Connect with us

LABARAI

Jihar Legas Ta Kama Ganda Mai Guba Ta Naira Miliyan 10

Published

on

Ma’aikatar aikin gona ta jihar Legas ta kwace kusan tan 30 na ganda da ake zargin ta na dauke da guba, ma’aikatar ce ta bayyana hakan yau Litinin, inda ta bayyana cewa gandar ta nada matukar hadari.

Kwamishinan ayyukan gona na jihar Legas, Mista Oluwatoyin Suarau ne ya bayyana haka, inda yake cewa kimar kudin gandar da su ka kama ya kai Naira Miliyan 10.

Jami’an ma’aikatar sun kai samame guraren da ake sarrafa gandar, inda suka yi samun masu sarrafa gandar a bakin aiki, ana tunanin robar da ale amfani da ita wajen babbaka gandar ce ta ke haifar da guba a cikin gandar.

Sannan an kama mutum shida da suke aikin babbaka gandar, sannan an rufe wata mayanka sa ita ma ake sarrafa gandar, wacce aka bude ta ba bisa ka’ida ba.

Ma’aikatar ta gargadi masu sarrafa da babbakar gandar, su guji amfani da abubuwa masu hadari wajen babbakar fata don mayar da ita ganda.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!