Connect with us

RAHOTANNI

Hakikanin Abin Da Ya Faru Tsakanin I.G Wala Da Hukumar NAHCON

Published

on

Wannan wani rahoto ne na musamman dangane da hakikanin abin da ya wakana tsakanin Ibrahim Garba Wala, wanda a soshiyal midiya a ka fi sani da I.G Wala da Shugaban Hukumar NAHCON, Barista Mukhtar Abdullahi da hukumar alhazai ta kasa.
Da yawan mutane sun dauka cewa, an yi amfani da karfi ne a kan Ibrahim Garba Wala (IG Wala), wanda a hakikanin gaskiya kuma ba haka bane. Domin lamari ne mai cike da sarkakiya wanda ke bukatar a fayyace shi a bayyane domin tantancewa tsakanin mai gaskiya da marar gaskiya.
Wannan rahoto ne da zai yi ninkaya cikin hakikanin dambarwar. Wanda a ka tattaro dalilai daga bangarori mabambanta, ciki har da wasu abubuwa na jawabai da I.G Wala ya wallafa a shafinsa na Facebook, wanda a ciki ya aikata zargin da ya tura shi gidan yari. Haka kuma za mu bibiyi wasu rubuce-rubuce da a ka yi, wadanda ke dauke da hujjojin da mai karatu zai so karantawa don ya karu.
Yadda Lamarin Ya Faro
A ranar 26 ga watan Satumbar 2017 ne Ibrahim Garba Wala (I.G Wala) ya wallafa a shafinsa na Facebook, wani rubutu wanda a cikinsa ya yi ikirarin cewa, Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa ‘NAHCON, Barista Abdullahi Mukhtar ya yi sama da fadin akalla naira biliyan uku a yayin gudanar da aikin sauke farali na hajjin shekarar 2017.
Ga abin da I.G Wala ya rubuta cikin harshen turanci; “Wasu takardun sirri da CATBAN ta yi tozali da su sun bayyana yadda Shugaban Hukumar NAHCON ya samu tsabar kudaden da ba su gazawa naira biliyan uku ba a bayan kammala aikin hajjin shekarar 2017.”
Wala ya ci gaba da cewa: “A binciken, CATBAN na da zimmar bin diddigin yadda NAHCON ta kashe adadin kudi Naira 97,906,500,000 (Kusan naira biliyan dari) wanda a ka samar da su ta hanyar amsar kudin hajji a kan Naira Miliyan 1.5 a hannun kowanne mahajjaci cikin mahajjata 65,271 da suka halarci aikin hajjin shekarar 2017 daga Nijeriya.
“Bisa dubi ga wadannan takardun, kamfanonin jirgi da otal sun taimaka matuka wurin bayar da na goro ga jami’an hukumar.
“Wadannan kudade yawansu ya kazanta. Domin daidaito kan turbar da gwamnatin Buhari ta doru ta yaki da cin hanci da rashawa, CATBAN na son cikakken jawabi kan yadda aikin hajjin shekarar 2017 ya gudana domin a wallafa cikin gaggawa.” Inji I.G Wala
Shahararren Dan Jaridar nan, kuma Shugaban Kamfanin kafar sadarwa na ‘Dailynigerian.com’ wato Jaafar Jaafar ne mutum na farko da ya fara tattauna wannan zargi na I.G Wala. Domin kuwa a ranar da Wala ya yi wannan ikirari a Facebook, ya ziyarci Malam Jaafar a ofishinsa da ke Abuja.
Yadda Ta Kaya Tsakanin I.G Wala Da Jaafar Jaafar
Kamar yadda Dan Jarida Jaafar Jaafar ya bayyana, a ranar I.G Wala ya ziyarci ofishinsa bayan ya wallafa wannan katoton zargi kan Shugaban NAHCON, shi kuwa a daidai wannan lokacin dan tahaliki, Barista Abdullahi yana can kasar Saudiyya domin sa ido kan tabbatar da an gudanar da aikin hajjin shekarar 2017 cikin aminci. Duk da haka, sai Jaafar Jaafar ya kira Shugaban na NAHCON a waya duk dai cikin kokarinsa na ganin an samu sasanci.
Wannan lamari ya matukar bakantawa Barista Abdullahi rai, kamar yadda Jaafar Jaafar ya bayyana. Wanda hakan har ta sa shi Shugaban na NAHCON ya ki amincewa da yin wata magana da I.G Wala, tare da bayyana cewa, zai bi hakkin kazafin da Wala ya yi mishi a kotu. Da kyar dai Jaafar ya ba Barista Abdullahi Mukhtar baki ta hanyar lallaba kan ya yi hakuri a yi sulhu ba tare da an kai ga zuwa kotu ba.

A nan ne Shugaban na NAHCON ya bayar da sharadi daya tak, na cewa, dole ne I.G Wala ya koma intanet ya janye kazafin da ya yi mishi, tare da rubutun ban neman afuwa kan zargin.
Sai dai, bayan da Jaafar ya sanar da I.G Wala yadda suka yi da shugaban na Hukumar NAHCON, kan ya janye wannan zargi da ya yi. Atafau, Wala ya jajirce kan ba zai goge zargin ba, balle a kai ga ban hakuri. A wannan daren, I.G Wala ya bar ofishin kamfanin ‘Dailynigerian’ ne cikin fushi, tare da ikirarin cewa, sai ya saki wasu sirrika masu zafi kan lamarin.
Haka kuwa a ka yi, washegari wato ranar 27 ga watan Satumbar 2017, sai abin na I.G Wala ya kara kamari. Ya ruga a guje zuwa Facebook da sabbin kazafe-kazafe. Cikin rashin gajiyawa, Jaafar ya kira I.G Wala domin ya tunasar da shi irin hadarrun da ke tattare da wannan kazafe-kazafe da ya ke ta faman yi. A maimakon ya saduda, sai ma dai zazzafan gargadi da ya yi wa Jaafar din kan ya fita harkarshi kan wannan batu.
Yayin da Jaafar Jaafar ya sanar da Shugaban NAHCON yadda ta kaya a tsakaninsa da I.G Wala, sai Shugaban na NAHCON ya ce, babu komi zai nemi hakkin kazafin da I.G Wala ya yi mishi a kotu.
Wani abu da ba kowa ya san da shi ba, dangane da wannan tataburza shi ne, a cikin wannan shekarar, Shugaban hukumar ta NAHCON ya samu tagomashin shiga cikin dakin Allah ‘Ka’abah’, inda a cikin dakin na Allah, kamar yadda ya sanar da Jaafar Jaafar, ya roki Allah da ya bi mishi hakkin kazafin da I.G Wala ya yi mishi.
A ranar 26 ga watan Oktobar 2017 ne Shugaban hukumar NAHCON, Barista Abdullahi Mukhtar ya shigar da kara kotu, inda ya nemi fansar naira biliyan daya kan kazafi da bata mishi suna da I.G Wala ya yi. Wannan ya biyo bayan kauracewar da I.G Wala ya yi wa wasikar neman janye kazafin da ya rubuta, wanda lauyan Shugaban NAHCON, Farfesa Yusuf Dankofa ya rubuta.
Abin ya yi kama da wata shiryayyar makarkashiya, domin kuwa duk da shigar da kara kotu, wannan bai hana I.G Wala da abokan burminsa ci gaba da yada karairayi da kazafe-kazafe kan Shugaban Hukumar NAHCON ba. Sun yi amfani da wata kungiyarsu mai suna CUPS wurin yada labarin karya wai Hukumar DSS ta cafke Shugaban Hukumar NAHCON domin tuhumarsa kan bayanan sirrin da I.G Wala ya fitar a kansa.
Daga cikin karyar ta su har da batun cewa, Shugaban na Hukumar NAHCON ya arce daga Nijeriya saboda EFCC na nemansa ruwa a jallo, har da kazafin wai Saudiyya ta hana shi matsuguni saboda alakar kasa da kasa da ke tsakaninta da Nijeriya, amma ya samu mafaka a Landan.
A daidai lokacin da su I.G Wala suke rubuta wadannan maganganu nasu (duk da ba su da tushe ballantana madogara), shi kuma Shugaban NAHCON ya na kan hutun shekara da kowanne ma’aikaci kan samu. Wanda kuma bayan cikan wa’adin kwanakin hutun da ya dauka, ya dawo Nijeriya. Wannan duk dai bai ishi Wala wa’azi ba, ya ci gaba da rubuce-rubucen batanci kan Shugaban na NAHCON.
Yadda A Ka Zartas Da Hukuncin Dauri Kan I.G Wala
Da yammacin ranar 15 ga watan Afrilun 2019 ne a ka zauna sauraron karar shari’a tsakanin Shugaban Hukumar NAHCON da I.G Wala. Wanda ya gudana a Babbar kotun tarayya, da ke Abuja, karkashin mai shari’a Yusuf Halilu.
Shaidun gani a kotun sun tabbatar da cewa, alkalin kotun ya yi ta dage zaman duk a kokarinsa na ganin an samu sulhu a tsakani, tare kuma da bayar da isasshen lokaci ga I.G Wala don ya harhada takardun hujjoji kan zargin da ya yi ta rubutawa a kan Barista Abdullahi Mukhtar, amma shiru, babu nadama daga bangaren Wala, babu kuma wata hujja ko da kuwa ta karya ce.
Yana da kyau mai karatu ya fahimci wani abu, alkalin ya bayar da wani gajeren hutu kafin a dawo a yanke hukunci, wanda a lokacin ya so a yi sulhu a karo na karshe, amma maimakon haka, sai I.G Wala ya haska bidiyo kaitsaye a turakarsa ta Facebook, inda ya zargi alkalin da rashin adalci. Da a ka dawo don ci gaba da zaman kotu, sai a ka ankarar da alkalin dangane da wannan bidiyo da I.G Wala ya wallafa a Facebook.
Wannan tsageranci da kokarin yi wa shari’a hawan kawara, duk da rashin hujja kan kazafin da I.G Wala ya yi wa Shugaban hukumar NAHCON – bayan alkali ya same shi dumu-dumu da laifin kazafi, karya, sharri da batanci sai ya yanke mishi hukuncin shekara 12 a gidan yari.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin I.G Wala da Barista Abdullahi Mukhtar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!