Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Yaro Dan Shekara 10 Ya Nutse Cikin Kududdufi A Jihar Kano

Published

on

Wani yaro dan shekara 10 mai suna Shuaibu Musa, ya nutse a cikin kududdufin da ake kira da suna Ramin Tasiu da ke kan titin Sheika cikin Kumbotso ta Jihar Kano, lokacin da ya tafi yin wanka. Kakakin hukumar kashe gobara ta Jihar, Mista Saidu Mohammed, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na kasa ranar Laraba a garin Kano cewa, lamarin ya auku ne a ranar Talata da rana lokacin da mamacin suka tafi yin wanka.

“Mun samu kiran wayar salula daga bakin Malam Abdullahi Naguru, da misalin karfe 3.15 na rana cewa, an ga gawar Musa tana yawo a cikin ruwa. “Lokacin da muka samu kiran wayar, nan take muka tura tawagar jami’anmu wurin da misalin karfe 3.30.“An ciro Musa daga cikin kududdufin mace, an mika gawarsa ga mahaifinsa mai suna Alhaji Musa Ya’u,’’ in ji shi.

Mohammed ya shawarci mutane musammam ma iyaye da shugabanni da su daina barin yara suna zuwa kududdufi, domin ceton rayukansu.

Ya ci gaba da cewa, “Haka ne, har yanzu ‘yan sanda ba su samu wani shaida a kan zargin da ake yi masa na kisan mutum bakwai kafin lokacin da fusatattun mutane suka kona shi ranar 20 ga watan Afrilun shekarar 2019. ‘Yan sanda sun kwace shi kafin daga baya ya mutu a ranar 21 ga watan Afrilun shekarar 2019,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!