Connect with us

Da dimi-diminsa

A Yau Buhari Zai Kai Ziyara Kasar Ingila 

Published

on

Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina a yau Alhamis ya bayyana cewa shugaban kasa zai kai ziyara zuwa kasar Ingila, bayan ya kammala ziyararsa a garin Maiduguri duk a yau din. Adesina, ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja. Inda Adesina ya tabbatar da cewa; shugaba Buhari zai dawo Nijeriya ne a ranar 5 ga watan Mayu.

Sanarwar ta ce; bayan shugaban kasar ya kaddamar da ayyuka a jiya Laraba a jihar Legas wanda gwamnan jihar ya gudanar, an tsara shugaban kasar zai je Maiduguri a wata ziyara ta musamman, inda ake tunanin shugaban zai kaddamar da wadansu ayyuka a bangarorin lafiya, ilimi da kuma tituna. Daga nan zai zai wuce kasar Ingila domin kai wata ziyara ta musamman.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!