Connect with us

RIGAR 'YANCI

Dubun Sojan Da Ya Yi Wa Yarinya Fyade A Gaban Iyayenta Ta Cika A Yobe

Published

on

Rundunar yan-sandan jihar Yobe ta cabke mutum 26 wadanda take zargi da aikata laifukan fyade; ciki har da wani soja daya da ya yiwa wata yarinya fyade a gaban iyayen ta, a garin Buni-Yadi da ke jihar.
Kamar yadda jami’in hulda da jama’a a rundunar yan-sandan, ASP Abdulmalik Abdulhafiz ya bayyana, tara da karin haske kan cewa masu laifin sun hada har da masu garkuwa da mutane, yan fashi da makamai guda uku, wadanda suke tsare a ofishin binciken manyan laifuka (CID), da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Ya ce, daga cikin wadanda ake zargi da laifin fyade akwai soja daya, Pribate Akhigbe Tijjani, wanda yake aikin samar da tsaro a runduna ta 27 (Taskforce Brigade), wanda ya yi amfani da wannan damar inda ya kutsa kai a gidan su yarinyar tare da yi mata fyade a gaban iyalan ta.
Abdulhafiz ya kara da cewa, daga baya kuma Tijjani ya bukaci ala-dole sai dan uwan yarinyar kan ya yi lalata da ita. Bayan da ya ki bin umurnin Akhigbe din ne, sai ya zaro wuka tare da caka masa ita.
Har wala yau kuma, abokan aikin nasa sun kai rahoton wannan aikin assha da Tijjani ya aikata ga na gaba dashi, domin daukar matakin ladabtarwa, wanda a karshe aka kore shi.
Abdulhafiz ya kara da cewa, daga cikin wadanda ake zargi da laifin fyade, a tsakanin watan Junairu da Afirilu, inda suka samu mutum biyu Abubakar Sadik Dauda da Tasi’u Zilla suka yi wa wasu yara; dan shekara 9 da 13 fyade a garin Potiskum.
A hannu guda kuma, akwai wasu mutum takwas (8) da suka yiwa wata yarinya yar shekara 15 fyade. Yayin da sai bayan gano yarinyar ta na da ciki, sannan iyayen ta suka tabbatar cewa fyade aka yi wa yarinyar.
A cikin wannan adadin, rundunar ta yi nasarar damke Tasiu Abdulkareem, da laifin hannu wajen garkuwa da wani karamin yaro dan shekara biyar, inda daga baya yaron ya mutu a hannun su, a garin Potiskum.
Wanda kafin hakan, ya bukaci iyayen yaron su biya shi naira miliyan 8 a matsayin kudin fansa, wanda ya karbi 50,000 na kafin alkalami. Yayin da a kokarin karbar kudin ne yan-sanda suka cabke shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!