Connect with us

SIYASA

Masari Ya Tarar Da Kalubalen Rashin Tsaro Ne A Katsina –Sugaban Matasa

Published

on

Abubakar Abba ya tattauna da Kwamarade Abbas Tukur Maigirma sanannen mai fashin baki a siyasar Nijeriya, musamman a jiharsa ta Katsina kuma shi ne Shugaban Kungiyar Matasan jihar Katsina, ya yi bayani a kan kokarin da Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari yake yi na tabbatar da tsaro a jihar da kuma a kan sauran lamura.

Lamarin rashin tsaro ya addabi jihar Katsina, a matsayin ka na dan jihar wane kokari ka ke gani Gwamana Masari ya ke wajen magance matsalar ?
Matsalar rashin tsaro ba a Arewa ko Katsina ba ne kawai, kalubale a kusan a daukacin Nijeriya, musamman idan aka yi la’akari da yadda rashin tsaron ke shafar tattalin arzikin Nijeriya, lamarin rashin tsaro a Katsina yana da nasaba da yadda sauran jihohi musamman wadanda suke makwabtaka da Katsina su ma suka samu wannan matsalar. A baya jihar Katsina ta kasance daga cikin sahun johohin dake cikin zaman lafiya kuma muna da tarihin zaman lafiya a Katsina, amma a yanzu abubuwa suna neman su tabarbare amma duk da hakan, Allah nab a da nasara saboda addu’oin da muke samu tun daga gun malamai da waliyyai da ke jihar na baya, inda Allah ya taimaka mu matsalar take zo mana da sauki sabanin a wasu jihohin da muke makwabtaka da su. Tun bayan zuwan gwamnatin Dallatun Katsina a shekarar 2015, yana zuwa a lokacin ya akwai kalubalen rashin tsaro a jihar, musamman a kananan hukumomin Danmusa, Faskari, Batsari, Safana, Sabuwa Dandume, a inda yana zuwa sai ya fara kokarin yadda zai takawa lamarin birki, inda ya kirkiro da nemo masu tayar da kayanr baya don gwamnatin jihar ta tatauna da su don su daina, Allah kuma ya bayar da nasara a karkashin jagorancin Shugaban kwamitin aka nada Sakataren Gwamnatin Jihar Mustapha Inuwa, aka nemo masu tayar da zaune tsayen aka zauna da su a karshe aka cimma matsaya na yar da za su ajiye makamansu, su kuma zamo mutane na gari. Gwamnati ta yi masu afuwa a bayan sun ajiye makamansu, wasu kuma daga baya suka sake komawa ta’asarsu, inda gwamnatin jihar ta sake yi shiri don magance lamarin baki dayansa. Kowa ya san yadda aka samar da tsaro a jihar Katsina wanda inda Masari bai trashi tsaye ba da ba a samu saukin lamarin rashin tsaro a jihar ba, ina mai tabbatar maka da yanzu mun dinga barin jihar. Alhamdulillahi, Masari yana yin iya kokarinsa duk da ba a iya magance lamarin baki daya ba, amma ya yi kokari saosi.

Amma ba ka ganin lamarin rashin tsaron na yanzu a jihar yana da nasaba da yadda rashin aikin ya yi yawa a jihar?
Alhamdulillahi, amma badan muna da alumma masu yawa a Katsina ba na san da Masari ya samarwa kowannne dan jihar aikinyi, amma duk da hakan gwamnati Masari ta smar da shirye-shiye na daukar matasa aikin yi an kuma basu horon akan sana’oin hannu kuma ko wanne matashi da kansa zai zabi sana’ar da yake son yi, ina daya daga cikin kwamitin suka yi wannan aikin wanda Sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuiwa ya jagoranta wasu matasan an basu kudi kai tsaye kamar naira dubu dari ko wannen su, wasu kuma an horas dasu sana’oin hannu, inda aka bude masu shaguna aka zuba masu kaya aka kuma biya kudin shagunan. Anyi horon ne kashi- kashi kuma kungiyoyi da dama a jihar sun amafa domin tun lokacin da gwamnatin Masari tazo, tana yin aiki da kungiyoyi. Har ila yau, gwamnatin Masari ta samar da guraben ayuka gay an jihar kamar na NDE da sauransu.

Me za ka iya cewa rundunar yansandan jihar a fannin tsaro a jihar ?
Muna da kyakyawan fahimta da su, amma shawarar da zan ba su na san suna iya kokarin su amma muna son su dinga yin sirri wajen gudar da ayyukansu, inda duk abin da za su yi, sai dai kawai a ga sun gudanar ba tare da mutanen gari sun sani ba, musamman idan aka yi la’akari da wasu yan shoshiyal mediya a kasar da suke yi wa lamarin tsaro karan tsaye wajen yada karya. Ina kuma kira ga matasa da su dinga yi wa shugabbin addu’a da a ba su goyon baya a kan shugabancisu amma duk inda sukaga shugabannin sunyi kuskure, su dinga basu shawarar data dace da kuma yin suka mai ma’ana bata yarfen siyasa ko tozarta su ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!