Connect with us

ADABI

Asadul Muluuk (40)

Published

on

Naasirul-haamidi Sarki ne da ya fito daga yankin Igreek, wanda dattijo ne mai dattaku da yakana ga nutsuwa, shi ne ya taso ya tare shi ya zaunar da shi, ya na rarrashinsa. “Haba ranka ya dade, ai bai kyautu a yi haka ba, nan fa duk bakinka ne, kuma duk ‘ya’yan na mu ne ba ma banbanta ko daya daga cikinsu, fusata da hayagaga ba za su maganta komai ba, ina makasudin wannan lamari? Nan ya kwashe labarin abin da ya faru ya gaya masu, sai kallo ya koma kan Al’akbar, shi ma ya ba su labarin abin da ya faru tsakaninsa da dansa, kuma har yanzu bai san halin da a ke ciki ba.
“Asadulmuluuk da Badee’atulkhairi su na son juna kuma sun amincewa juna bisa alkawarin za su yi aure, yaya kuma za a zo da wata magana daban, in dai ba kuma fitina ake son tayarwa ba?” sun je sun shirya magana a tsaninsu ba mu sani ba, mu kuma a nan mun yi magana da Addumashki na nema ma masa auren Suldaanatu kuma ya yi alkawari ya ba ni na karba masa, yanzu so ake in ce ba na so, yin haka shi ne dattaku, shi ne adalci? Ban hana shi ya auri Badee’ah ba, amma dai ai sai a fara daga kasar Dumashka ko? Ai dama hakkinmu ne mu yi musu aure bisa cancanta, to kuma duk sun dace da junansu.
Ni yanzu na bar komai a hannunku duk abin da shawara ta bayar ina goyon baya, amma kafin haka don a fidda da ni daga zargi ina son a kirawo Asadulmuluuk in yi masa wasu tambayoyi a ji daga gareshi.” Inji Al’akbar mahaifin Asadulmuluuk.
A ka yi sa’a aka same shi ya fito aka kirawo shi ya zo ya zauna, mahaifinsa ya ce; “Abdul’azim kai dana ne, ni mahaifinka ne, kuma yanzu ina cikin zargin Sarakuna abokaina, cewa ina son na hana ka auren Badee’ah, shin daga ranar da aka haife ka har ranar da muka zo kasar nan ka taba zo min da maganar aure ko da sau daya?” ya ce; “Ban taba ba.” “ Jiya da ka zo min da na tambaye ka ko ka zo min da wani albishir ne ka yi magana?” ya ce; “Ban yi ba.”
Yau shekara nawa ina yi maka magana a kan ka nemo matar aure?” “shekara biyu.” “Da na yi maka albishir na samun matar aure, ka gaya min kana da wata wadda za ka aura?” To a nan Sai Asadulmuluuk ya ce; “ Ina tsoron kada Allah ka yi fushi da ni idan na kawo wata magana sama da hukuncin da yanke, daga baya Allah ya yi fushi da ni.”
Al’akbar ya ce; “Alhamdulillahi, kun ji tarbiyyar gidana, a kullum ina gaya musu su guji fushin Allah ne, kuma na gaya masu yadda fushin Allah yake, don haka ba ni suke jin tsoro ba, Allah suke jin tsoro. “To ka sani labari ya zo mana na maganar auren ku da Badee’ah yanzu ga iyayenka za su tattauna a kai abin shawara ta bayar za su sanar da ku, amma ni da mahaifinta mun amince da aurenku sai dai ba za mu sanya baki a tattaunawar da za su yi ba, ka je mun sallame ka.”
Bayan tafiyar Asadulmuluuk a ka tabbatar da rashin laifin mahaifinsa, wasu daga cikinsu suka ba da shawara a kan tun da dai an ba shi dama a farkon marra, to kawai sai a fara gabatar da aurensa da Suldaanatu, tun da ai shi dan sarki ne bayan kamar wata biyu ita kuma Badee’ah sai ta shigo.
Wasu kuma suka ce a’a to me zai hana aura masa matan biyu a sa’i daya? sai aka ce, ba za a yi hakan ba saboda gudun fitina kada kuruciya ta shigo ciki. To sai aka tsaida magana daya kan cewa a fara aura masa Suldaanatun, kuma aka kirawo su suka zo aka yi musu bayani ba tare da an nemi shawara daga gare su ba, aka sallame su.
Soyayyarsu ta sake samun martaba da inganci, inda aka ba su wani katafaren wuri na musamman da sarki ke hutawa duk ranar Juma’a, a wannan rana da yamma Asadulmuluuk ya je can inda suka saba haduwa, yana zaune sai ga Ummu Nazifah ta shigo ta gaishe shi ta ce; “An ce in jagorance ka zuwa muhallin da za ku zauna hira.” Ya taso fuskarsa cike da damuwar wancan hukunci da aka yanke, har suka isa wurin.
Daki ne da aka yi masa ado da kujeru kawai na hutawa iri-iri, ga fitilu ma su saukin haske da kyawun launi, ya shiga ya zauna sai ya ji ya banbanta da in da suke zama a farko. “Kai Sarakunan Yamma ba za su so wani abu da ya wuce jin dadi ba, ta yaya za su so a ce yau yaki ya fuskanto su?” kalaman da zuciyarsa ke fada kenan.
Carass-carasss, shi ne sautin da ya fara ji na karar kayan ado, shaida ta farko kena da ta ke alamta masa ita ce take tafe, ko da ta sanyo kafarta ta dama cikin dakin sai ta sauke hular da ke kanta ta jikin alkyabbarta, ta mayar da mayafin kanta ta sake rufe fuska, ta kalle shi da murmushi har sai da ya ga hasken hakoranta kamar kankara, shi ma dai ya daure ya yi mata murmushin, da ta zauna sai ta lura da halin da yake ciki ta ce,
“Asadulmuluuk na fuskanci har yanzu da sauran duhu a fuskarka, ya kamata yau dai mu koma muhallinmu na farin ciki mana, kada ka tafi da bacin rai, in ka bar wurin nan da bacin rai ina kuma zan sa kaina? Ka da fa zuciyata ta saba da daukar bacin rai ya yin da ta ganka, idan ta saba da hakan to babu makawa zan dawwama cikin bakin ciki. Zan iya maganta duk matsalar da take damunka in dai ta biyo ta kaina, yi magana da abin da zuciyarka ke dauke da shi.”
“Hukuncin da Sarakuna suka yi bisa shawara ya yi tsanani, yaya za a yi a fara daura min aure da wadda ban taba ganinta ba, kuma ban taba jin sonta a raina ba? Wannan fa wani lamari ne da ya yi kama da keta haddi, me ya sa ba za ki taya ni jin wannan bacin ran ba? Shin kina goyon bayan a ce wata mace ce na fara zaman aure da ita ba ke ba? ba na kaunar ganinki cikin bacin rai ko miskala zarratin, amma wannan lamari zai ci gaba yada bacin rai a zuciyata” in ji shi.
Ta ce; “Wayyo bakin cikin dawwamar masoyi na cikin bacin rai, kaicon kwalliyar bakin ciki mai cudanye mummunan gani, alkawarinsu na yi maka auren fari ba da ni ba, ba shi ne abin dubawa ba, da kasancewa ta matar ka ta farko ko akasin haka ba shi ne nake hangowa a yanzu ba, ai ko da zan zo a ta hudu abin da nake fata shi ne in ji ance ta uku ta shiga na san nice amarya.
Kai nake so kai nake kallo a kowace fuska, kana bakin cikin a ce ba ni ce ta farko a gidan ka ba, ni kuma ina farin cikin kai ne miji na farko a gareni. Ya Asadulmuluuk ina son duk wani abu da zai biyo bayan wannan hukunci kada ka waiwaye shi balle ka bari ya bata maka rai, ya kamata mu bai wa zukatan mu hutu daga irin bakin cikin da suke kunsa.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: