Connect with us

MAKALAR YAU

Rashin Tsaro Tushen Asara: Hare-haren ‘Yan Fashi Da Mafarin Boko Haram

Published

on

Ci gaba daga makon jiya
Idan mai karatu na biye, zai ga an nuna aniyar kawo wasu misalan da za su nuna irin yad da ayyukan ‘Yan Fashi a wannan Kasa ke kara jefa sha’anin tsaro cikin yanayi na ni-‘ya-su. Cigaba da samun hare-haren ‘yan fashi cikin nasara a ko wace Kasa ce kuwa a Duniya, kai-tsaye a na da hujjar dora ayar-tambaya ga masu alhakin tabbatar da tsaron Kasar, kasantuwar mummunan yanayin, na bayuwa ne wajen jefa Dukiyoyi gami da Rayukan ‘YanKasa cikin wani hali na dardar da rashin tabbas.

1-Fashin Kan Hanyar Benin-Lagos;
Yayinda ‘yan fashin suka tare irin babbar Motar nan dake dibar Fasinjoji masu tarin yawa, sai suka rika bin Mutane daya-bayan-daya suna amshe musu dukiyoyinsu. Wani abu ma fi ta da hankali da ya afku a wannan waje shi ne, sai a ka tattare Mutanen da ba a sami kudi a hannunsu ba wuriguda, a ka ce su jeru su kwanta kan Titi. Bayan da suka kwanta, sai a ka tsara Direban Motar da bindiga aka ce ya bi ta kan wadannan Fasinjoji dake kwance bisa titi. Hakan kuwa aka yi, aka bi su da Motar aka tattake. Laifinsu shi ne, an zo za a yi musu fashi, amma abin haushi, sai ya kasance ‘Yanfashin ba su sami wasu kudade a hannunsu ba.
(Sahara Reports, March 3, 2010).
2-Fashin Garin Igarra, Edo
Ranar 10 ga Watan Agusta na Shekarar 2018 ne, kafar yada Labarai ta News 24, ta hakaito labarin wani fashi da makami da aka yi a garin Igarra na jihar Edo.
News 24 ta cigaba da fadin, Mutane 10 ne suka rasa ransu, yayinda ‘yan fashin suka kai hari wani Caji Ofis na ‘Yansanda, da kuma wasu Bankuna 2 a garin na Igarra.
Yayinda Maharan suka je Ofishin na “Yan Sanda, ba tare da bata lokaci ba sai suka bude wuta. Nan take wasu mutane biyu dake kulle a Ofishin, suka ce ga-garinku. Shi ma wani Dan Sanda guda, a nan ne ya bakunci-lahira. Sai suka yi awon-gaba da makaman Ofishin.
Suma wasu Mutane uku dake kusa da Ofishin ‘YanSandan yayin wancan hari, sun rasu nan take, sakamakon wasu harsasai da sukai batan-kai suka cim musu.
Yayinda ‘yan fashin suka dira wadancan Bankuna biyu, nan take ne suka aike da Mutane hudu zuwa Lahira, cikin su akwai abokanan mu’amala ko a ce kwastomomin Bankin.
Da wancan Caji Ofishi da kuma Motar Eriya Kwamandan ‘Yansandan, duka ‘yan fashin sun kone su ne kurmus, yayinda suka kai farmakin. Sannan, wannan ta’addanci, an yi shi ne ranar Alhamis.
3-Fashin Garin Offa, Kwara
Kamar yad da Kamfanin Dillacin Labarai na Kasa, NAN, ya labarta ga “Yan Kasa, ran 5 ga Watan Afurilu na Shekarar 2018 cewa, Mutane Talatin ne (30) aka kashe a wannan fashi na Offa.
‘YanFashin, sun sami nasarar kai wa Bankuna Bihar (5) hari ne a lokaci guda, 4:30 na yamma. Bankunan, na nan ne dab da Kasuwar Owode dake Karamar Hukumar Offa ta jihar Kwara. Sannan, sai da Maharan suka yi tsawon awanni hudu (4) suna barin-wuta a lokacin farmakin. Sun ragargaza Bankunan, kuma sun bar mutane da daman gaske kwance cikin jini.

An fadi cewa, ‘yan fashin, sun yi awon-gaba da tarin Miliyoyin Nairori. Cikin mutum 30 da ‘Yanfashin suka hallaka, tara 9 “Yan Sanda ne.
Cikin Mutanen da Channels Telebision suka tattauna da su, akwai masu cewa, irin wannan mummunan fashi da makami da aka tafka, na neman zama tamkar wata zaunanniyar al’ada a garin, domin kuwa, duk bayan Shekaru Bihar (5) ake dibga FASHI irinsa a garin. Shi ma wannan mummunan fashi, an yi shi ne ranar Alhamis.
Babu shakka, mai karatu ma na da tarin misalsalai da ya gani ko ya karanta ko aka fada masa game da tsantsar rashin imani da ‘yan fashin ke nunawa, yayinda suke aikata fashin. Tambayoyi;
i-Yanzu za a cigaba da tsintar-kai cikin irin wannan mummunar ta’ada ta fashi da makami dake neman zama ruwan-dare-game-duniya?
ii-Afkuwar fashin akai-akai, na nuna samun kyautatuwar tsaro ne a Kasa ko akasin haka?
iii-Ashe al’uma ba su da hakkin a kare Dukiyoyinsu da Rayukansu da Mutuncinsu a Kasa?
ib-Wane yunkuri ne gwamnatoci ke yi a jiya da yau, wajen magance ta’adar fashi da makamin?.
b-Da fashin ke afkuwa a ranar Alhamis-Alhamis, shin, jami’an tsaro ba su zurfafa tunani game da ranar ta Alhamis ba?
bi-Me ke haddasa ta’adar fashin ne a Kasa?
bii-Yaya za a yi a magance matsalar?
A can gaba, bayan kammala rubutun, za a amsa tambayoyi biyu na karshe In Sha Allah.
Mafarin Kungiyar Boko Haram

“The biggest enemy of Islam is the ignorant muslim whose ignorance leads him to intolerance, whose actions destroy the true image of Islam…”
“Ma fi girman makiyi ga addinin musulunci, shi ne musulmin da yake Jahili dodadde. Sai ya zamana wannan duhun jahilci da yai masa katutu, ke fuzgar sa zuwa ga kin girmama ko kin yad da duk wata fahimtar addini da ta sha-babban da tasa.

Wasu da ake zargin ‘yan boko haram ne da sojoji suka taba kamawa

Sai aka wayigari munanan ayyukan wannan musulmi maras sani, ba sa barkata komai ga Addinin, face rugurguza yad da hakikanin koyarwarsa take a idon-duniya..”. In ji Marigayi Sheikh Ahmad Deedat.
Wannan shimfida da aka fara gabatar da ita a sama cikin Harshen Ingilishi, ta fito ne daga bakin Marigayi Shehi Ahmad Deedat. Ga fassarar kalaman da Hausa;
Ko shakka babu, wancan tsokaci da Marigayi Deedat ya yi, ya yi kwabo-da-kwabo da halin da Musulmin Duniya ke zaune cikinsa a yau. Kusan kowane Musulmi na ganin;
i-Yad da ya fahimci Addini, babu dadi babu ragi, dole duk mai son shiga Aljanna, fahimtarsa ta yi daidai da tasa.
ii-Duk ingancin wani karatu, muddin ba ya jin sa na fitowa daga bakunan Malumansa, to wannan ILMI yasasshe ne.
iii-Bai damu da duk wata hujja da zai ji a na kafawa ba, ya fi damuwa da ya ji, shin, wai mai yin maganar, MECECE AKIDARSA?.
Ib-Duk cikar Duniya da batsewar ta, babu wasu Malamai da suka kai Malamansa ILMI.
b-Yawancin lokuta, tunaninsa, ba shi ne, Allah Ya shiryi wadanda yake yi wa kallon tababbu ba ne samsam. Babban burinsa shi ne, Allah Ya gaggauta shafe su daga doron kasa Ya je Ya azabtar masa da su. Allah-wadan mushen tunani!!!!!!!
Tsokacin da ake son yi game da lamarin Kungiyar Boko Haram shi ne, duk wanda akidarsa ba irin tasu ce ba, zai gamsu da cewa, aikace-aikacen Kungiyar, na kara tabarbarar da sha’anin tsaro ne a Najeriya. Mu kuma gashi wanda ke biye da wannan fili mai taken, “Rashin Tsaro Tushen Asara” ya san mun tasamma bayanai ne game da wasu halayya iri daban-daban cikin wannan Kasa, da a yau ake yi musu kallo da barazana ne ga lamarin tsaron Kasar. Misalin su; Fashi da Makami; Farauce Mutum; Ayyukan Kungiyar Boko Haram; Rikice-Rikicen Kabilanci, na Siyasa, na Bangarenci, da makamantan su.
Gabanin kutsawa cikin farfajiyar waccan Kungiya, akwai bukatar yin wani karin haske tukuna.
Shimfida da Karin Haske;
Yana da matukar muhimmancin gaske mai karatu ya sani cewa, duk wasu gungun mutane da a yau cikin Duniya za su yake shawarar rungumar makami da sunan yin wata gwagwarmaya ta Addini ce, ko ta Kabilanci, ko ta Siyasa ce, ko ta samun Abin-masarufi, ko ta Kwatar “Yancin-Kai, babu makawa, za a samu cewa;
i-Ko dai gwamnatin Kasar na dafawa gwagwarmayar.
ii-Idan kumajin, na cikin wata Kasa ce ta Afurika, za a samu cewa, ko dai wasu Kasashe cikin na Afurikar na marawa ‘YanTawayen baya ne, ko kuma a samu cewa, wasu Kasashe na Larabawa ko na Turawa ko Waninsu na mara-baya ga tafiyar.
iii-A wasu lokutan ma, a kan samu cewa, wasu Kungiyoyi da suke da manufa iri guda da su daga can uwa-duniya, kan mara-baya ga tafiyar.
ib-Sannan, a wasu lokutan, “Yan Siyasar dake adawa da gwamnati mai-ci, kan mara-baya ga irin wadannan Kungiyoyi.
Tsohon Ministan Tsaro gami da Harkokin cikin gida na Kasar Faransa daga Shekarar 1988-2000, Jen-Pierre, ya taba cewa, “…An kirkiro Kungiyar Da’esh ne, don a karasa lalata Kasar Iraki, bayan yakin da Amurka ta kaddamar a Kasar”.
Cikin rubuce-rubucen Masana, musamman Mujallar “ Current Trends in Islamists Ideology “ inda Dr AbdulBasid Kassim ya yi wani rubutu a Sifilin (Bolume) Mujallar na 21, ya tabbatar cewa, lalle kam akwai sa-hannun…(wata Kasa a yankin Gabas-ta-Tsakiya, jigo ce sannan madafa ga Musulunci da Musulmi) ta cikin ayyukan ta’addanci dake wakana a sassan Duniya.
Wasu Masanan na cewa, Littafin Durarus Saniyya fil Ajwibatin Najdiyya” wanda yake cike da zafafan fatawowi dake ishara zuwa ga kafurta Masallaci tare da tsayar masa da haddin ridda, saboda ba ya kan akida…(iri kaza), sun taimaka wajen zafafa kan irin wadancan Kungiyoyi. Dadin dadawa, yanzu haka akwai wata babbar Kasa a yankin Gabas-ta-Tsakiya, wad da ke samar da tuli na kwafi-kwafin irin wannan Littafi ta rabar da shi kyauta.
Ita ma Kungiyar Hizbullaahi, ai za a ga cewa, wata Kasa ce a nan yankin Tekun Fasha…ta kirkire ta, sannan har zuwa wannan rubutu, waccan Kasar ce mai daukar nauyin Kungiyar wajen tafiyar da ayyukanta na yau-da-kullum.
Kungiyoyi da suka zabi rungumar makami don cim ma burikansu irin su; Alka’ida; Isis; Boko Haram; Lashkare e Taiba; Taliban; Alshabbab da makamantansu, wani binciken da Sashin Addinai na Hukumar CIA ta gabatar, ta ayyana wata hamshakiyar Kasa dake a nan Gabas-ta-Tsakiya da take tallafar ayyukan irin wadancan Kungiyoyi dare da rana.
Masu Mara-baya Ga Gwamnatin Najeriya da Masu Mara-baya Ga Kungiyar Biafra, 1967-1970
Kamar yad da aka fadi a baya kadan cewa, duk wata Kungiya da a Duniya za ta rarumi makami ta farwa gwamnati ko ta farwa wata Kabila ko ta farwa mabiya wani Addini da ma sauran dalilai na son zuciya, nan da nan ne za a ga Duniya ta rabu kusan gida hudu ne zuwa sama;
i-Wasu Kasashen, za su mara-baya ne ga bangaren A.
ii-Wasu Kasashen kuwa, za su mara-baya ne ga tawagar B.
iii-Wasu Kasashen, za su raba-kafa ne wajen nuna goyon-bayansu. Ko su mara-baya ta karkashin-kasa. Sannan,
ib-Wasu Kasashen kuwa za su zabi matsayi da ake kira ne da “Yan-ba-ruwanmu.
‘…The cibil war was indeed bery costly and debastating. About four million people were killed and the Federal Gobernment edpended about $ 300 million on the war”.
(Fagge and Alabi, 2007: 1999-200).
Wadancan kalamai na sama, sun kasance wani yanki ne na Littafin, “Political And Constitutional Debelopment In Nigeria : From Pre-Colonial To Post Colonial Era”, wanda bajimin malami Farfesa Kamilu Sani Fagge da Dr Dabid Oluwatoba Alabi suka wallafa. Suna yin tsokaci ne game da talalabuwar da ta faru a Yakin Basasar da aka yi cikin wannan Kasa, daga Shekarar 1967 zuwa 1970. Ga fassarar kalaman cikin Harshen Uwa da Uba, Hausa;
“… Babu shakka, yakin basasar da aka yi cikin wannan Kasa, ya lankwame dimbin dukiyoyi da rayukan jama’a. Domin kuwa, kusan mutane miliyan hudu ne aka aike da su Lahira a yakin. Sannan, gwamnatin tarayya, ta kashe wuri-na-gugar-wuri a yakin, har kusan fan din Ingila miliyan dari uku ($300)”.
Yana da kyau mutane su fahimta cewa, a duk sa’ad da wani tashin hankali mai kama da yaki-yaki ya afku cikin kowace Kasa, sauran Kasashen Duniya a yau, abu na farko da za su fara dogon tunani a kai shi ne;
i-Wace lagwada ce za a iya warba a fitinar?
ii-Wane bangare ne cikin masu fadan, wanda goya masa baya zai fi kawo gwaggwabar riba?
Shi yasa za a ga, gwargwadon arzikin da za su warba a tashin hankali, gwargwadon karfin da za su jibge a rikicin. A dubi rikicin Iraki da Kuwait mana, a zamanin Saddam Hussaini.
Kasashen da suka marawa Gwamnatin Najeriya baya karkashin jagorancin Jamar Yakubu Gowon, sun hadar da; Egypt; United Kingdom; Sobiet Union; USA; Canada; Bulgeria; Ethiopia; Senegal; Somalia; Sierra Leone; Cameroon; Niger; Algeria; Syria da Saudi Arabia.
Daga Kasashen da suka mara-baya ga “Yan Kungiyar Biafra masu son ballewa daga Tarayyar Najeriya, karkashin jagorancin Chief Odumegwu Ojuku, sun hadar da Kasar France; Yugoslabia; China; West Germany; Israel; Portugal; Holy See; Haiti; South Africa; Rhodesia; Italy; Gabon; Ibory Coast; Tanzania da Kasar Zambia.
Marigayi Muhammad Yusuf Da Kungiyar Boko Haram
Marigayi Muhammad Yusuf ne cikin rubuce-rubuce da dama, za a iske cewa shi ne ya kirkiri ko ya samar da Kungiyar da a yanzu haka aka fi kira da Boko Haram.
Haihuwar Muhammad Yusuf
An haifi Muhammad Yusuf ne ran 29 ga Watan Janairu, Shekarar 1970 a Kauyen Girgir, Jakusko, jihar Yobe a yau. Sannan, a na dai kiran sa da Ustaz Muhammad Yusuf.
Karatun Muhammad Yusufa
Ustaz Muhammad Yusuf, ya fara karatun zaure ne, daga bisani ya je ya fadada karatunsa. Muhammad Yusuf, ya rungumi fahimtar Addini ta Salafawa ne, sai ya zama Basalafe.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa cikin yardarm Allah.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!