Connect with us

SIYASA

Katsina 2019: Dalilan Da Su Ka Sa Masari Ya Ci Zabe Da Kalubalen Da Ke Gabansa

Published

on

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kasance daya daga cikin gwamnonin da suka samu nasarar cin zabensu a karo na biyu da gagarumin rinjaye. Sakamakon zaben ya nuna shi ne gwamna mai ci yanzu a arewacin Nijeriya da ya fi dukkanin ‘yan takarar da suka samu nasara yawan kuri’u da kuma yake da gagarumin rinjaye tsakanin sa da abokan takarar sa a zaben da ya gudana.
Dalilai da dama na iya kasancewa sirrin da ya baiwa gwamnan damar samun nasara ba tare da wata wahala ba ba kuma da gagarumin rinjayen da ya ba abokan takarar sa tazarar kuri’u masu yawa da su ka ba shi damar lashe zabensa da gagarumin rinjaye.
Masu sharhi akan al’amurra na ganin cewa daga cikin dalilan da suka ba Masari damar lashe zabensa akwai kyawawan tsare-tsare da manufofin da ya zo da su tun hawansa karagar mulki a watan Mayun 2015 da su ka kunshi bai wa muhimman bangarori muhimmanci ganin sun ci gaba karkashin shirin sa da Katsina restoration project a turance wanda ke da nufin farfado da muhimman bangarorin da su ka durkushe domin maido da martabar jihar Katsina da a ka san ta a baya.
Bangarorin kuwa sun kunshi bangaren ilimi da lafiya da aikin gona da samar da ruwan domin noman rani da ayyukan yau da kullum a kauyuka ba birane. Kazalika, Gwamna Masari ya baiwa bangaren tsaro da cigaban mata da matasa muhimmanci domin ganin ya tafi da kowa da nufin inganta rayuwar dukkanin al’ummar jihar.
Idan mu ka dubi bangaren ilimi karkashin jagorancin Gwamna Masari a jihar Katsina zamu ga cewa abu daya ne daga cikin abubuwan masu muhimmanci inda zamu ga cewa ya gyara makarantu da dama da yawansu ya kai kimanin dubu ukku a fadin jiha tare da sanya masu kujerun zama a dukkanin azuzuwan wanda ke da nufin samar da kyakkyawan yanayi a makarantun domin koyo da koyarwa tare da rage cunkoson dalibai a azuzuwan, al’amarin dake zama babban kalubale a baya.
Duk a bangaren ilimi Gwamna Masari ya dauki sababbin malamai na din-din-din da yawansu ya kai dubu biyar tare da karfafa su da guda dubu biyar daga shirin S-Power na gwamnatin jihar Katsina dake kamanceceniya da shirin N-Power na gwamnatin tarayya da shugaba Buhari ya bullo dashi wanda hakan ke da nufin wadata makarantun firamare da isassun malamai baya ga guda 2000 da aka dauka domin tura su a makarantun sakandire.
Hakika wannan shiri ya zo da muhimmanci iri biyu. Na farko ya wadata makarantun jihar Katsina da isassun malamai, sannan na biyu kuma ya raba dubban matasa da sukai karatu da zaman banza tare da faranta masu rai su da iyayen su.
Wata nasarar a bangaren ilimin ita ce yadda gwamnan ya wadata makarantun da kayan aiki tare da karin girman malamai lokaci zuwa lokaci inda a makarantun firamaren jihar kadai an kara ma malamai sama da dubu ashirin girma a zuwan gwamnatin cikin kasa da shekara hudu.
Ko da yake dai cigaban ilimi a jihar Katsina abu ne wanda wannan takaitacciyar kasida ba za ta iya bayyanawa ba, amma dai wadannan abubuwa da muka zanta a sama zasu tabbatar da irin kulawar da bangaren ya samu a matsayin daya tilo daga cikin bangarorin da gwamnatin ta sanya a gaba wanda ko shakka babu.
A bangaren lafiya ma Gwamna Masari ya taka rawa da dama inda aka gyara manyan asibitocin dake jihar ya zuwa na zamani da a ko ina za a iya alfahari da su. Asibitocin da aka gyaran sun hada da manyan asibitocin garin Katsina da Funtua da Daura domin ganin an kula da lafiyar al’ummar jihar. Kazalika, asibitocin garin Musawa da Dutsinma da Kankia sun samu gagarumar kulawa tare da wadata su da kayan aiki.
Akwai kuma shirye-shirye karkashin ma’aikatar lafiya domin kulawa da lafiyar al’ummar jihar Katsina da suka hade da shirin ceton rayuka miliyan daya (Sabing One Million Libes) da ke kokarin kare yara daga kamuwa da cututtukan da ke halaka su.
Akwai kuma kokarin da gwamnatin tayi na inganta makarantun koyon aikin lafiya da dai sauransu. A bangaren aikin gona ma gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Masari tayi kokari da dama wajen samar da wadataccen takin zamani ga manoma da kuma samar masu da iri da magungunan feshi da kwararrun malaman malaman gona tare da basu tallafi daban domin inganta bangaren da kuma wadata kasa da abinci tare da fadada ayyukan yi daga fannin na noma a lokacin rani da damina.
Manufofin dai sun baiwa manoman kwarin gwuiwar cewa ana yi da su, al’amarin da ake ganin yasa da dama daga wannan bangaren sun jajirce domin ganin Gwamna Masari ya dawo a karo na biyu domin cigaba da kyawawan tsare tsaren da ya taho da su a wannan fanni da ya kunshi kashi saba’in na al’ummar jiha dake ganin idan suka bada goyon baya ba abinda zai hana wanda suka goya ma baya ya samu nasara.
Wani bangare da ya samu kyakkyawar kulawa daga Gwamna Masari da kuma ake ganin abin ya haifar da nasarar zabensa shine yadda ya kula da rayuwar matasa da mata inda a kullum kiransa gare su shi ne su tashi tsaye domin dogaro da kan su a duk lokacin da ya halarci taruka domin kaddamar da basu jari da tallafin sana’a inda masu sharhi suka tabbatar da cewa lallai dubban mata da matasa sun samu tallafi domin dogaro da kan su al’amarin da ake kallon dama ce ga shi Gwamnan wajen tattaro kuri’u daga wadanda ake ganin sune kashi sittin na al’ummar Jihar watau mata da matasa da ake wa kallon sune suka fi kowa yawa wajen bayar da kuri’u.
Kazalika, bangaren tsaro ya samu kulawa ta musamman karkashin Gwamna Masari ta hanyar kokarin samar da shirin sasanci tsakanin fulanin daji da manoma domin samar da zaman lafiya a tsakanin manoman da fulanin dajin dake da nufin samar da dauwamammen zaman lafiya domin bukasar tattalin arzikin al’ummar Jihar Katsina.
Bangaren sufuri da ruwan sha ma bangarori ne da suka samu kulawa ta musamman inda aka kammala ayyukan hanyoyi da dama tare da cigaba da ayyukan wasu, kazalika an kashe kudade da dama wajen ayyukan samar da ruwan sha a manyan birane tare da samar da famfunan tuka-tuka a kauyuka da dama dake fadin jihar.
Gwamnatin Gwamna Masari a kasa da shekaru hudu ta raba al’ummomi da dama daga barazanar ambaliyar ruwa karkashin ma’aikatar muhalli inda aka gina magudanan ruwa da dama a manyan birane da garuruwa da kauyukan dake fadin jihar al’amarin da ake ganin ya faranta rayukan iyali da dama da suka sha alwashin maida biki a lokacin zaben da ya gudana.
Koda yake Gwamna Masari ya taka rawa a ayyukan raya kasa da ake ganin sun inganta rayuwar al’ummar jihar da suka haifar da goyon bayan da Gwamna Masari ya samu wajen samun nasarar zabensa.
A bangaren masu sharhi akan al’amurra na ganin salon iya siyasar Gwamna Masari da iya mu’amala da jama’a da kuma kokari na daga cikin muhimman abubuwan da suka saukaka ma shi nasara a zaben da ya gudana.
Masu sharhin na ganin cewa tun kafin a buga kugen siyasa Masari ya dukufa maido yan adawa ya zuwa jam’iyyarsa ta APC har ta kai ga ya maido mafi yawan ‘yayan jam’iyyar PDP wanda take zama a matsayin babbar jam’iyyar adawa zuwa APC.
Daga cikin su kuwa har da manyan diga-digai da suka hada da babban Daraktan yakin neman zaben PDP a 2015 da tsohon kakakin majalisar jihar har sau biyu a karkashin gwamnatin PDP uwa uba da ma dan takarar Gwamnan karkashin jam’iyyar PDP a 2015 wadanda dukkanin su suka taho da magoya bayan su.
Kazalika, gwamnan ya samu nasarar maido mafi yawan tsofaffin ciyamomin kananan hukumomi da kansiloli da ‘yan majalisun jihar karkashin gwamnatin baya zuwa jam’iyyar APC wadanda dukkanin su suka yi alkawarin goya masa baya a zaben da ya gudana, al’amarin da aka kalla a matsayin alamun nasara ga Gwanma Masarin tun kafin a gudanar da zaben wanda kuma hakan ta kasance.
Al’ummar jihar Katsina su na cike da farin ciki tare da godiya ga Allah madaukaki wanda ya ba su gwarzon gwamna Rt. Hon. Aminu Bello Masari.
Ayyukan gwamnatin Dallatu a jihar Katsina a bangarori daban-daban, kama ilimi, lafiya, ruwan sha, nomad a kiwo, cigaban matasa, tsaro da sauran ayyukan cigaba wadanda al’ummar jihar Katsina suka gani a kasa ba labara ba.
A dalilin haka ne gwamna Dallatu ya zamo zabin mutanen jihar Katsina a zabe mai zuwa na shekara ta 2019.
Hakika wannan ba abin mamaki ba ne, domin Gwamna Aminu Bello Masari ya share ma al’ummar jihar Katsina hawaye tare da cika masu alkawurra da ya dauka.

Kalubalen Da Ke Gaban Gwamna Masari

Ko da yake Gwamna Masari ya taka rawa sosai a bangarori da dama domin inganta rayuwa da kuma samar da walwala ga al’ummar jihar Katsina, masu sharhi na ganin wajibi ne ga Masari ya rubanya kwazonsa wajen inganta tsaro musamman a yankunan dake fama da garkuwa da mutane da nufin shawo kan matsalar.
Kalubalen da ake ganin wajibi ne gwamnan ya tashi tsaye sakamakon jihar na iyaka da jihohin da wannan mu’amala ta fi kamari da suka hada da jihar Zamfara da kuma Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Kalubalen na biyu dake gaban Gwamna Masari shi ne baiwa mara da kunya a bangaren da ake ganin nan ne yafi kwarewa watau bangaren samar da ruwan sha.
Al’ummar jihar Katsina dai na da fatan kawo karshen matsalar ruwan sha daga gwamna Masari a fadin jihar a matsayin sa na kwararre a fannin ruwan sha kamar yadda al’ummar Nijeriya ke da fatan kawo karshen kalubalen tsaro daga shugaba buhari a fadin Nijeriya ganin cewa shi ma kwararre ne a bangaren.
Kamar dai yadda Masari ya bugi kirji a lokacin yakin neman zabe tun karo na farko na kawo karshen matsalar ruwa, al’ummar jihar sun sanya ido domin ganin alkawari ya cika.
Kalubale na gaba kuma na karshe dake gaban gwamna masari a karo na biyu a mulkin sa na karo na biyu da ke tafe shi ne fatan da al’ummar jihar ke da shi na ganin ya kewaye kan sa da mutanen kirki masu son cigaban al’umma kamar irin kallon da suke masa na mutumen kirki wanda kullum kofar sa a bude ta ke domin sauraren al’umma da kuma amsa kukan su.
Masu sharhi na fatan ganin gwamna Masari yayi garambawul a majalisar sa domin tafiya da mukarraban da sukayi dai-dai da aniyarsa domin ciyar da jihar gaba.
A wani fannin kuma sha’anin tsaro ma cima jihar Katsina tuwo a kwarya ganin irin yadda ‘yan bindiga suka addabi mutanen kananun hukumomin jihar Katsina kamar karamar hukumar da sakataren gwamnatin jihar Katsina ya fito wato Danmusa, da karamar hukumar Safana, Batsari da kuma Jibia. Wadannan dukkanin su suna fuskantar matsalolin tsaro har yau kuma nan dazukan rugu da zamfara sukayi ma kawanya.
Akwai matsalar sace-sacen jama’a da ‘yan bindiga ke yi wanda har ta kai shi kan sa gwamnan jihar bai tsira ba shi da kan sa ya bayyana hakan a gaban al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!