Connect with us

ADABI

Burina In Ga Littafina Ya Yadu A Ko’ina Don Amfanin Al’umma —M. Sa’id

Published

on

Gabatarwa
Sunana Musa M. Sa’id, amma an fi sani na da Autan Elokuence. Ni dan asalin jihar Borno ne, haifaffen karamar hukumar Biu. An haifi nia shekara ta 1998, kuma na yi karatu na tun daga firamare zuwa sakandire a garin Biu, sannan kuma a iya sakandire din na tsaya.

Ya aka yi ka tsinci kanka a harkan rubutu?
Eh to a gaskiya zan iya cewa, tun ina dan karami na ke sha’awar rubuce-rubucen litattafai, amma ban taba yin rubutu na ajiye ba kafin na san cewa ana rubuta litattafai a Intanet ba, a lokacin da na fahimci hakan kuma, sai ni ma na fara nawa rubuce-rubucen.

Zaka kai shekara nawa da fara rubutu?
Zan yi shekara Uku zuwa hudu da fara rubuta littafi.
Zuwa yau kuma na na rubuta littafi guda hudu, Mahaifiyata, Hakki, Amanar So, Shari’ar Adalci, sai kuma wanda nake kan rubutawa a yanzu, wato Kudin Zobe. Amma Amanar So da Shari’ar Adalci ban karasa su ba, sakamakon rasa su da na yi. Sannan kuma na rubuta wasan kwaikwayon Hausa guda daya, takensa Gidan Aure.

A cikin littafanka, wanne ka fi so, bi ma’ana, wanne ya fi burge ka? Kuma wanne ne ya fi ba ka wahala lokacin rubuta shi?
Eh to a gaskiya na fi son Mahaifiyata, duba da cewa shi ne littafina, na farko. Kuma saboda yadda labarin ya yi min dadi, duk da cewa a lokacin ban wani san ka’idojin rubutu sosai ba. Littafin da ya fi ba ni wahala wajen rubutawa kuma shi ne wanda nake kan rubutawa a yanzu, wato kudin zobe.

Wani darussa littafin mahaifiya take kkunshe da shi a dunkule?
Daga cikin darasin da littafin Mahaifiyata yake dauke da shi, akwai illar hada kai da muguwar Abokiyar zama, wato kishiya domin cutar da Abokiyar zamansu, da kuma fa’idan taimakon wanda ba ka san waye shi ba, balle kuma in da ya fito.
Abin da ya sa na fi shan wahala a rubuta littafin Kudin Zobe kuwa shi ne, saboda labari ne da ya ke da jigo kusan Uku zuwa hudu, kuma yadda na faro labarin dole ya wahal da ni. Saboda na yi amfani ne da wani irin salo, in da na dauko tsakiyar labarin na kawo shi farko.

Wani lokaci kafi jin dadin yin rubutu?
A lokacin da nake cikin farin ciki, ina yin rubutu sosai, haka zalika idan ina cikin bacin rai, nan ma na kan dan yi rubutu. Sannan bayan sallar La’asar ma ina yi rubutu fiye da kowane lokaci.

Kasancewarka marubuci namiji, na san ba za a rasa wani kalubale da ka fuskantarka ba, lokacin da ka fara rubutu, ko daga mutane da dai sauran su. Wane irin kalubale ka fuskanta?
Sannan kuma wadanne irin nasarori ka samu ta hanyar rubutu?
Tabbas na fuskanci kalubale wanda har yanzu ina jin zafinsa a raina, amma ba daga makaranta ba ne. Wata rana ce na tura wani littafi cikin group na marubuta, to sai ya kasance marubuciyar tana sirkawa da Turanci, sai wani marubuci da ba zan fadi sunansa ba, ya ga littafin, sai ya yi suka saboda Turancin da ya gani a cikin littafin. Sai na ce masa,
“Ai ba dukka marubuta ne Hausawa ba, ta iya yiwuwa ita ma ba Bahaushiya ba ce, kuma ba za ta iya rubuta wasu abubuwan ba in da ba Turancin ba. Ko ni ma nan ina rubuta litattafai, amma ba Bahaushe ba ne ni.”
Budar bakinsa, sai ya ce, “To me ya sa kai ba za ka yi rubutun da harshenka ba, sai ka ari harshen wasu?.”
A zahirin gaskiya wannan maganar ta kona min rai kwarai da gaske, domin a lokacin har na yanke shawarar na daina rubutu har abada. Babu jimawa da faruwar haka, sai na fara tunanin shin ko zan samu tarihin Mahaifa ta a rubuce? Wato gari na Biu? Sai na yanke shawarar na bincika a Intanet, in dai akwai a rubuce-rubuce zan iya samu.
Haka kuwa aka yi, ina cikin bincike na sai na ci karo da tarihin a rubuce-rubuce. Sai mamaki ya kamani, saboda ban taba tsammanin zan samu tarihin ba. Abin da ya kara ba ni mamaki kuma shi ne, wanda ya rubuta tarihin dan garin Biu ne kuma Babur, kuma Marubcuci ne da ya shahara a rubutun litattafan Hausa da hikayoyi da sauransu. Sunansa Dakta Bukar Usman OON
Ko da na bibiyi tarihin rayuwarsa, sai na ga ashe shi ma ya taba fuskantar irin wannan kalubalen, kuma hakan bai sa ya daina rubutu ba.
A gaskiya nasarori kam na samu Alhamdulillahi, dan samun masoya ma babbar nasara ce. Kuma babbar nasarar da ba zan manta da ba ita ce, nasarar tsallake matakin farko da na yi a gasar rubuta gajeran labari na Pleasant Library, in da a cikin Marubuta fiye da 200 aka ware guda 50 da suka yi zarra, in da ni kuma a cikin Marubuta 50 na zo a mataki na 35 da labari na mai taken Rana Da Zafi. Kin ga wannan ai nasarace babba, musamman ma idan kika duba da cewa ba Bahaushe ba ne ni, kuma wannan ne karo na farko da na fara shiga gasar rubuta labari.

Kamar yadda ka ce kai ma’aboci karatun littafan Hausa ne. Wanne marubuci ne ya fi burge ka?
Littafin wani ko wace marubuciyar ka fara karantawa? Kuma ya sunan marubucin/ marubuciyar littafim?
Marubucin da ya fi birge ni shi ne, Abdul’aziz Sani Madakin Gini. Littafin Marubuciya Hafsat A. Ladan na fara karantawa, sunan littafin Muguwar Sakayya.

Wane kira za ka yi wa ‘yan uwanka marubuta, har ma da masu karatu?
Shawarar da zan bai wa Marubuta a nan ita ce, ya kamata mu san abin da za mu rinka rubutawa, saboda fa za ai mana tambaya a kan abin da muka rubuta da hannayenmu a gobe kiyama. Idan ka rubuta sharri, za ka gani, idan kuma ka rubuta alkahiri, za ka gani. Kuma musamman Marubutan mu mata, wallahi ya kamata ku ji tsoron Allah, an san mata da kunya, amma wani abin takaicin yanzu mata sun wofintar da wannan kunyar da aka sansu da ita, sai ki ga mace tana rubuta littafi, amma ban da batsa babu wani abu da ke cikinsa.
Na karshe, su dai masoya rahama ne, kuma don kana matsayin Marubuci ba yana nufin ka fi kowa ba ne, bai kamata ka wulakanta wani ba, idan suka kira ka a waya da sauransu.
Makaranta kuma a rinka yi wa Marubutan nan uzuri

Me za ka iya cewa dangane da maida littafan online na kudi da wasu marubutan ke yi?
A gaskiya wannan tunani ne mai kyau, ai ba za mu so mu karar da basirarmu a online ba kawai, kuma a kyauta ba, dole za mu so ci gaba komai kankantarsa. Don haka ni dai wannan tunani ne mai kyau a wajena, kuma ai shi dama online writer mafarkinsa bai wuce wata rana ya ga littafin sa a kasuwa ba, kuma wannan wani mataki ne da zai taimaka kwarai da gaske.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: