Connect with us

BIDIYO

Burina Shi Ne Kannywood Ta Yi Gogayya Da Sauran Masana’antun Fim Na Duniya –Afakallahu

Published

on

Babban sakataren Hukumar Taca finafinai ta jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallahu, ya bayyana cewa, babban burinsa shi ne ya kai masana’antar shirin fim ta Kannywood matakin da za ta iya gogayya da takwarorinta na kasashen duniya.

Shugaban hukumar tace-fina-finan da dab’i ya ambata wannan ne a ranar 18 ga watan afrilu 2019 a ofishinsa bayan kammala kaddamar da kwamitocin bayar da tallafi ga halattattun ‘yan masana’antar. Afakalla ya nuna matukar kishinsa ga masana’antar yadda yake bin duk hanyar da ya ga ta dace don tallafar masana’antar. A irin namijin kokarnsa ne har wannan tallafin ya tabbata.
Ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar Kano tana sane da irin matsalolin da masana’antar ke ciki kuma ta damu don ganin ta kawo karshen duk matsalolin wanda makasudin wannan taro yana ciki wato samar da kwamitin da zai bayar da rance ga masu shirya fim da duk wani abu da ya dangance shi da mawaka da marubuta. A hangenmu muna ganin kalubalen sana’ar akwai rashin kudi akwai rashin ilimi akwai rashin tsari irin na kasuwanci na zamani sannan ma akwai rashin wadatattun kayan aiki na zamani da tafiyar da su. Wadannan kalubale ne gare mu ba yanda za a yi mu zauna mu zuba wa tulin wadannan matsaloli ido a matsayinmu na jagorori sana’armu ta sami tangarda. Kuma akasarin masu wannan sana’armu matasa ne a cikin sana’ar suke ci suke sha suke ma rufawa kansu asiri da ma wani nasu. Wannan ya sa gwamnatin jihar Kano ta Maigirma Dakta Abdullahi Ganduje mai kishin al’ummarta ta ta amince da ta zama garanto don a bayar da tallafin nan don ta taimaki al’ummarta su yi dogaro da kansu.
Kudin Kyauta ne ko Bashi Kuma wa Za a Ba wa?
Wannan kudi ba kudi ne da za a bayar kyauta ba. Kudi ne da za a bayar bashi domin ta yarda za a bunkasa sana’ar. Wannan kudi kofa a bude take ga kowa, kowa ya cancanta ya karba in har dan halalin masana’antar ne kuma ya cike duk ka’idar da kwamiti da hukumar tace fna-finai da dab’I ta ambata sai wanda ba ya so.
Wanne irin Sharudda Hukumar ta Shimfida Don Karbar Wannan Kudin?
Dalilin fitar da wadannan kwamitoci har guda biyar an fitar da su ne don tabbar da tsare-tsaren karbar wannan kudin. Na farko dai sai ka cike ka’idojin hukumar tace fina-finai kama daga kan cewa kana da rijistar hukumar da dukkanin ka’idoji da hukumar ta shimfida na farko kamfaninka yana da rijistar CAC yana da rijista da hukuma da dai dukkan sharudda da aka tanada na kamfani ya zamana kamfaninka ya cika su. Wanda mafi akasarin wadanda ke wannan sana’a sun san su tunda abin da yawa ga kuma lokaci.
Akwai Sauran sharudda mu ma namu a bangarenmu ba wai daga kawo takardar nema za mu bayar da kudin take ba. A’a akwai matakai sannan sannan sai mun hada wadanda suka fara kawo wa mu tattara sannan mu ga nawa muke nema da za mu fito da shi.
Zuwa Wanne Lokaci ne Wa’adin da Wannan Kwamiti Zai Dauka na Wannan Tallafin
Mu dai mun bayar da sati biyu domin a yi gangamin na wadanda za su kawo takardunsu don neman tallafin wannan sana’ar don haka wannan bukatocin da za a bijiro da su su ne za mu ga iya lokacin. Harkar fim sana’a ce mai fadi da yawa don haka ba za mu iya kayyadewa ba illa wadanda suka zama a shirye ko da cikin karshen watan nan ne za mu iya nema kuma za mu samu da yardarm Allah.
To Marubuta ta ina Ka Ke Ganin Za a Su Shigo?
Marubuta suna cikin ‘yan halalin hukumar nan kuma muna sane da ire-iren matsalolinsu na mutuwar kasuwa da rashin sanin ina ma harkar ta dosa. Su ma kamar takwarorinsu masu sana’ar fim ne rashin samun hanyoyin kasuwanci na zamani da kayan aiki na zamani da ma rashin sabunta dabaru da karin neman ilimi kan rubuce-rubucen ne ya dankwafar da harkar. Amma da yardarm Allah muna san su ma idan suka cika dukkan sharudda suka amshi wannan tallafin za su inganta harkar rubutun har ya zamana ana jin amon rubutunsu a duk duniya maimakon takaita kasuwarsu a bata da bakin rimi da hannun dai-daikun al’umma. Duniya ta ci gaba marubuta da su ake alfahari cikin al’umma wanda fatan wannan hukuma mu ma namu marubutan su hau wannan matsayin. Don haka a shirye muke su ma marubuta mu tallafa musu ko zuwa akarshen watan nan ne in sun kawo takardunsu za su samu.
To ya Batun Ladabtarwa da Hukunci ga Wadanda Suka Kauce Ka’idar Hukumar
Babbar manufar hukumar tace fina-finai da dab’i shi ne kare martaar addininmu da al’adunmu wanda tun da aka samar da masana’antar manufar kenan kuma mu ma akan wannan muka tsiru ba mu kauce ba. Don haka hukumar tana da dokokinta da hanyoyinta na ladabtar da duk wanda ya kauce ma doka ko ka’ida. Sai dai ba yanda za a yi mu zo mu fadi wasu abubuwan ta yadda muke kama masu laifi. Sai dai mutane su sani duk wani fim kafin ya fito al’umma ta gan shi sai da ya biyo ta hannun hukumar tace fina-finai sharin yin haka karya doka ne sannan bayan an bayar da gyara in ba a yi ba shi ma laifi ne da hukumar ba za ta yafe ba sai ta dau mataki. Sannan ba wani dan kasuwa da zai sayar da fim ko mai shirya fim da zai shirya fim sai yana da rijista da hukuma kuma ya san ka’idojinmu. Amma duk wanda ya karya dokar muna daukar matak sai dai ba ma shiga kafofin yada labarai mu yayata saboda duk lokacin da muka ce fim kaza ya shiga kasuwa ba da sahalewarmu ba to fa kamar mun yi wa wannan fim talla ne don kuwa al’umma za su je su nema don ganin mene a ciki. Amma ba za a rasa wanda zai karya doka ba kuma amfanin tsara dokokin kenan in mutum ya karya doka hukunci yay i aiki a kansa. Bisa bin wadannan dokoki zai s aka ga da wahala an sami wani fim a kasuwa ba tare da an tantance shi ba.
A karshe ina yi wa wannan masana’anta fatan alheri Allah ya kara daukakata ta yi gogayya da duk takwarorinta na duniya wajen inganci da kasuwa da tsari da tsafta da tarbiyya da bin doka da oda da tafiya akan tsarin kasuwanci na zamani na karni na ishirin da daya amin.
An raba babban kwamitin zuwa kananan kwamiti guda goma don saukaka aikin tantancewar. Kwamitin sune
1. Pre- Production shugaban Kwamitin Shi ne Malam Ado Ahmad Gidan Dabino
2. Musicians Shugaban wannan kwamitin Ibrahim Ibrahiim
3. Production shugaban kwamitin shi ne Nasir B Muhammad
4. Musicians Shugaban kwamitin Malam Mudassir Kassim
5. Post production Karkashin kulawar Abdullahi Sani Abdullahi
6. Musicians Karkashin Alfazazi
7. Marketing and Distr. Karkashin shugabanta Dr Sarari
8. Musicians Tijjani Shehu
9. Edhibitation & Brodcst Alhaji Tijjani SBS
10. Musician Sani Dahiru (Boy one) Supreme counsil
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!