Connect with us

MANYAN LABARAI

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Dauki Malaman Makaranta 867 Aiki

Published

on

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce, za ta dauki malaman makaranta dari takwas da sittin bakwai (867), ga wadanda suke da takardun gama makaranta daga cikin mutane 5,000 wadanda suke karkashin inuwar aikin wucin gadi S-Power.
An gabatar da shirin S-Power a shekara ta 2018 wanda yawancin malaman sun kammala karatu matakin NCE,kuma kowanne karshen wata akan biya su kudi da adadin sa ya kai N20,000 na tsawon shekaru biyu.
Malam Lawal Buhari, Shugaban kwamitin gudanarwa na majalisar cibiyar ilimi na Katsina, shi ne ya sanar da hakan a cikin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), a garin Daura ranar Asabar.
Ya ce “zamu karfi takardun malaman makaranta guda 867 domin yin aiki a matsayin malaman gwamnatin jiha na dindindin wanda zamu fara basu horo ranar Talata makon gaba. “
Shugaban hukumar ya bayyana cewa, abin farin ciki ne ga duk kanin mutanen da suke jihar, an dauki wannan aikin ne duba da yadda malaman S-Power suke iya bakin kokarin su wajen hidimtawa jihar Katsina domin samun ingantaccen ilimi.
Ya kara da cewa” gwamnatin jihar ta yanke hukuncin ne sabida rage yawan masu zaman banza da ake da su hakan zai karawa jihar daukaka a idanuwan duniya kuma zai kara dago da tattalin arzikin ta. “
A cewarsa, Gwamna Aminu Masari ya gamsu da ayyukan malaman karkashin tsarin S-Power kuma za mu dauke su aiki domin su rinka koyarwa a makarantun Firamare a fadin jihohi 34 na jihar “in ji Buhari.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!