Connect with us

SIYASA

Neja 2019: Dalilan Da Su Ka Sa Bello Ya Ci Zabe Da Kalubalen Da Ke Gabansa

Published

on

Tun bayan kammala zabukan 2015 jihar Neja ke muradin ganin an samu cigaba da samun salon shugabancin jihar da talakawan jihar suka yiwa lakabi da sunan canji. Canjin da a ka kasa samun sa ya samo asali ne akan irin guguwar karam mahaikacciya da guguwar Buhari ta kwaso a lokacin, wanda hakan yasa wasu zababbun taka rawar gani yayin da wasu tun asubahin fari ‘yar manuniya ta nuna kasawarsu wanda hakan bai rasa nasaba da rashin jituwan wasu gaggan ‘yan siyasar da ke ganin kusancinsu da gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello.
Wannan rashin fahimtar da ta taso wadda ta shafi wasu ‘yan majalisar dokokin jihar da na tarayya ya taimaka gaya wajen kawo tsaiko a kan tafiyar da harkokin gwamnati wanda yasa har wasu zababbun fitowa su bayyanawa duniya irin matsalolin cikin gida da gwamnatin jiha da jam’iyya mai mulki, inda tun a wannan lokacin tafiyar da gwamnati ya zama tafiyar hawainiya wanda ya zama duk irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashe wa da sunan aiki ba wani muhimmin aikin da za ka iya nunawa da suka lashe irin wadannan kudaden. Duk da hakan bai hana gwamnatin nuna bangarenta ga zababbun ‘yan siyasar ba wanda ta kai tsawon shekaru uku zuwa hudu da daman jama’ar jiha ba su gamsu da irin ayyukan da gwamnatin ke cewa ta yi ba musamman lokacin da ta bata tana kokarin ganin kusan dukkanin zababbun ‘yan majalisun sun zama ‘yan amshin shatan ta, a matakin da ta fi mayar da hankali musamman a lokuttan da zabukan 2019 ya gabato shi ne farauto ‘yan adawa daga wasu jam’iyyun adawa a jihar wanda wata ruwayar ta nuna cewar gwamnatin ta kashe makuddan kudi akan hakan, sai dai wani jigon adawa a jihar yace lamarin ‘yan adawa ba gaskiya ba ne, in ma an saye wasu ‘yan adawar su kan ba a basu ko sisin kwabo ba illa dai sun hango adawar ba tada wani alfanu a jihar duba da kashi tamanin da biyar cikin dari zuwa tis’in ba adawar suke ta gaskiya ba, in ma an tura su ne dan neman suna ko kuma tunanin wani zai iya zamawa gwamnatin kadangaren bakin tulu a lokacin zabe, kasancewar kashi tamanin na ‘yan siyasa a jihar tsoffin ma’aikatan gwamnatin jiha ne ko kuma daman ‘yan kwangila ne a jihar, dan haka adawar siyasa a Neja bai wani tasiri illa ka jira inda bakin alkalami ya karkata kai ma sai ka bi sahu, dan haka mu dai a jihar nan ko ba a bada kudi ba ma mafi yawan ‘yan takarar mu ba da gaske suke takarar ba kan haka ne ma yasa ba su cika mayar da hankali wajen shiga karkaru ba dan yakin neman zabe sai ‘yan kalilan dinsu.
Ke nan idan mun ce siyasar jihar Neja tamkar direba ne da fasinjoji, domin akwai wasu gungu da ke gefe su ke juya komai yadda suke muradi kan haka tsarin karba-karba ya gagari rushewa a jihar, domin in ban da irin wannan tsarin akwai shiyyar da har rana-faduwa ba zasu taba mafarkin hawa kujerar gwamnan jihar ba, wanda hakan yasa wasu ke kallon irin wannan tsarin na daga cikin abinda ya hanawa dukkanin gwamnatocin da suka shude kasa tabuka komai, wanda suke kallon koda gwamna Abubakar Sani Bello zai sake maimaita wasu shekarun hudu akan mulki inda aka fito can za a sake komawa.
Daga cikin irin gurabun da suka zama tarnaki ga gwamnan da kasa tabuka komai shi ne gadar gaban siyasar da ya yi na kin yin biyayyar wasu zaratan siyasar jihar wanda wadanda suka samu damar kaiwa ga mulki guguwar shugaba Buhari ce ta ba su damar da ba a yi tsammani ba irin su Barista Dabid Umaru da ake takaddamar kujerar sa na majalisar dattijai da yake ikirarin cewar ya samu sahalewar dawo karo na biyu ta hanyar Automatic ticket, yayi da jam’iyyar APC a jihar ta ce ba san da hakan ba domin ta shirya zaben cikin gida inda ‘yayan jam’iyyar suka kada Baristan tare da maye gurbinsa da Alhaji Sani Musa 313 da kuri’u sama da dubu talatin da tara da yayin da shi sanatan da ke kan kujerar bai samu kuri’u koda dubu goma duk da cewar shi ma ya samu damar shiga zaben.
Irin wamnan yanayin ne yaso shafar Sanata Aliyu Sabi Abubakar mai wakiltar Neja ta Arewa inda ya tsallake da kafar dama, yayin da abokin karawar na sa kwamishinan kananan hukumomi a wancan lokacin Jikantoro da ke ikirarin samun nasarar a zaben na fidda ya amince da sake komawa kan kujerar sa ta kwamishina a jihar. Abin bai tsaya nan ba irin wannan badakalar ta shafi dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kontagora, Mariga da Wushishi, Mashegu. Hon. Abdullahi Idris Garba da ke kan kujerar da Hon. Abdulmalik Sarkin-daji da ake zargin gwamnatin ta turo shi dan karbe kujerar, irin wannan cin daddawan ne yake addabar Hon. Shehu Slow mai wakiltar kananan hukumomin Rijau da Magama wanda dukkanin su suna gaban kuliya.
Duk da wannan takaddamar da ke faruwa bai hanawa gwamnan samun saukin cin zabe karo na biyu ba, wanda masana ke ganin an yi hakan ne dan ayarda kwallon mangwaro a huta da kuda kamar yadda al’ummomin Neja ta kudu da ake cewa Zone “B” sun yi ba, domin suna ganin kada Alhaji Abubakar Sani Bello a zango na biyu tamkar dabawa cikin su wuka ne, domin suna ganin da zaran ya kammala wannan wa’adin tsarin karba-karba zai sake ba su damar sake karban ragamar mulki duk barazana da tsoron da ake ba su cewar da zaran gwamnan ya dawo kan karagar mulki zai kakkaba ga ma’aikatan gwamnatin jihar duba da irin yawan da suke da shi a aikin gwamnatin.
Wamnan burin na su na sake karban mulki bai sa sun yi kasa a guiwa ba wajen baiwa gwamnan dubban kuri’u da ‘yayan jam’iyyar PDP ke ikirarin cewar ma ba zaben aka yi a yankin ba, an dai yi anfani da sayen kuri’u tare da aringizon kuri’un a inda aka samu damar hakan. Koma da me, gwamna Abubakar Sani Bello ya samu damar samun nasarar zabe karo na biyu duk da cewar akwai korafe-,korafe a kotunan sauraren karar zabe akan yadda zaben ya gudana.
Abinda jama’ar jihar ke bukata mayar da hankali akan ayyukan raya kasa, kyautata rayuwar al’ummar jihar, samar da gurabun aiki, kula da bangaren kiwon lafiya duk da cewar yanzu gara ka ziyarci asibitocin kudi akan ziyartar asibitin gwamnati musamman ga mata masu haihuwa saboda tsada da yadda aka makance akan neman kudin shiga, sai dai wani hanzari ba gudu ba, hanya daya ce ta ragewa talakan jihar shi ne na rashin samun dai-daito tsakanin gwamnatin jiha da majalisar dokoki ta jiha saboda irin cin kashin kaji da taka ‘yan majalisar da wasu makusantan gwamnan da ake zargin sun yi a lokacin zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a baya na ganin ko ta halin kaka sai an kafa ‘yan amshin shata a majalisar.
Hakan ya baiwa shugaban majalisar daman yin fitan kutsu inda ya tsallake da kyar, yayin da mataimakinsa bayan ya tsallake siradi a babban zabe PDP ta dadashi da kasa. Zuwa yanzu dai guguwar ta samu nasarar yin awon gaba da kujerun wasu ‘yan majalisun musamman ma karamar hukumar da gwamnan ya fito inda yake da ‘yan majalisun jiha guda biyu.
Ana kyautata zaton idan sabon zubin shugabancin majalisar zai baiwa shugaban majalisar, Hon. Ahmed Marafa Guni damar dawo wa kan kujerar zai iya zamawa gwamnan tarnakin da ba zai sake samun damar murzawa yadda yaso kamar a baya ba, tun kafin zaben dai majalisar ta fara ishara akan wani makusancin gwamnan da ke kwangilar ginin sabbin ofisoshi a harabar majalisar inda ta juya akalar aikin zuwa ma’aikatar ayyuka ta jiha mai makon aikin kai tsaye daga majalisar.
Abu na biyu da jama’a ke fatar dorewarsa shi ne maganar ruwan sha inda ya zama kalubale a jihar wanda sama da shekaru goma zuwa sama har yanzu wasu kananan hukumomin jihar ba su san anfanin ma’aikatar ruwa ba a jihar, rashin hanyoyin karkara mallakin gwamnatin jiha wanda kusan ya taimaka wajen dakile harkokin kasuwanci a jihar, duk da irin tafiye-tafiyen da gwamnan ke yi zuwa wasu kasashen duniya dan nemo masu zuba hannun jari ya kare ne akan sanya a MOU, wanda jama’a na fatar ganin MOU din sun fara aikin a wannan zangon.
Wani abin yabo da yabawa ga gwamnatin a zangon farko ta fara yunkurin gyaran makarantun gaba da sakandare musamman na kimiyya mallakin gwamnatin jihar, tare da daga darajar makarantun kiwon lafiya zuwa matakin da ya dace, biyan albashi cikin lokaci ga ma’aikta ya daga darajar gwamnatin a idon ma’aikata.
Babban kalubalen da ta ke huskanta hauhawar yawaitan marasa aiki, da koma baya ga kananan kasuwanci a jihar, a zango na biyu kusan al’ummar jihar ta sanya ido ga majalisar dokokin jiha na ganin ta tursasawa gwamnatin bin kasafin kudi sau da kafa kamar yadda ta gabatar mata.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!