Connect with us

TATTAUNAWA

Kuskure Ne Da Rashin Adalci Hada Mabaraci Da Almajiri –Magajin Malam

Published

on

Alaramma Ibrahim Khamisu Dan Yaranchi wanda aka fi sani da Magajin Malam, Guda cikin ‘ya’yan Alaramma Gwani Khamisu Ibrahim Dan Yaranci, wanda ya kafa tsohuwar shaharariyar tsangayar nan da ta yaye Gwanayen da Gangarayen Alkur’ani wadda Unguwar T/Murtala cikin Karamar Hukumar Nasarawa.
Atattaunawarsa da Wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Magajin Malam ya bayyana matukar damuwa bisa yadda duk wata shara idan aka kwaso sai ajibgawa Almajiran tsangaya, sannan kuma ya jadadda aniyarsu ta ci gaba bayyana kyawawan halayen almajirai sannan ya bayyana bambancin da ke tsaknin Mabaraci da Almajiri.

Ga dai yadda tattaunawar ta Kasanace za mu so ka gabatarwa da mai karatu kanka?
Alhamdulillahi ni sunana Ibrahim Khamisu da ga Alaramma Khamisu Dan Yaranci wanda aka fi sani da Magajin Malam, an haife ne a unguwar Tudun Wada dake cikin karamar hukumar Nasarawa a Jihar Kano. Kuma na yi karatun alkur’ani da sauran fannonin ilimi gwargwadon iko a wurin mahaifinmu kamar yadda aka sani dama mun tashi cikin tsangaya ne don haka da Alkur’ani muka bude ido.

Me za ka ce kan yanayin da ake samu a halin Yanzu, musamman yadda ake ta yayata matsalar barace-barace da cewar almajirai ke yinta?
Alhamdulillahi Wannan shi ne babban takaici kuma a fahimta ta ina ganin wannan babban Kuskure ne kuma rashin adalci ne hada Mabaraci da Almajiri, domin Kalmar almajiri kalma ce ta larabci wadda aka samo ta daga Kalmar Almuhajir, wanda ya yi tafiya daga wani wuri zuwa wani, daga wani gari zuwa wani garin domin neman ilimi walau na alkur’ani ko sauran fannnin ilimi addini. Tafiya zuwa neman ilimi kuma wajibi ne kamar yadda duk Musulmi suka sa ni.
Saboda haka mu a bangarenmu na ahlin tsangaya wanda muka yi imani da wannan tsari wanda ke cike da kyakkyawar tarbiyya da kuma sadaukar da kai, sannan kuma acikin tsarin karatun allo akwai illimai da ke kushe a cikin tsarin karatun allo. Don haka kuskure ne ka hada Mabaraci da Almajiri.

Idan Haka ne Magajin Malam ya kamata a bayyanawa mai karatu bambanci tsakanin Mabaraci da almajiri?
Alhamdulillahi tun da farko ma abinda mahukunta da mutanen da suka dauki karantsana suka jibgawa tsarin karatun allo ya kamata suyi, domin shi abinda ba ka da ilimi ko masaniya akansa yana da wuyar gaske ka yi wa wasu adalci. Ko shakka babu akwai gagarumin banbanci tsakanin Mabaraci da Almajiri, da farko dai shi almajiri wani tsari ne na tafiya da yake yi domin neman ilimi, kenan kaga shi cikin jihadi yake kodayaushe, sannan kuma ina tabbatar maka da cewa babu wani almajirin tsangaya da yake wuce shekara 15 yana bara, musamman daman barar almajiri bara ce ta abinci ba neman kudi ba balle zuciyarsa ta mutu.
Abu na baiyu kuma shi ne Allah ya wadata almajiran tsangaya da wadatar zuci, dan abin da suka samu ya wadatar da su, hakan tasa kake ganin duk wani almajirin tsangaya da wuri yake fara sana’a, musamman sana’ar almajirai wadda ta hada da yankan farce, dinkin hula, aikin babbar riga da sauransu, saboda haka da zarar sun fara wannan sana’a zaka iske sun samu abin da za su ci gaba da sakawa abakin salati.
Amma shi mabaraci ya dauki bara ne a matsayin sana’a, don haka baya wadatuwa da duk abin da ya samu, sannan kuma mabarata suna nan sun cika hanyoyi, masallatai, da manyan tituna, zuciyar ta mutu ba zasu iya yin kowacce irin sana’a ba domin dogaro da kansu.
Sannan zaka tarar da mabaracin da ya haura shekara 50-70 yana bara. Amma don rashin sani ko hassada ko kuma bin umarnin yahudawa sai kaga wasu marasa kishin karatun al’kurni ako da yushe suka tashi yin Magana kan harkokin barace-barace sai su jibgawa almajiri.

Amma ana ganin yadda ake dibar yara ana tafiya dasu shi ne babbar matsalar da ke haifar da gurbacewar tarbiyar yaran?
Ina son tambayarka shin tsakanin ilimin alkur’ani da na boko wanne ya riga wani shigowa arewacin kasarnan?
Kamar yadda aka sani ilimin alkur’ani ya riga ilimin nasara shigowa wannan yanki namu sama da shekara dubu, kuma shi kansa Bature ya iske iyayenmu da tsarin karatu da rubutu domin tuna wancan lokaci an tarar da jama’ar mu suna gudanar da harkokin mulki da shari’a ta hanyar amfani da rubutun ajami.
Kuma da kake maganar tafiyar yara daga nan zuwa can mantawa ka yi a kasar nan akwai tsarin makarantun Unity wadda ake dibar yara da wannan jihar zuwa waccan, kuma idan ka ce wannan akwai tsari da hukumomi suka tanada domin daliban, shin me ya hana hukumomi da gwamnatoci su samar da irin wani tsari ta yadda za a dinga samar da irin wannan tallafi ga makarantun allo domin suma su shiga cikin tsarin samun gudummawar gwamnatoci?
Tun lokacin da ilimin nasara ya shigo wannan yanki sai mahukunta suka karkata zuwa bangaren turawa, su kuma daman neman kofa suke don haka sai suka fara likawa wasu daga cikin jagororin al’umma kudi ta yadda har sai da turawan suka samu gindin zama, sannan kuma suka yi duk mai yiwuwa wajen kassara kimar wannan tsari na Karatun Alkur’ani, kuma daman ai an san turawa makiya Allah ne, ta ya zasu yi abinda zai inganta wannan tsari na tsangaya.
Idan har za a dauki yara daga Kano zuwa Legas domin halartar makarantar Unity banga dalilin da za’a dora karan tsana akan tsarin tafiye tafiyen almajiran tsangaya daga wannan gari zuwa wancan ba, musamman kuma da suke ta tsegungumi kan cewa wai ana tafiya ne da kananan yara, to sun manta cewa mu annabin rahama ya fada mana karfin sanin yaro karami kamar rubutu ne akan dutse, ya yinda da sanin babba bayan ya girma kamar rubutu ne a akan ruwa. Wannan ne yasa iyaye ke gaggawar fara samawa ‘ya’yansu ilimi tun suna kanana.

Yanzu an fara jin yunkurin Gwamnati na duba matsalar almajirai, da za’a tuntuce ku wacce shawara zaku bayar domin samun nasara?
Alhamdulillah kamar yadda muke fada aduk lokacin da gwamnati ke kokarin kawo gyara a cikin harkar almajirai na hakika ba mabarata ba, ayi kokarin shigo da alarammomi na Hakika ba alarammomin riga da mota ba. A tabbatar da samun alarammomin dake tare da almajiransa ba wanda ya manta rabonsa da tsangaya ba. Sannan kuma abinda muke so mahukunta su yarda shi ne Alkur’ani Ilimi ne mai zaman Kansa, dole idan anason al’amura su inganta sai dawa koyarwa alkur’ani.
Idan aka yi haka babu shakka za’a samu ingantattun shawarwari da idan Gwamnatin tayi amfani dasu za’a samu Nasara, musamman ganin yadda daman ai barin gini tun ran zane akayi. Alaramman gaske yasan almajiri na hakika domin akwai yaran da suke gaban iyayensu amma saboda halin rayuwa suke daukar kokon bara suna amsa sunan almajiri.

ALaramma me zaka ce dangane da irinhadin kan almajiran tsangaya?
Alhamdulillahi wallahi kullun na tuna wannan sai zuciya tat a kara yin fari, domin ina tabbatar da acikin al’umma babu wasu jama’a da suka kai almajirai hadin kai, domin duk inda wani sha’aninarziki ko rashi ya faru nan zaka dandzon ‘yan uwa anyi tururuwa domin taya murna ko jajantawa, wannan tasa ahlin tsangaya basu bakunta, duk inda suka shiga matukar akwai tsangaya ko ahalinta zaka kamar suna gidansu ne cikin nutsuwa da kwanciyar Hankali.

Mene sakon ka na karshe?
Alhamdulillahi sakon mu musamman ga hukumomi dake rajin kawo dauki ga tsarin tsangaya, da farko ina so shaida masu matakin farko na wannan gyara shi ne aminta da cewa Alkur’ani ilimi ne mai zaman kansa, kuma bayyada zaka raba musulmi na hakika mai kwadayin saduwa da Mahaliccinsa cikin Natija da Alkur’ani. Sannan kuma dole masu ruwa da tsaki idan dai gyaran da Ganske ake to dole akoma cikin tsangayu a sadu da alarammomi masu darasu wadanda ko da yaushe suke tare da almajirai, sune kadai zasu bayar da cikakken bayani da kuma nagartattun shawarwari da idan gwamnatoci suka yi amfani dasu na tabbata kwalliya zata biya kudin sabulu.
Haka kuma ina kara kira ga matasan alarammomi irina da mu tashi haikan domin tunkarar wannan kalubalen da ke tunkaro harkar karatun alkur’ani, mu saukewa iyayen mu alarammomi da girma ya kamasu, mu kyale su da harkokin darasu da hidimar al’umma,mu mu fito domin hadai karfi domin fito sahihan bayan nan da suka shafi harkokin tsangaya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!