Connect with us

RAHOTANNI

Uwargidan Gwamnan Neja Ta Yi Nasarar Zama ‘Sardaunar Zamaninmu’

Published

on

Uwargidan Gwamnan Jihar Neja, Dakta Amina Abubakar Bello ta yi nasarar lashe kambin zama ‘Sardaunar Zamaninmu’, wato (Sardauna of Our Time), bayan kwamitin da aka dora wa alhakin tantance wadda ya ko ta dace da kambin ya kammala aikinsu.
Dama dai ta yi fice a tsakanin matan gwamnonin da ke kasar nan kaf, bisa yadda take taimakon al’umma ta fuskoki da dama musamman kan abin da ya shafi kiwon lafiyar mata da yara.
Da yake masu iya magana kan ce ‘yabon gwani ya zama dole’, za mu waiwayi irin ayyukan da uwargidan gwamnan take gudanarwa wadda suka daga tutarta a kasar nan har aka yi mata taken ‘baya-goya-marayu’ kuma har ila yau ta zama ‘Sardaunar Zamaninmu’.
Ita dai Dakta Amina Abubakar Bello, kwararriyar likita ce a kan matsalolin kiwon lafiyar mata wacce take da digiri na biyu a kan kula da lafiyar jama’a, kuma ta kasance mai rajin tabbatar da ganin ‘yancin mata wajen samun cikakken koshin lafiya a bangaren haihuwa.
Ita ce ta kafa Gidauniyar RAISE, wacce ta kudiri aniyar ganin an daina samun wata ‘ya mace da ke mutuwa saboda matsalar da ta shafi daukan ciki da haihuwa. Aikin da take yi tukuru a Gidauniyar ya ba ta damar yi wa matsalolin mata kan abubuwan da suka shafi haihuwa farin sani, musamman tun daga daukar ciki, da goyon cikin da haihuwa da kuma nau’o’in cututtukan daji (cancer) na mata irin su ciwon daji na nono da mai kama mahaifa. Gidauniyarta ba ta tsaya kan kiwon lafiya ba kawai, har ila yau tana karfafa mata da matasa.
Wakazalika, ta kafa sansanoni da dama na warkar da mata masu fama da matsalar yoyon fitsari inda aka warkad da masu fama da lalaurar a Jihar Neja kawai su 226 tare da sake mayar da su su cigaba da rayuwarsu a cikin al’umma ba tare da tsangwama ba. Gagarumin aikin da Gidauniyar ta fi dukufa a kai shi ne bayar da gudunmawa wajen tabbatar da cewa mata suna haihuwa cikin koshin lafiya a asibiti. Tana gudanar da wannan kokari ne ta hanyar wayar da kai, kai dauki, horas da ungwazomomi da kuma bayar da akwatunan kayan karbar haihuwa ingantattu ga mata kyauta.
Gidauniyar uwargidan gwamnan, ba ta yi kasa a gwiwa ba inda ta bude wata katafariyar cibiya irinta ta farko a Jihar Neja domin gano wadanda suka kamu da ciwon daji na nono da na mahaifa tun kafin abin ya ta’azzara tare da yin rigakafi ga wadanda ba su kamu ba. Ta gudanar da aikin tantance kamuwa da ciwon daji na nono ga mata 3,229 da kuma kamuwa da ciwon daji na mahaifa ga mata 2,076. Gidauniyar ta taimaka wajen warkad da wadanda suka kamu da kuma taimaka wa wadanda suke bukatar kara zurfafa bincike a kansu.
Bugu da kari, uwargidan gwamnan ta mayar da hankali wajen wayar da kan al’umma game da ciwon daji ta hanyar shirya taron laccoci game da ciwon daji, da yin tattaki na musamman domin neman tallafin warkad da wadanda suka kamu da ciwon. Yanzu haka, Gidauniyarta ta shirya tsaf domin kafa kananan cibiyoyin tantance kamuwa da ciwon daji a mazabun ‘yan majalisar dattawa uku da ke Jihar Neja.
Dakta Amina Abubakar Bello tana da matukar sha’awar aiwatar da ayyukan da suke taimakon mata tare da inganta rayuwarsu kai-tsaye da kuma shirye-shiryen karfafa su da na inganta ilimin ‘ya’ya mata. Gidauniyarta ta karfafa kungiyoyin gama kai na mata da suka dukufa yin aikin gona a Jihar Neja. Gidauniyar ta samar musu da injinan sarrafa amfanin gona irin su surfe da nika.
Har ila yau, uwargidan gwamnan tare da hadin gwiwar uwargidan mataimakin shugaban kasa, Misis Dolapo Osinbajo sun horas da mata da matasa sana’o’i irin su dinki, tsara ado da sauran sana’o’in hannu masu kayatarwa, da sarrafa murjani da kayan leda.
Haka nan, Gidauniyarta tare da hadin gwiwar wasu abokan hulda sun gudanar da aikin tantance masu matsalolin kiwon lafiya a Jihar Neja kyauta, inda aka yi wa mutum 16,212 magani a kan cututtukansu daban-daban, sannan wadanda suke bukatar tiyata ko kara zurfafa bincike a kan cututtukansu da kula da su, an tura su zuwa manyan asibitoci tare da biyan kudin jinya da magungunansu.
Dakta Amina Abubakar Bello, ta gudanar da bincike-bincike da dama kan abubuwan da suka shafi kiwon lafiyar mata masu juna biyu. Ta kuma yi wasu ayyukan a kan matsalar zubar da ciki ta hanya mara kyau, hanyoyin tsarin iyali da sha’anin cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko.
Bugu da kari, ta kara inganta iliminta ta hanyar halartar kwasa-kwasai da tarurrukan bita da na kara wa juna ilimi a sassan duniya. Ta kasance mamba a Kungiyar Likitoci ta Kasa (NMA), da Kungiyar Likitocin Hakori ta MDCN, da Kungiyar Likitoci Mata ta Kasa (MWAN) da kuma Kungiyar Kwararrun Likitocin Cututtukan Mata ta Kasa (SOGON), sannan mamba ce a Kwalejin Likitocin Fida ta Yammacin Afirka.
Kasancewar masu iya magana kan ce ‘rai dangin goro..,’ uwargidan gwamnan, Dakta Amina Abubakar Bello, a yayin da ta ke hutawa, takan yi wasan wasa kwakwalwa, karanta littafai da kuma zama a cikin iyalanta. Sannan duk da dimbin abubuwan da ta ke yi a matsayinta ta matar gwamna, har yanzu takan yi aiki sau biyu a mako a Babban Asibitin Minna.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!