Connect with us

LABARAI

Kungiyar Matasan Arewa Ta Yi Zanga-zanga Kan Kashe-kashen Zamfara

Published

on

Daruruwan matasa ne karkashin inuwar kungiyar Hadin kan matasan Arewa, suka gudanar da zanga-zangar neman a kawo karshin kashe-kashen da ake a jihar Zamfara, sannan gwamnatin ta kawo karshen ‘yan bindiga a jihar da jihohin da suke makwabtaka da ita.

An yi gangamin ne da safiyar yau Litinin a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, wasu zanga-zangar sun bayyana cewa sun dauki wannan matakin ne don kira ga hukumomi da su kawo karshen wannan al’amarin a jihohin Arewa maso yamma.

Shugaban kungiyar matasan, Adamu Matazu ya bayyana cewa wadannan kashe-kashen sun yi yawa, kuma kullum abun sake gaba ya ke yi, maimakon a samu sauki, don haka suke rokon gwamnatin tarayya da ta kawo karshen wannan lamarin.

Matazu ya zargi wasu manyan mutane da hakar ma’adanai a jihar ta Zamfara, wanda ana ganin hakar ma’adanan ya sa wadannan kashe-kashen suka ta’azzara har suke neman fin karfin gwamnatin jihar ta Zamfara.

‘Kiran mu shine gwamnati ta kawo karshen wannan lamarin, kuma wannan shine kadai abinda za mu iya yiwa al’ummar jihar Zamfara din, ba Zamfara ba kadai, dukkan yankin Arewa maso yamma da ma kasar mu gaba daya.’ inji Matazu
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!