Connect with us

MAKALAR YAU

Zabukan Kano: Ina Mafita?

Published

on

A cikin nazarin dana yi kuma na rubuta a wasu shafuka dangane da zabuka a Kano cikin shekara 20, zamu iya gano abubuwa shida a dunkule.
Na daya: ‘Yan siyasa iri daya ne, halinsu daya, tunaninsu daya a karkashin kowane nau’in shugaba. Sun nuna halinsu na kirki da rashin kirki a zamanin gwamnoni uku da suka jagoranci Kano
Na biyu: Masu mulki sun dauki zaben kananan hukumomi a jihohinsu a matsayin kayansu, shi kuma zaben cike gurbi a jihohinsu sun dauke shi a matsayin damarsu
Na uku: Yadda jagora yake na siyasa, haka mabiyansa suke. Gwamnati tana tafiya ne a bisa koyarwar jagoranta. Alkibarsa ita ce alkibla.
Na hudu: Jama’ar gari da ‘yan siyasa suna karbar sakamakon zabe da aka yi na gwamnatin tarayya a dukan falan daya ko su suka samu nasara ko su suka samu akasinta
Na biyar: Mutanen da suke fadar gwamnati da masu neman biyan wata bukata a sarari ko a boye, a dalilinsu ne ake barin mulki ko a zauna a kansa ala dole
Na shida: Da sara.da.suka da kisa da lalata dukiya, da yarfe da cin mutunci da karfa karfa sun yi kaka-gida, akasarin masu yin na farko matasa ne, na biyu ukuma iyayen gidansu

Nazari
Kano tana da tarihin siyasa na musamman a Najeriya. Siyasar da ake yi a Kano tana tasiri matuka a sauran sassan kasar nan, saboda matsayin da Kano take da shi ta fuskar tattalin arziki da rayuwa.
Duk mutumin Kano yana alfahari da ita, kuma yana jin dadi in an yi kirarin Kano ko da me kazo an fika.
Sai dai ana yin siyasa batacciya a Kano, sara da suka da kisa da lalata dukiya tun Rimi da Bakin Zuwo har zuwa yau ana yi ba a daina ba. Likkafar lamarin ma gaba ta kara yi. Mai gwamnati shi ke da mulki, kuma ya cinye du. Wannan al’ada tana damun Kanawa, abin takaici kuma maimakon ya ragu saboda an samu karuwar ilimi da wayewa da yalwar arziki, kullum sai gaba ya ke yi.
Daga cikin dalilan da suka sanya Janar Buhari da abokansa sojoji suka tankwabe gwamnatin Marigayi Shehu Shagari a shekarar 1983, akwai yawaitar harkar Banga a ko ina, har ta kai matsayin cikakkiyar matsalar tsaro a kasa.
Yau mun shekara 20 cur da mulkin farar hula a jamhuriyya ta hudu, ga shi kuma har yanzu ba a daina banga ba. Ya kamata mu kalli wannan matsala a tunkure ta don a shawo kanta.
Da akwai alamu da suke nuna tsarin democracy zai dore a kasar nan. Amma ba zai dore ba sai da zaman lafiya don shi ne ginshikin mulki na adalci. Ba za a samu zaman lafiya ba, sai an samu shugabanni da aka zabo su ta halastacciyar hanya. Sune wadanda jama’a zasu yi musu da’a ba karhanci, sannan su mara musu baya a yi mulki.
Ba za a samu shugabanni ba sai an kautar da banga, an yaketa, an yi jam’iyya don ra’ayi, an yi zabe da ‘yanci.

Hanyoyi
Za a iya gyara wadannan matsaloli a matakai iri uku. Matakai na kusa na nan take da mataskai na gajeren zango da kuma matakai da zasu dauki lokaci.
Masu yin siyasa da wadanda suke yin siyasa kullum kullum, su gane siyasa ba rashin mutunci bane, a kuma dirty game bane. Aikin al’umma ne, kuma jarumi da sadauki a cikin siyasa shi ne mai hakuri da mutunci da bin ka’ida da tsari na cikin gida na jam’iyya da tafiyar da gwamnati. Gwarzo kuma ba shi ne mai kwata da karfi ba, a’a mai karbar kaddara da sallamawa ra’ayin jama’a.
Na biyu.: A ganar da ‘yan siyasa cewa siyasa wasa ne, ba yaki bane ko a mutu ko a yi rai, abokin hamayyarka kuma ba makiyinka bane ko mahassadi ko abokin gaba ba. A’a abokin derby ne shigen irin wanda ke tsakanin Barca da Madrid ko Arsenal da Manchester, amma dukanku al’umma ce a gabanku.
Na uku: Idan ‘yan siyasa sun samu dafa iko su fahimci amana ce suka karba, a wajen samar da abokan aiki a dauki hazikai, masana, masu kishi ba ‘yan maula ko banbadanci ba, masu kewaye shugaba da karya da dora shi akan abin da yake so, ba taimakonsa akan daidai ba.
Na hudu: Na fadi uku na dogon zango.
Na hudu: Idan zai yiwu kuma da hali, bayan shekarar zaben nan ta kare wato zuwa 2023 da Sanata Kwakwaso da Mallam Shekarau da Gwamna Ganduje su ajiye neman duk wata takara da zata tsaya a Kano, in har ma zasu nemi wani abu to ya shafi na Najeriya baki dayanta.
Na biyar: Matasanmu masu kishin al’umma da suke saka baki a harkokin siyasa to su shigota tsundum, su daina rara-gefe. Zasu shige tane domin al’umma kuma zasu yi hakuri su bugata irin yadda ake yi da dan kwaskwarima. Ina magana da irinsu Salisu Kofar Wambai ko Yakubu Musa ko Sanyi sanyi ko Muhsin Ibrahim.da dan uwansa Mubarak ko Aliyu Dahiru Aliyu ko Yamai Muhammad da sauransu da yawa.
Na shida: kalmomin da jagorori suke amfani da su a wajen kamfen da nau’in jama’ar da suke fita da su, a yi gyara na gaggawa. A maida hankali a maganganu masu tsabta da mutuntaka da suka mai ma’ana da jan hankali da kuma mayar wa da Allah lamarinsa.
Na bakwai: A yi da gaske a yaki jahilci da talauci da zaman banza na matasa wanda yake bada kofar shan kayan maye da miyagun kwayoyi
Na karshe: Ko dai a samar da jam’iyya ta uku mai karfi kuma ba jam’iyyar ‘yan takara, a’a jam’iyya ta akida da kishin al’umma ko kuma a yi aikin gyaran dokar kasa da ta zabe da za a bada damar yin takara ta indifenda
Wadannan na gajeren zango ne, sauran na ba ku garin. Allahu a’alam.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!