Connect with us

SIYASA

Gombe 2019: Dalilan Da Su Ka Sa Inuwa Ya Ci Zabe Da Kalubalen Da Ke Gabansa

Published

on

Farin jinin Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, wanda saboda shi ne Jam’iyyar APC ta karbu har ta kai ga wadansu yan takarkaru marasa kima da ba za su iya cin zabe ba suka samu nassra a mukamai daban daban saboda shi a dalilin yin APC sak wanda Sak din ne ta debo tarkace da ake kuka da su a jihohin su.
Yanzu haka da ba dan Buharin ba da tuni jam’iyyar ta zama tarihi an manta da ita amma albarka cin sa da yake yana jamiyyar shi yasa har yanzu Jam’iyyar ba ta mutu ba kuma da yawan gwamnoni da suka ci zaben da a wata janiyya ce da ba za su kai labari ba.
A jihar Gombe ma albarkacin wannan guguwar canjin ne Sabon zababben gwamnan jihar Gombe a karkashin tutar jam’iyyar ta APC Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, yaci har ya zama gwamna bugu da kari kuma da hakurin da yake da shi.
Bayan farin jinin APC a kasa yazo dai dai da a jihar Gombe an gaji da mulkin PDP saboda rashin rungumar kowa a jiki a tafi tare a kuma taimaki yan siyasa da gwamnatin Dankwambo, ba ta yi ba yasa jama’a suka gi yin jam’iyyar PDP suka jajirce wajen yin dan takarar APC Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya.
Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, mutum ne mai hakuri wanda hakurin sa ne ya kai shi ga samun nasara dan taken sa ma shi ne Nasara daga Allah domin hakurin ne ta sa ya yi takara a shekarar 2011 da 2015 yaci zabe aka hana shi aka shiga kotu daga karshe ya hakura sai yanzu a shekara ta 2019 ya sake takara a karo na uku a jam’iyyar APC din Allah ya ba shi gagarumin rinjaye kan abokin takarar sa na jam’iyyar PDP Sanata Usman Bayero Nafada da kuri’u dubu 364,179, inda shi kuwa Sanata Bayero Nafada na PDP ya sa mu kuri’u dubu 222,868 banbanci tsakanin su 141,311.
Sanata Bayero Nafada, dan siyasa ne daga tushe wanda ya fara daga Majalisar jihar Gombe ya zama shugaban Majalisa, ya zama dan. Majalisar tarayya ya zama mataimakin shugaban Majalisa yanzu haka Sanata ne a Gombe ta arewa amma bakin jinin jam’iyyar PDP ce da rashin sanin mutuncin mutane da gwamnan PDP Ibrahim Hassan Dankwambo, ya yi ne ya kara Bayero a takarar gwamna a 2019.
Bayan hakurin sa da cancantar sa yazo a lokacin da farin jinin jam’iyyar PDP ya kare dan kowa ya gaji da ita da yasa aka nemi canji kuma aka samu, domin bakin jinin jam’iyyar PDP din ne yasa hatta kujerun Sanatoci uku da yan majalisun tarayya shida APC ce ta samu a zaben yan majalisun jiha ne cikin 24 PDP din ta samu 5.
Hakurin Inuwa Yahaya ne yasa mutanen jihar Gombe suka ga dattakun sa wajen yin dubi da halayen sa na kirki da kamalar sa da irin hakurin da yake da shi din suka zabe shi amma ba cin zabe ne damuwa Ba matsalolin dake gaban sa.
An shaidi Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, da nitsuwa kuma mai magana daya ne ba ya fade fade kuma ba’a shede shi da shaye shaye ko neman mata ba kuma mutane suna da yaginin adali ne suna tsammanin adalcin nasa a lokacin da ya kama aiki idan aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekarar.
Cin zaben sabon zababben gwamna Inuwa Yahaya, ya bude wani sabon shafi na kafa tarihi wanda idan ya yi abunda ya kamata za’a dade ba’a manta da shi ba kuma hakan ne zai ba shi dama na zarcewa karo na biyu domin a tarihin Gombe shi ne gwamnan da aka dinga yanka dabbobi ana sallolin Nafila a lokacin da aka sanar da cin zaben sa saboda murnan cin zaben sa hakan tasa ake ganin idan ya kamanta zai bar tarihi mai kyau.
Daga lokacin da Inuwa Yahaya, yaci zabe jihar Gombe ko ina kaji mutane ji za kayi suna cewa Allah yasa a mora domin duk dattakun sa da kamalar da yake da ita mutane suna ganin akwai matsala domin ba lailai a more shi ba saboda jama’a suna ganin ba shi da Kyauta sai dai ana Kyauta ta tsammanin zai canja tunda yaci zabe.

Kalubalen Da Ke Gabansa A Matsayin Gwamna
Yadda zai hada kan ‘ya’yan jam’iyyar APC wajen ciyar da jam’iyyar gaba da kuma yadda za’a sake dinke barakar dake jihar domin sai ya tsaya da kafar sa sannan za’a shawo kan matsalolin dan a samu jam’iyyar ta sake cin zabe a shekarar 2023.
Kasancewar sa kwamishinan kudi na shekarar takwas a gwamnatin gwamna Danjuma Goje ya san matsaloli jihar Gombe sosai yanzu haka yasan matsalolin da ko ya hau kujerar zan san ya zai fuskance su.
Akwai kuma matsalar ruwan sha da ta addabi jihar Gombe sama da shekaru ashirin wanda wasu unguwanni a fadar jihar suna fama da matsalar da har yanzu basu da ruwan sha irin Nasarawo da Tumfure da sauran unguwanni.
Kafin zuwan Sanata Danjuma Goje ya zama gwamnan jihar Gombe, anyi fama da matsalar ruwan sha sosai wanda da Goje ya zama gwamna ne Inuwa ya Kwamishinan Kudi aka jawo ruwan Gombe daga Dadin kowa inda aka kashe wajen biliyan takwas kuma shi sabon zababben gwamna yasan yadda ake kula da ruwan da kuma nawa ake kashewa da ma unguwannin da suke bukatar ruwa.
Ta wani gefen matsalolin za su zo mass da sauki tunda anyi gwamnati da shi yasan yadda ake gudanar da mulki kasancewar sa mamba na Majalisar zartarwa kuma shi ne ke sa hannu akan duk wani kudi da za’a kashe ashe in haka ne abun ba zai zama masa sabon abu ba.
A bangaren ma’aiakatr ilimi nan ma yana da kalubale domin ma’aikatar ilimi tafi kowacce ma’aikata girma da fuskantar matsaloli dan sune suke da ma’aikata fiye da dubu uku da har yanzu fiye da shekara uku basu da albashi kuma yan jiha ne magidanta ne dole yasan zai fuskanci kalubalensu.
Sannan akwai matsala a wasu makarantu kwana a bangaren ciyarwa da samar musu da kayayyakin karatu da aka rasa dan wannan gwamnati mai karewa tayi alfaharin cewa ilimi shi ne abun alfaharin ta na farko da na biyu dana uku amma har yanzu akwai makarantu da dama da ko kujerun zama basu da shi.
Idan muka lega ma’aikatar lafiya wajen samun izinin shiga kwalejin aikin jinya da ungozoma an bar yan Gombe a baya domin Makarantar ta Gombe ce amma duk shekara masu samun izinin shiga kwalejin tsiraru ne, kuma wannan ma’aikatar ma sai ya sa ido domin akwai bangarorin da sai an inganta su kuma sai an sa ido.
Misali kamar yadda aka ce haihuwa Kyauta ga mace mai ciki har in ya kai ayi mata tiyata amma lamarin ba haka yake ba mutane na korafi sosai kuma babu magunguna a asibitin,mafi yawan likitoci suna ganin marasa lafiya a asibitocin su ne ba’a na gwamnati ba sabon gwamnan yasan haka kasancewar sa dan Gombe.
Wajen bada maganin cizon Maciji a asibiti dake garin Kaltungo sai ya tashi tsaye domin an gina cibiya ta nazarin maganin cizon saran maciji amma har yanzu da sauran rina a kana.
Idan Inuwa Yahaya, ya shiga ofis dole sai ya inganta walwalar ma’aikatan gwamnati domin akwai hakkokin su da ba sa fita saboda matsaloli nan da can wanda kungiyar gwadago ta kasa reshen jihar Gombe sun san wannan.
Idan aka zo wajen aikin jarida dole sai ya nada kwararru dan bai wa yan jarida dama suyi aikin su yadda ya dace sannan su kuma za su hada kai da gwamnati dan samun yancin yin aikin su yadda ya dace.
Sabon gwamnan yasan akwai kalubale babba a kamfanin sufuri na motocin Gombe line dan duk motocin su sun mutu kuma babban kamfani ne da yake sauwakewa talaka harkar sufuri sannan kuma hakan samar wa gwamnati kudin shiga.
A bangaren ma’akatar aikin gona ya mayar da hankali yadda za’a dinga samar wa da manoma taki akan lokaci kuma a fara shi mai sauki ya rage kudin tarakta da za’a bai wa manyan manoma haya dan ayi musu huda hakan zai taimaka sosai.
Sannan akwai manyan Jami’ar kimiyya da fasaha dake garin Kumo da kwalejin ilimi ta jihar COE dake garin Billiri da kwalejin koyon aikin shari’a dake Nafada, da kuma kwalejin koyon aikin jinya dake garin Dukku, da kuma kwalejin fasaha dake garin Bajoga, wanda dukkan su an kirkiro su ne a lokacin gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo da ake ganin anyi sune dan siyasa.
Babban kalubale ma shi ne ya zai yi da yan takarar nan takwas da suka yi takara da shi wane mukami zai basu da zai sama musu ko kuma ya zai yi da dinbim magoya bayan su dan idan yaki hada kai da su ya sa ka musu tunda sun ba shi hadin kai za’a sa mu matsala babba
Akwai matsalar kamfanin samar da hasken wutar lantarki ta JED da al’ummar jihar Gombe suke kuka da su na rashin samun wutar Yadda ya kamata ga tsananin bill da suke bai wa mutane na wutar da basu sha ba idan kagi biya duk da haka a yanke maka wutar.
Idan sabon gwamna ya sa baki a harkar wutar lantarki komai zai inganta ya kuma yi musu barazanar korar su idan basu gyara ba, za’a sa mu sauki dan ko a lokacin mulkin Goje daka take faruwa ana rasa wuta kiran manajan ya yi ya bude masa wuta sannan aka sa mu sauki.
Yanzu fa a Gombe hasken wutar lantarki fasin fasin akeyi kamar kwallon kafa idan aka baku wuta na awa biyu a wuni sai gobe kuma ko ma jibi, wanda wannan rashin wutan yakan hana masu Sana’a da wutar da kuma masu injunan nika neman taro da kwabo kuma wahala na karuwa a tsakanin al’umma.
Bayan wannan akwai matsaloli a cikin gari musamman hanyar Pantami zuwa bye pas hanyar tayi kadan ana yawan samun matsala na hatsarin ababen hawa da ta kai ga mutane suna rokon duk wanda Allah ya sa yaci zabe ya zama gwamna ya fara da ita waje fadada ta.
Akwai matsalar rabon mukamai wanda Sai Inuwa ya dage ya kuma daure kafin ya iya shawo kan wasu matsalolin saboda koda wadanda suke jam’iyyar tun tuni kowa so yake a ba shi mukami balle wadanda yan jam’iyyar PDP ne da suka sauya sheka zuwa jamiyyar ta APC kuma suka taka rawa wajen samun nasarar cin zaben sa suma so suke ayi dasu.
Har ila yau kuma wata matsalar ita ce ba zai iya gane duk kalubalen dake gaban sa a yanzu ba har sai yan kwamitocin da ya nada sun gama aikin su sun ba shi rahoton abubuwan da suka gani a dukkan ma’aikatun gwamnatin jihar da wasu bangarori na hukuma.
Sannan wajen raba mukaman siyasa kamar Kwamishinoni da masu bai wa gwamna shawara da makamantan su nan ma akwai kalubale da dole sai ya rufe ido wajen zakulo wadanda suka cancanta kafin a basu mukaman ya kuma yi taka tsantsan dan gudun samun matsala.
Sannan wata matsala dake a kasa ita ce ta yan fansho domin tsohuwar gwamnatin PDP ta Ibrahim Hassan Dankwambo, mai barin gado ta bar bashin biliyoyin naira domin yan fansho sun sha kokawa a gidajen jaridu kan rashin biyan su hakkokin su domin wasu ma da yawa yunwa da talauci ta kashe su saboda rashin biyan su balle su iya samu su dauki dawainiyar iyalan su.
A gefe guda suma manya da kananan yan kwangila a jihar suna cikin matsala saboda tun hawan gwamna Dankwambo ake da alkaluma na rashin biyan yan kwangila kudaden su domin da yawa daga cikin su sun karye.
Idan dai har gyara Inuwa Yahaya, zai yi dan shawo kan wadannan matsalolin dole sai ya ajiye wasu manyan ayyukan da aka fara ko kuma idan ya karisa su kar ya yi wasu sai ya rage wasu matsalolin dan a samu walwala a jihar Gombe in ba haka ba za’a shiga matsalar da za ta jawo ayi kuka da shi fiye da gwamnati mai barin gado.
Akwai Yara Matasa yan Marshall da aka samar wa aiki a matsayin yan kalare da suka tuba su fiye da dubu biyar da ake ganin zai kore su idan aka rantsar da shi wanda shi kuma a wasu bayanan sa a rediyo yace zai tafi da su ba zai kore su ba zai tantance su ne duk da cewa lokacin siyasa ake ciki korar su zai jawo masa bakin jinin da zai sa shi a matsala saboda Yaran sun gyaru dan abunda ake biyan su a wata ya rage sace sace da aika-aikar yan ta’adda a jihar.

Mafita
Ganin yadda ake cikin kunci na matsanancin rayuwa kasancewar sa masanin harkar kudi kuma dan kasuwa zai iya amfani da kwarewar sa wajen samar wa yan jihar mafita.
Bayan dan kasuwa ne kuma Wanda yasan harkar kudi ya taba zama kwamishinan kudi na jihar Gombe na shekara takwas yasan matsalolin jihar ya san yadda zai inganta samun kudin shigar jihar dan samar da wasu hanyoyi da jihar za ta amfana.
Yana da kyau ya rungumi kowa da kowa yan jihar su ba da shawarin su wajen ciyar da Jihar gaba domin kowa yana da rawar takawa idan aka ajiye banbancin siyasa.
Har ila yau a bangaren kananan masana’antu zai taimaka idan ya hada kai da kwararru aka samo kamfanoni dan koyawa matasa sana’oi da zai rage zaman banza samun hanyar dogaro da kai.
Kafin a samu maslaha ko mafita a duk matsalolin nan sai Inuwa ya kafa wani kwamiti da zai yi dubi akai bayan kwamitin muka mulki da yin dubi kan ayyukan gwamnati ya mika rahoton sa ko kuma a kara mu su da wannan aiki.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!