Connect with us

MANYAN LABARAI

Gobe Za A Fara Azumin Ramadan A Fadin Nijeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Kwamitin Shura na fadar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’adu Abubakar ta sanar da ganin jaririn watan Ramadana da yammacin yau Lahadi, inda kwamitin ya bayyana gobe Litinin a matsayin daya ga watan Ramadana.

Kwamitin ya fitar da wannan sanarwar ne da misalin karfe 9 na daren yau, inda mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayana goben a mastayin daya ga watan Ramadana, sannan ya taya al’ummar Musulmi murnar shiga watan Ramadana mai tsarki, sannan yake fata ayi ibadu cikin lafiya da kwanciyar hankali.

Kasar Saudiyyar ce kusan kasa ta farko da ta bayyana ganin jinjirin watan Ramadana na wannan shekarar, amma dai ba mu san zuwa anjima ba, ko wasu karin kasashe za su yi irin wannan sanarwar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!