Connect with us

FILIN FATAWA

Yaya Kaffarar Direban Mota Da Ya Zama Sababin Mutuwar Mutane Da Yawa?

Published

on

Ci gaba daga shafi na 24

Tambaya:
Assalamu Alaikum Sheikh. Mutum ne suka yi accident (hadari) a cikin mota sai aka kai su asibiti, bayan wasu kwanaki wasu daga cikin wanda suka yi accident din suka mutu. Shin Malam mene ne matsayin direban motan?, zai yi azumi ne?; kuma idan zai yi guda nawa zai yi?, saboda ba mutun daya ne ya mutu ba. Ina fata Sheikh zai don ma amfanin ragowar musulmai masu damuwa irin wannan. Na gode Allah ya kara ilimi da imani.
Amsa:
To dan uwa kisan kuskure yana wajabta abubuwa guda biyu:
1. Diyya wacce dangin wanda ya yi kisan za su bayar ga dangin wanda aka kashe da kuskure, sai dai in sun yafe.
2. Kaffara, wacce zai ‘yanta kuyanga, in bai samu ba sai ya yi azumi sittin (60), kamar yadda aya ta 92 a Suratun Nisa’i take nuni zuwa hakan.
Idan sama da mutum daya suka mutu a mota, ya wajaba ga Direban motar ya yi wa kowa kaffara kuma danginsa su biya diyya, mutukar shi ne sababi a hadarin, kamar ya zamana ya wuce danja ko kuma ya yi gudun da ya zarce ka’ida, ko burkinsa ya lalace amma ya ki gyarawa, ko wani abu makamancin haka wanda yake nuna sakacin Direba, ko wuce ka’idarsa.
Idan hatsari ya faru wasu suka ji ciwo saboda sakacin Direba ko wuce ka’idarsa, sai suka mutu daga baya, danginsa za su biya diyyarsu kuma zai yi wa kowa kaffara, ko da kuwa bayan shekaru biyar ne da faruwar hatsarin, saboda duk dalilin da yake kaiwa zuwa abu, to yana dadidai da abun.
Don neman Karin bayani duba: Al’inaya 1\116, Madalibu Uli-Annuhaa 6\147 da kuma Fataawa Allajnah Adda’imah 23\352.
Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (20)
Tambaya:
Assalamu alaikum, Allah ya taimaki mallam,Tambayata itace, mutum ne ya mutu yabar yaya hudu, uku mata daya namiji,da kuma matarsa daya, yakuma bar gidaje biyu da gonaki, ya rabon gadonsu zai kasance?

Amsa:
Wa alaikum assalam, za’a raba duka dukiyar da ya bari gida takwas, a bawa matarsa kashi daya, ragowar a bawa ‘ya’yan nasa hudu, su raba a tsakaninsu, namiji zai dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani.

Hukuncin Tsotson Farjin Mace Yayin Saduwa
Tambaya:
Assalamu alaikum, M. Na kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.
Amsa:
To ‘yar’uwa hakan ya halatta, ba matsala a shari’ance, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Malik, sai dai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa: a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya.
Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta: 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.
Allah ne mafi sani.
Duba: Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul Khalil 3\406.

Ingancin Auran Wadanda Ba Musulmi Kafin Sun Musulunta
Tambaya:
Assalamu alaykum, don Allah ina son a Tambaya min malamai wannan Tambaya: Wani bawan Allah ne ya musulunta shi da iyalan sa ta dalili na, kuma ni na basu kalmar shahada. Su na da yara manya da kanana, sai suka tambaye ni ya ya matsayin auren su nace auren su na nan kamar yadda shariar musuluncinta tsara, sai yace min to yaya matsayinya`yan su? To gaskiya wannan ne ban sani ba shine nake son a mika min wannan Tambaya ga malam, Allah ya taimaka amin.

Amsa:
Wa’alaikum assalam, To ɗan’uwa auran da kafurai suka yi kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi shi akan ƙa’idoji da sharuɗan da suka yarda da su na auratayyarsu, saboda Annabi ﷺ bai canza auran kafiran da suka musulunta ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda da ‘ya’yayansu da suka haifa ta hanyar wancan aure. Sahabban Annabi ﷺ da yawa an haife su ne ta hanyar auratayyar zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da dangantakarsu zuwa iyayansu, wannan ya sa duk ɗan da kafurai suka haifa ta hanyar aure za mu danganta shi zuwa iyayansa bayan sun musulunta.
In kafirai suka yi zina suka haifi Ɗa ba za’a danganta shi zuwa baban sa ba bayan ya musulunta.
Don neman karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kuma sharhul Mumti’i 12/239.
Allah ne mafi Sani.

Yadda Ake Yin Sallah A Jirgin Sama Da Motar Haya
Tambaya:
Assalamu alaikum. Gafarta Mallam ya halatta yin Sallar Farilla a cikin Mota/jirgin Sama da na Ruwa? domin wa su lokutan Mutum ya kan yi tafiya mai nisa zuwa jahohin kudu ga lokacin Sallah ya yi ba sa Tsayawa domin ayi Sallah, sbd ma fi akasarin fasinjojin Ba Musulmai ba ne, kai har direban ma ba Musulmi bane.

Amsa:
Wa alaikum assalam To dan’uwa ya halatta ka yi sallah a jirgi ko mota, idan ya zama ba za ka sauka ba, sai bayan lokacinta ya fita, saboda fadin Allah madaukaki “Kuma Allah ya wajabtawa muminai sallah a cikin lokuta kayyadaddu” Surattunnisa’i aya ta:103.
Amma mutukar zaka iya riskar lokacinta bayan ka sauka, to ka jinkita ta daga farkon lokacinta, shi ya fi, saboda ka samu damar cika ruku’u da sujjada yadda ya kamata, hakanan idan tana daga cikin sallolin da matafiyi zai iya hada ta da ‘yar’uwarta, kamar azahar da la’asar, ko magriba da Isha, saboda za ka iya jinkirta ta farkon, ka yi ta hade da ta karshen.
Duk sallar da ka ji tsoron fitar lokacinta za ka iya yinta a jirgi ko mota gwargwadon yadda ka samu iko, don haka ya halatta ka yi nuni da ruku’u ko sujjada lokacin da kake sallah a mota, idan kuma jirgi ne mutukar ka samu damar yi a tsaye ba za ka zauna ba, sannan ka yi kokari a duka wajan fuskantar alkibla, sai in ya ta’azzara.
Annabi s.a.w. ya halatta yin sallah a jirgin ruwa kamar yadda Albani ya inganta hadisin a Sahihul-jami’i a hadisi mai lamba ta : 3777, wannan sai ya nuna halaccin yi a mota da jirgin sama, saboda dukkansu ababen hawa ne.
Allah ne mafi sani.

Shekara Daya Mijina Bai Sadu Da Ni Ba, Me Ya Kamata Na Yi?

Tambaya:
Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah ya sa mu dace. Malam don Allah ina son na san matsayin aurena, shekara daya mijina be kusance ni ba alhalin muna tare kuma dukkanin mu muna lafiya. Na gode.
Amsa:
Wa’alaikum assalam, Auranku ingantacce ne, amma zai yi kyau a kira magabatanku a tattauna matsalar, tun da saduwar ma’aurata ginshiki ne na Zamantakewar aure, wanda rashinsa yana kai ma’aurata zuwa saɓon Allah. In har ba ku cimma matsaya ba, bayan zama da magabata kina iya kai shi Kotu alkali ya muku hukunci, Saboda a musulunci bai Halatta miji ya kauracewa matarsa ba sama da wata (4) kamar yadda aya ta (226) a suratul Bakara ta tabbatar da haka.
Allah ne mafi sani.

Koyi Da Magabata Wurin Amfana Da Lokaci
Magabata sun kasance suna bada himma wajan amfana da lokacinsu, ba sa barin wani bangare na lokacin ya tafi a banza, kai wasu ko bayan gida suka shiga suna da wanda zai yi musu karatu daga waje, don kar wannan lokacin ya tafi a banza, daga cikin malamai akwai wanda ba ranar da take wuce shi bai yi wani ilimi da zai amfane shi ba, na san malamin da ya lazimci Ibnu Baaz bai taba fashi ba a darusansa a cikin shekaru ashirin da bakwai sai sau daya, Imamu shafi’i yana cewa:
Yanzu ba ya cikin asara darare su wuce ban amfana da su ba (wajan neman ilimi) kuma na kirga su a cikin shekaruna na rayuwa
Sannan kar ka jinkirta neman ilimi zuwa wani lokaci na musamman, kar ka ce sai lokaci kaza zan fara, saboda ajalinka zai iya zuwa ba ka sani ba, kamar yadda wasu mutanen suke yi idan aka yi musu maganar neman ilimi sai ya ce misali shekara mai zuwa zan fara, wannan kuskure ne saboda shekarar za ta iya zuwa da wasu abubuwa wadanda za su hana ka neman ilimin.
Kuma wadannan kwanakin, da suke zuwa su wuce ba za su taba dawowa ba, kamar yadda kowa ya sani, Hasanul Basari yana cewa (Ya kai Dan Adam ba wani abu ba ne kai illa kwanaki, duk lokacin da kwanaki su ka tafi, to wani bangarenka ya tafi).
Duba hilyatu Al-auliya’a na Asfahani 2\147.

Fatawar Rabon Gado (25)
Tambaya:
Assalamu alaikum malam rabon gadon macen da ta mutu ta bar danta da mahaifanta da mijinta, Allah yasakadaalkairi.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za’a raba dukiyar da ta bari gida: (12), mijin ya dauki kashi (3) Sai uwa a bata kashi (2), Uba ma zai dau kashi (2), ragowar kashi (5) din sai a bawa dan da ta bari.
Allah ne mafi sani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!