokacin dana koma can karshen kujerar ba na zauna, muryata na rawa na ce mishi, “wanne irin kiss kuma My?” “kowanne iri kikamun ina so”“Na rantse da Allah My nidai ban iya ba” “ki cemun dai baki mun, anma wanne irin baki iya ba? A haka zamuyi auren? Karfa ki manta wannan ce alfarma ta farko dana taba nema a wurinki, idan bazakimun ba ki fada kawai”
Wallahi mamaki ne fal a zuciyata lokacin, inajin labarin wannan halayen na maza, anma ban taba tunaninsu daga wurin Yusuf ba, sai kuma wani tunani daya fadomun, kodai gwadani yakeson yi? Hakan ya saka nadan saki fara’a, “baka taɓa neman alfarma a wuri na ba My, anma meyasa zaka fara da wasa? Nidai banson wasannan plz, kuma kafin auren mu ai duk zan koyi soyayya kala-kala ne na dinga maka…”
Na karasa da er dariya ina rufe idanu, tun kafin in karasa magana naga fuskarshi ta canza, “kinga alamun ina wasa ne kenan? Ko kuwa soyayyar da kikemun ne bata kai matsayin da zakimun Kiss ba?”
Kafin in bashi amsa Khadija ta shigo da ruwa da drinks ta aje
mishi, sai da ta fita sannan ya sake kallo na, “kefa nake jira” Na matsa ina cewa, “bara dai in zuba maka ruwannan kasha, da alama yau rigima kakeji” Habiba ta saukar da ajiyar zuciya tana kallon Deen, Hannuna da nakai zan dauka Cup, ya daura nashi hannun akai, nayi saurin janye hannun nawa da niyyar kwacewa, anma bai sakeni ba, sai ma ya kara damke hannun nawa cikin nashi, yana wasa da hannun, gaba daya tsikar jikina sai tashi take, ga wani kyarma da jikina keyi, wai yau nice hannuna rike a hannun namijin da ba muharramina ba, abinda na dade ina kyamata a zuciyata, nake tir da halin duk macen da soyayya ta
rufe mata ido tayi hakan, Jikina na kyarma, na kasa hada ido dashi, “don Allah ka sakeni My, ba halinka bane wannan, kafi kowa sanin zunubin da zamu samu akan wannan”
Bai saurareni ba, yaci gaba da murza yatsun hannuna, na mike
tsaye da niyyar canja wurin zaman, ya kamo dayan hannun nawa ya zaunar dani, “ina sonki Habibatee, idan ba wurinki ba a wurin wa kikeso in nema? Don Allah karki bama soyayyarmu dalilin gurbacewarta” kai zan cewa haka My, don kaine kazomun da sabon abu, don Allah ka cikani” Na fara kokawar kwacewa, bai cikani ba, sai na kokarin canja salon da yake, Da naga da gaske yake, sai raina ya kara baci, ina kokarin kwacewa, yana kokarin kara rikmkeni, anan take fa sai muka fara rigima, har ya kwantar dani saman kujera yana a sama, ina mishi magiya, yana kalallameni da dadin baki, tsabar rainin hankali da kuma babban abun takaicin shine a gidanmu yakemun wannan abun, Da raina ya gama baci, bansan lokacin dana daga kafafuwana da
dukkan karfina ba na wuntsilar dashi gefe, ni kaina ban taba sanin ina da karfi haka ba.
Can ya fada gefen center table dake tsakar falon, kanshi harya bugu da glass din ba karamin faduwa yayi ba, Nidai tunda na samu na kwaci kaina nayi tsaye ina maida numfashi kamar wadda tasha gudu, ya tashi tsaye yanamun kallon dake nuna tsantsar bacin rai, “ni zaki yiwa haka Habiba? Akan kiss kawai? Sakayyar da zakimun kenan akan soyayyar da nake miki? An dade ana bani labarin duk son da kikemun karyane, ban taba yarda da hakan ba sai yau, da zuciyarki da bakinki duk ki rike bani so, iyakar kokarina nayi akan na baki dama, anma kin ki, kinsan mata nawa ne kemin tallar abun da ke kika kasa bani? Ki rike jikinki kinji ko, wannan abun da kikaimun, duk
abunda ya faru a gaba, kada kiga laifina, kiyi zargin kanki” Yana gama fadar hakan, ya fice fuuu ya barni, hannunshi dafe da
goshinsa. A haka nima na sulale na bar dakin.
Kusan sati daya na daina jin Yusuf, lokacin tuni na fara dana sanin abun da na mishi, wata irin soyayyarshi ce ta kara dawomun sabuwa, kullum saina tashi da shawarar kiranshi in bashi hakuri, anma na kasa, ina ta fama da soyayyarshi a raina,
Ranar daya cika sati daya da zuwa gidanmu, ina kwance kallo nake a waya da earpiece a kunne na, duk da na kure kara ina jiyo hayaniyar mutane a gidanmu, na dauka ma Ummi tayi baki, na kara lafewa donma kar tace in fita in gaishesu.
Sun dade bakinnan kafin in daina jiyo hayaniyarsu, alamun sun tafi kenan, sai ga Ummi ta shigo dakina, “kinanan kwance kina sana’ar taki baki ma san meke faruwa a gidan ba kenan?” “menene ya faru Ummi?”
“ki zo falo mahaifinki na emanki, zaki ji koma menene”
Inajin Abba ke nemana ai ba shiri na wuntsila nabi bayan Ummi, su dukansu da Alama fuskarsu babu walwala, Abba ya kalleni bayan na zauna, “Meye ya hadaki da yaronnan Yusuf?”
Na zaro idanu ina dafe kirji, “Yusuf kuma Abba? Babu abunda ya hadani dashi” “yanayin da kika shiga kwanaki biyunnan dole akwai alamun tambaya Mamana, tun dawowar yaronnan na kula da ya rage zuwa gidannan, sannan kuma yau kwatsam sai gashi da aike wai a mayar mishi da kayan aurenki daya kawo ya fasa, sauran bayani kuma mu tambayeki, shin meke faruwa ne Mamana?”
Tayaya zan fada maka tashin hankalin dana shiga daga jin wannan maganar daga bakin Abba? Na shiga firgici iyakar firgici, tashin hankalin da bazan iya misaltashi ba, iyayena ne su dukan, nasan bazasu fadamun ba gaskia ba, kuma banga alamun wasa ba a fuskokinsu, ballantana in nema su kara tabbatarmun da hakan. Kuka ne kawai ya kwacemun, da gudu na tashi na tafi dakinmu ba tare dana bama Abba amsoshin tambayoyinsa ba, Haka Ummi ta sake biyoni dakina, tana lallabani in faɗa mata dalilin daya saka Yusuf cewa ya fasa aurena, anma na kasa, ta yaya zan kalli fuskokinsu ince musu ya fasa aurena ne kawai don ya nema kiss naki mishi? Haka suka gaji da lallashi suka samun ido, karshema haushina suka koma ji, suna tunanin wani katon laifi na mishi shiyasa na kasa fadi.
A daren ranar, yanda naga rana haka naga dare, na ringa kiran wayar Yusuf da niyyar bashi hakuri, anma yaki ya daga, daga karshe ma ya kashe wayarshi, Da safe kuma naci gaba da kiran wayar kawata Fatima, don na tabbatar ita zata bani shawarar yanda zan shawo kan matsalar, duk da yanzu ta daina zuwa gidanmu, ta kuma daina kirana a waya, koni na kirata bamu dadewa muna waya zatacemun zata kirani, Yau ma sai kiranta nake ban samu ba, na tambayi Ummi zuwa gidansu ta hanani fita.
Da yamma kawai na kasa hakura, na shirya na sulale na tafi gidansu Fatima da niyyar idan ta kama ma muje ta rakani gidansu Yusuf na bashi hakuri, Tsautsayi ya fitar da ni daga gidanmu, fitar da har yau nake dana sanin yinta, nake dana sanin kinbin umarnin Ummi da tamun na hana ni fita.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: