Connect with us

SIYASA

Kotu Ta Soke Zaben Dan Majalisar Tarayya Na Adamawa

Published

on

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta soke zaben dan majalisar tarayya daga jihar Adamawa Abdulrauf Abdulkadir Modibbo sakamakon zargin bayar da bayanai na karya da ya yi wa hukumar zabe (INEC) a lokacin da ke shigar da bayanai.
Mai shari’a Inyango Ikwo shi ne ya yi hukuncin a jiya Juma’a hadi da umurtar uwar jam’iyar APC da hukumar zabe INEC da cewar su amince da Mustapha Usman wanda shine ya ci na biyu a zaben fitar da gwani da jam’iyyar ta gudanar a ranar 7 ga watan Oktoban 2018, a matsayin wanda ya samu nasara a zaben majalisar tarayya mai wakiltar Yola ta Kudu da Girei a majlisar wakilai ta kasa daga jihar Adamawa.
Mustapha Usman dai shine ya gabatar wa kotun da shaidar cewar Abdulrauf Modibbo ya gabatar da shaidar karatu na bogi wanda hakan ya saba wa doka, a bisa wannan ne kotun ta soke nasarar da ya samu hadi da umurtar a dawo da nasarar zaben kan Usman wanda shi ne ya ci zaben fitar da gwani na biyu a jam’iyyarsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!