Connect with us

TATTAUNAWA

Tsangayar Koyar Da Aikin Jarida Ta ATAP Ta Kafa Tarihin Da Babu Irinta, Cewar HOD

Published

on

NAZIF ABBA PALI, wanda shi ne shugaban tsangayar koyar da aikin jarida a kwalejin kimiyya, fasaha da kere-kere mallakin gwamnatin jihar Bauchi, wato ATAP, a hirarsa da LEADERSHIP A YAU ya shaida cewar tsangayarsu ta samu tagomashin da take daf da dara wa kowace tsangayar kowar da aikin jarida a shiyyar arewacin kasar nan, yana mai shaida cewar yanzu haka suna da gidan rediyo da aka shakeshi da kayayyakin aiki na zamani wanda a ka samar domin koyar da aikin jarida a zahirance ga daliban kwalejin. Duk dai a hirar da su ka yi da wakilinmu, KHALID IDRIS DOYA, ya kuma tabo batun wani tarihin da suka kafa wanda kwalejince kadai ta fara samun irin wannan damar a Nijeriya, ku biyo mu sannu a hankali don jin hakan da sauran batutuwan da suka shafi tsangayar koyar da aikin jarida ta ATAP da ke Bauchi.

Masu Karatunmu Za Su So Ka Bayyana Musu Kanka?
Sunana Nazif Abba Pali Nine shugaban tsangayar koyar da aikin jarida (HOD) ta Kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin jihar Bauchi wato ‘Abubakar Tatari Ali Polytechnic, Bauchi’.

Me za ka iya shaida wa duniya kan wannan tsangayar da kake shugabanta a daidai wannan lokacin?
Alhamdullahi kamar dai yadda ka sani ne wato tsangaya ce wacce aka kirkiro da ita domin koyar da dalibai ko kuma samar da dalibai wadanda suke sha’awar aikin jarida, a kodayaushe ana samar da irin wannan tsangayar ne domin ganin ana bayar da horon da suka dace dangane da yadda ake gudanar da aikin jarida a zahirance. Kamar yadda jama’a suka sani, mu a wannan tsangayar lallai mun yi nasara kasancewar muna da shugaba haziki wanda yake kula da wannan kwalejin sosai wato Dakta Sulaiman Muhammad Lame yana da sha’awa matuka wajen ganin an samar da matasa masu son aikin jarida da tabbatar da sun kware sun gwanance a fannin da suke da muradin zama. A dangane da haka ne aka samar da dakin horo (Studio) domin koyar da dalibai aikin jarida a zahirance, baya ga wanda ake koyar musu a azuzuwa; (Studio) din muna da kusan guda biyar wadanda suke dauke da na’urori na zamani wadanda duk duniya da irin wadannan na’urorin ake amfani a yanzu, domin ganin an baiwa daliban horo na zahiri akan aikin jarida don tabbatar da kenkeshe ‘yan jarida masu cike da sanin aikin da kuma kwarewa a abun da suka koya.

A wadannan dakunan tace muryar da kuke da su har biyar a wannan kwalejin, shin kuna watsa shirye-shiryenku a cikin jihar ne ko kuma iyaka makarantar kuke sake gwajin naku?
Kamar yadda aikin jarida ya kunsa akwai koyarwa a aji da kuma koyarwa na zahiri (a aikace) kamar wanda ga na’urorin ana gwada wa daliban ga yadda ake aikin a zahirance, kuma kamar yadda na fada maka a baya a bisa sha’awa da shugaban wannan kwalejin yake da shi kan wannan sashin yanzu haka muna jiran lasisi ne kawai daga hukumar tantance yada shirye-shirye wato (NBC), domin dukkanin ka’idojin da ya kamata mu cike mun cike don za a bude gidan rediyo ne, wannan gidan rediyon idan aka bude shi a nan cikin garin Bauchi kai har ma da Jos idan muka cilla na’urarmu za su samemu kai tsaye, kuma an samar da wannan dakin watsa shirye-shiryen ne domin su daliban su samu horo na zahirance, yaro na son ya koyi aikin jarida, misali na son ya koyi aiki a gidan rediyo an kawo shi ga gidan rediyon kuma an gaya masa duniya suna jinsa ka ga kenan an fara bashi horo na yadda zai nutsar da kansa wajen gudanar da aikin jaridar yadda ya kamata. Baya ga haka, akwai dakin gudanar da aiki wadanda kamar na Talabishin wanda muke da kyamarorin da ake yayi a wannan zamanin da suka kai guda takwas, wadannan na’urorin dukka ana samar ne domin a nuna wa daliban yadda za su kwarance da gwanancewa wajen daukan horo da yadda za su gyara horo da sauransu.

A bincikenku kawo yanzu a dukkanin fadin arewa maso gabas akwai wata kwalejin kimiyya da take koyar da aikin jarida wacce take da irin wannan na’urorin da kuke da su?
Gaskiya da sauki saboda mu a bincikenmu ya nuna mana a dukkanin arewacin Nijeriya ma Kaduna Polytechnic ce kawai take da gidan rediyo nata na kanta wanda ake kira ‘Campus Radio’ wanda daliban suke amfani da shi, ba ya ga Kadpoly har yanzu ba mu ji wata kwaleji a arewa da take da gidan rediyonta ba. Amma a jami’o’i akwai, kamar ka ga a BUK Kano, jami’ar Maiduguri ma suna da shi, jami’ar Jos ma suna da gidan rediyo a cikin jami’ar, don haka wannan ci gaba ne matuka wajen koyar da ‘yan jarida aikin sosai da kuma fitar da sakamakon mai kyau. Mu nan ATAP mun yi fice sosai mu zama zakara wajen ganin muna da gidan rediyo domin koyar da dalibai aikin jaridar nan yadda ya kamata.

Akwai matsalar rashin kula da na’urori a kafafen sadarwa da muke da su; a matsayinka na shugaban wannan sashin wacce hanyoyi kake bi wajen tabbatar da kula da wadannan na’urorin?
Gaskiya dai kamar yadda abubuwan suke tafiya a kodayaushe irin wannan yana daga cikin matsalar da muke fama da shi a Nijeriya na batun rashin kula da na’urori domin tabbatar da an moresu yadda ya kamata. Mu gaskiya Alhamadullahi a wannan tsangayar muna abun da ya dace wajen kula domin muna da kwararru wadanda daman ita makarantarce ta daukesu aiki domin kulawa da wadannan na’urorin, suna kuma sanar da mu dukkanin wani abu da suka hango ko ya faru domin mu dauki matakin da ya dace a lokacin da ya dace domin ganin ana baiwa na’urorin nan kulawar da suka dace. Tun lokacin da aka kawo na’urorin nan zuwa yanzu ana amfani da su cikin ikon Allah har yanzu ana kan basu kulawar da ta dace domin ganin ba a samu gibin rashin kula da su ba.

Daga iyaka lokacin da kai ka hau wannan kujerar da muke magana da kai a kai wacce nasarori kai ka iya cimmawa kawo yanzu?
Masha Allah! Ni kafin na karbi wannan ragamar HOD a wannan tsangayar muna bayar da takardar shaidar kammala karatun Diploma (OND) ne kawai, amma bayan da na hau ko daf da zan hau shi shugaban kwalejin kimiyyar Dakta Sulaiman Lame ya yi tsayuwar daka wajen ganin an samar da amincewa da tantancewa a (National Diploma) a tsarin NBT wadanda suke kula da wannan kwalejojin duk lokacin da suka baka yardar ka gudanar ko ka bayar da takardar shaidar National Diploma sai ka dauki shekara biyu an ga kwarewarka da irin malaman da kake da su a kasa da na’urorin da kake da su a kasa na gudanar da aikin jarida kafin a baka damar gudanar da karatu mai zurfi a matakin babban Diploma (HND) amma mu cikin ikon Allah a shekarar da aka amince mana mu ci gaba da tafiyar da National Diploma saboda na’urorin da suka zo suka gani da kayyakin aikin da suka gani a wannan shekarar suka ce mu ci gaba da HND wanda ba a taba yin irin wannan ba a tarihin NBT a dukkanin fadin Nijeriya, a kanmu ne aka fara samun wannan, ka ga wannan yana daga cikin nasarar da muka samu wanda ni ina daya daga cikin wadanda suka samar da wannan ci gaban domin a daidai lokacinmu aka samu wannan babbar nasarar.
A wasu kwalejojin ma sun shafe shekara-da-shekaru suna bayar da takardar kammala Diploma amma har yanzu sun gagara samar amincewa daga NBT da su ci gaba da gudanar da HND domin ba su cika wasu sharuda da ka’idoji na NBT ba wadanda suka hada da malamai da irin wannan kayyakin aikin na koyar da aikin jarida, ka ga wannan ci gaba ne garemu.
A yanzu ni da na hau akwai tsare-tsaren da nake shiryawa, yanzu kamar batu na yanar gizo-gizo wato Social Media ko kuma ci gaba a bangaren sadarwa, domin yanzu muddin kana son ka ci gaba dole ne sai ka bayar da kokari da kulawa na musamman a bangar yanar gizo domin yanzu haka harkar da ake yi kenan, domin ko shi aikin jaridar yanzu ya fi tafiya a yanar gizo. To, ni abun da nake son yi shine na yi kokarin ganin mun samo kwararrun malamai wadanda su sun kware sosai a wannan harkar wanda muke kokarin mu ga sun bayar da horaswar da suka dace, kawo yanzu mun samar musu da dukkanin abun da suke bukata domin ganin sun koyar da yaranmu wajen ganin sun samu ilimin nan wato Online Journalism tun da yanzu shine ake yayi a duniya. Shi wannan Online Journalism din baya ga samun ilimin aikin jarida da dalibi ya yi wata hanyace ta samar masa da sana’ar yi da zai iya rike mutum a maimakon zaman jiran aiki; wannan yana daya daga cikin ababen da nake son na yi kokarin habbakawa a karkashin lokaci na.
Baya ga wannan, batun tarukan kara wa juna sani za mu yi kokarin muke tura malamai da ma’aikatan wannan tsangayar wajen tabbatar da suna mora, ina kan yin hakan kuma zan ci gaba da tabbatar da hakan duk da dai ba zan iya tura dukkanin ma’aikatana ba amma muna zaba idan wasu suka je suka dawo wasu ma sai su je wani karon domin a samu kwarewar da za a koyar yadda ya dace kuma daidai da zamani. A takaice zan ke tabbatar da samar da karin horaswa ga su kansu malamanmu da kuma sauran ma’aikatanmu domin samun samakamo mai gayar kyau wajen ci gaba da koyar da dalibai yadda ya kamata kuma daidai da zamani.

Ya za ka kwatanta mana irin da’ar dalibanka ganin cewar a wasu lokutan ana nuna daliban ‘Mass Com’ da rashin da’a?
Ni ba zan kammala wannan hirar da kai ban sanya kokari da himma daga sauran abokan aiki wato Lakcarorin da suke koyarwa a wannan sashin ba; domin gaskiya suna gayar taimakawa, ka san duk inda ka hada dan adam ba za a iya cewa ka sanya shi ya yi abun da shi baya so gaba daya ba, ba kuma zai iyu a ce dukkaninsu ka sanya gaba daya sun bi yadda kake so ba; amma dai Alhamudllahi da gudunmawar abokan aikina muna iya bakin kokarinmu wajen samar da da’a ga dalibanmu, yana ma daga cikin taken wannan makarantar ‘A-baka-tarbiyya-na-gari’, da kuma ‘Koyarwa’. Don haka muna iyaka bakin kokari wajen ganin mun bayar wa daliban wannan tsangayar ilimi da koyar musu da da’a ta yadda za su gudanar da rayuwarsu.
Yadda za ka gamsu da da’ar da dalibanmu suke samu, ba sai ka tambaya ba, yanzu idan ka shigo cikin makarantar nan tun da kofar shiga ‘Get’ su dalibanmu daban suke domin akwai tsarin shiga da dalibanmu suke yi, don su suna da tsarin shigarsu ma na daban, hakan na daga cikin kokarin da muka yi da ni da sauran ma’aikatana wajen tabbatar da mun bayar da horo na da’a da ilimi ga dukkanin daliban da suke wannan sashin na koyar da aikin jarida.

Daliban da suke koyon aiki jarida a wannan kwalejin na ATAP suna kokawa da cewar ba ku shirya musu yawon shakatawa domin karin ilimi meye sa ba za su maida hankali kan hakan ba?
Akwai bikin da muke yi duk zango guda da muke kiransa ‘MACOSA Week’ mako guda muke warewa domin ganin an wala an kuma shakata, tabbas muna jin koke-kokensu kan yawon bude ido, amma gaskiya mu mun fi son a baiwa karatun muhimmanci, kada ya zama a yi ta shirya shakatawar har su zo su shagalta da makasudin zuwansu neman ilimin, amma dai sau daya a shekara muna shirya MACOSA Week da ake gudanar da ababe daban-daban a yi shagula daban-daban daga karshe ana rufe Makon ne da zuwa dajin Yankari domin daliban su shakata amma a karkashin sanya idonmu domin gudun kada su kauce wa abun da muke a kai, muna sane da batun yawon shakatawa za kuma mu ci gaba da waiwayar wannan fannin.

Wasu irin kwasa-kwasai ne kuke koyarwa yanzu haka a wannan tsangayar da take koyar da aikin jarida a nan ATAP?
Muna koyar da ilimi a matakin Diploma da kuma National Diploma (ND) da kuma Higher National Diploma (HND) yanzu haka ma mun sake samun ci gaba wanda muke koyar da Diploma na karshen mako wanda aka samar domin ma’aikata da za su ke zuwa suna karatu a karshen mako Asabar da Lahadi su yi karatunsu wanda za a basu shaidar ND idan sun kammala.

Ita wannan kwalejin ta gwamnatin jihar Bauchi ce, yanzu wani dan jihar da ba Bauchi ba, da ke son koyon aikin jarida a nan za samu gurbin karatu a wajenku kuma ya zai yi?
Ita wannan kwalejin mallakin gwamnatin jihar Bauchi ce, amma ba wai ‘yan jihar kadai ke damar karatu a ciki ba, kowa na da damar samun gurbin karatu a ciki, amma dai ana bayar da fifiko wajen daukan ‘yan jihar amma makarantar ta kowace ga mai sha’awa.
Ga wanda ke sha’awar shiga wannan kwalejin ko wannan tsangayar, Da farko dai muna da abun da ake kira da Portal na wannan makarantar gaba daya wanda ta nan ne mutum zai cike neman gurbin karatu a ciki, bayan mutum ya shiga yanar gizo ya hau kan Portal dinmu zai yi rijista kamar yadda kowa ke yi, dukkanin bayanai na wannan tsangayar a ciki da zarar mutum ya cike zai zo garemu.

Mene ne babban fatanka a wannan kujerar da kake dale a kai?
Fatana shine na samar da Tsangayar da za ta yi fice a Nijeriya ba ma wai a ce maka a arewacin Nijeriya ba ko jihar Bauchi baki daya ba. Baya ga wannan ina fatan samar da daliban da za su zama gagara badau wadanda duk ta yadda aka taba su ba za su tabu ba. Alhamdullahi ana ci gaba, domin a kwanakin baya wasu daga Legas ma suka zo suka ce suna jin labarin wannan tsangayar tamu sun zo ne domin su gani da idonsu, muka zaga da su suka gani daga baya suka ce suna da gidan jarida da suke son na basu daliban da za su ke musu aiki na kuma basu ka ga wannan ci gaba ne, yanzu haka muna da dalibai daga Bayelsa da Delta dukka suna karatu yanzu haka a tsangayata ka ga dukka wadannan ci gaba ne alhali da wasu suna gani kamar yadda kake fada ai kwalejin jiha ce a’a kowa na da damar karatu a cikinta, mu abu ne wanda za muke alfahari da su a matsayinmu na dalibai.

Mun gode kwarai?
Ni ma na gode kwarai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!