Connect with us

LABARAI

Watan Azumi Wata Ne Na Ibada Da Yawaita Addu’oi – Shugaban Kwalejin Annur

Published

on

Watan Azumin Ramadan wata ce mai matukar muhimmanci ga al’ummar musulmin duniya, saboda haka ya zama wajibi mu yi amfani da watan wajen gudanar da ibada tare da neman gafarar Allah.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban kwalejin ilimi ta Annur Institute dake unguwar Rangaza a karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, Malam Auwalu Abubakar Suleiman, a lokacin da yake tsokaci a kan watan na Azumin Ramadan.
Haka kuma inji Malam Auwal Suleiman Abubakar, al’ummar musulmin su tabbatar sun mayar da hankulan su wajen yawaita karatun Alkur’ani mai girma saboda a cikin watan ne aka saukar da Alkur’ani mai girma littafin Allah mai tsarki. Addu’a abu ce mai muhimmancci a cikin watan na Ramadan al’umma su yi amfani da damar wajen yawaita addu’oi dare da rana tare da sanya kasar nan a cikin addu’oin su na samun zaman lafiya babu abin da kasar nan ta fi bukata irin addu’ar Allah ya kawo karshen garkuwa da mutane da ake yi a wasu jihohin arewacin kasar nan da sauran matsalolin tsaro.
Shugaban makarantar ta Annur Institute ya ba da misalin yadda sahabban manzon Allah ya shirin na musamman idan aka ce watan Azumin Ramadan ta kusa kamawa musamman akan kusantar Allah da karatun Alkur’ani da addu’oi da kuma taimakawa marasa karfi.
Saboda haka ya zama wajibi ga masu hali da su taimakawa marasa karfi musamman ciyarwa da kuma ba su kyaututtuka da sauran nau’ikan taimako da fatan Allah ya sa hadamu da albarkar dake cikin watan ya kuma amshi addu’oin da za mu gudanar a cikin watan mai albarka.
Da yake tsokaci akan harkokin ilimi a kasar nan Alhaji Auwalu ya shawarci shugabanni cewa ya za ma wajibi su kara azama wajen taimakawa harkokin ilimi domin yanzu ilimi na daya daga cikin abin da yake bukatar taimako na musamman. Babu ci gaba akasa idan aka ce ba ilimi. Amma ya nuna gamsuwar shi game da yadda gwamnatin jihar Kano ke kokari a kan harkar ilimi.
Shima Alhaji Sunusi Manaja da ya ke gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar Galadima a Kano ya yi nasiha ga al’ummar musulmi cewa su kasance masu yawaita ibada kamar karatun alkur’ni da taimakawa marasa karfi acikin watan Azumin Ramadan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!