Connect with us

SIYASA

Akwai Alkawari Tsakanina Da Jagororin APC Kan Kujerar Sakataren Jam’iyya – MB. Mustapha

Published

on

BARISTA MUHAMMAD BELLO MUSTPAHA, wanda a ka yi takaita lakabinsa da MB. MUSTAPHA, zakakurin matashin dan siyasa ne wanda ya yi matukar fice tun ya na dalibta a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya shugabanci kungiyar dalibai na jami’ar bakidaya. Ya yiwa rusasshiyar jam’iyyar CPC takarar gwamna a 2011, sannan ya na cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar APC a 2015, wacce ta lashe zaben shugaban kasa. Ya yi takarar neman sakataren jam’iyya ta APC a 2018, amma a ka ba shi hakuri, don ya daga wa wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, bisa alkawarin cewa, idan ya ci zabe za a maye gurbinsa da Barista MB. Mustapha. Tuni dai Mia Mala ya lashe zaben; abinda ya rage shi ne, ganin shin APC za ta cika wancan alkawarin ko akasin hakan? Editan LEADERSHIP A YAU, NASIR S. GWANGWAZO, ya tuntube shi, don jin matsayarsa kan batun da kuma halin da a ke ciki a lahin yanzu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Masu karatunmu so ka fara gabatar mu su da kanka a takaice.
Ni lauya ne, ni dan jihar Taraba ne kuma dan siyasa ne, sannan na fara siyasa ne tun daga jami’ar Ahmadu Bello da ta ke Zariya, inda kafin na kammala jami’ar na yi shugabancin kungiyar ’yan asalin jihar Taraba da ke jami’ar, sannan kuma na zama shugaban daliban jami’ar ta Ahmadu Bello gabadaya. Bayan wannan na gama makaranta a shekarar 2001. A 2002 Ina cikin jama’ar da su ka kira Janar Muhammadu Buhari ya shiga siyasa, kuma ya amsa kiranmu ya shiga. Shi ya sa a ka fara The Buhari Organisation (TBO) tare da mu. Ni ne shugaban matasa na Muhammadu Buhari na farko na kasa bakidaya. Daga nan har Allah ya kawo lokacin da mu ka fice daga tsohuwar jam’iyyar ANPP mu ka kirkiro tamu jam’iyyar mai suna CPC. Nan ma mu ka cigaba da fafutuka; na tsaya neman takarar gwamna a jihar Taraba. Allah ya taimake ni a ka tsayar da ni a zaben fitar da gwani. Don haka na tsaya takarar gwamna da gwamna mai ci. PDP ta yi ma na handama a lokacin, amma mu ne mu ka ci zabe a 2011. Haka mu ka cigaba da tafiya da Shugaba Muhammadu Buhari har Allah ya kawo APC. Ina daya daga cikin ’yan kwamitocin da a ka kafa hadakar jam’iyyun da su ka zama APC guda uku; ANPP,ACN da CPC.
A zabubbuka da su ka gabata na tsaya zaben sakataren jam’iyya na kasa, amma sai dattawan Arewa maso Gabas su ka hadu a gidan tsohon gwamnan jihar Adamwa Murtala Nyako a 2014 da ke Asokoro a ka roke ni na bar wa Kassim Imam daga Borno, na yar. Kassim Imam kuma da a ka je filin zabe, nan ma su Atiku, su Nyako su ka ce a madadin Gwamna Geidam na jihar Yobe ya ce idan ba a mayar ma sa da sakataren jam’iyya jiharsa ba, zai bar jam’iyya. To, shi ya sa sai a ka bar ma sa, a haka Mai Mala ya samu ya zama sakataren jam’iyya na kasa.
A shekarar 2017 lokacin da Babachir ya sauka daga sakataren gwamnatin tarayya da ma ya na rike da mukamin shugaban APC na yankin Arewa maso Gabas. To, sai ya rasa kujerun guda biyu. Nan ma na sake fitowa takara na je na yi kamfen a ko’ina. Sai manyan Arewa maso Gabashin Najeriya su ka zo su ka ce na yi hakuri a bar wa jihar Adamawa ta karasa, domin Babachir daga can ya fito. A ka ba ni hakuri a kan za a nemi abinda za a yi min a jam’iyyance ko a gwamnatance. To, amma Allah bai kaddara ba har zuwa yanzu. Ba na cewa sun hana ni, domin Allah ne bai kaddara ba. Nan ma na yi hakuri na bar wa Kwamred Mustapha Sale, wanda shi ya ke kan kujerar yanzu.
A shekara ta 2018, wato shekarar da ta gabata kenan a ka sake yin taron jam’iyya na kasa don zaben shugabannin jam’iyya. Na sake tsayawa takarar kujerar sakataren jam’iyya na kasa. Nan kuma na ce mu su ba zan sauka ba. A ka yi kwamitoci daban-daban, kwamitocin su Rochas Okorocha ko Gwamna Badaru. Sai na ce mu su babu dalilin sauka ta, domin ba mu taba samun wakilci a tsarin shugabancin jam’iyya na kasa ba (NWC). Sauran jihohin yankin Arewa maso Gabas duk sun samu, su na da wakilci. A ka yi ta kai ruwa rana har Allah Ya sa daya daga cikin shugabannin jam’iyyarmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da sauran manyan jam’iyya su ka zo su ka ba ni hakuri cewa sun san na yi hakuri a baya, amma su na sake roka. Su ka ce kuma idan cancanta ce, ni na cancanci na zama. Har na ke ce mu su idan ni na cancanta, me ya sa ba za a mara min baya ba? A nan dai a ka ba ni hakuri a ka ce ga alkawura guda biyu, wadanda za a cika. Alkawurran nan ba komai ba ne illa cewa a ka yi a mukamin gwamnati za a biya ni, sa’annan idan Mai Mala ya zo tafiya neman kujerar gwamnan, domin tun lokacin akwai fastocinsa, za a mayar ma ni da kujerar ta sakatare. Abinda ma ya kara sa ni fita daga takarar kenan, kuma sai da mu ka riga mu ka shiga mu ka gama ‘screening’ sannan a ka ce zai tsaya shi ma.
To, a ka ce ni zan maye gurbinsa, saboda duka sauran sun sauka, saura ni kadai. Don haka ni ne na karshen sauka, don ya zama sakataren jam’iyya na kasa. Ka ga wannan shi ne Bature ya ke kira da ‘First Runner Up’. A al’adar jam’iyya duk lokacin da irin wannan gurbin ya samu, to a na neman wanda su ka tsaya zabe ne a duba wanda ya ke biye da shi a maye gurbinsa da shi. Idan a ka duba za a ga sakataren yada labarai na jam’iyya, Bolaji Abdullahi, da ya bar jam’iyya sai a ka nemo Isa, wanda yanzu ya ke kan kujerar a ka ba shi. Su shugabannin Arewa maso Tsakiya su ka taru su ka kawo sunansa a ka ba shi, saboda shi ne na karshen sauka a lokacin takara. To, idan kuwa haka ne a baya a na yi, me ya sa yanzu ba za a yi ba?
Wannan shi ne abinda ya ke wakana; ba a cika alkawarin za a ba ni mukami a gwamnati ba, sannan kuma ban ki yiwa jam’iyya aiki ba, kuma ni din nan mamba ne na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa. Ina cikin kwamitoci daban-daban guda uku; na mata da matasa da na sadarwa da shirye-shirye da na tsare-tsare. Duka na shiga. Ka ga idan ba na biyayya kuma ban cancanta ba ai ba za su ba ni ba. Ba ni na nema ba; su ne su ka ba ni. Ni ba komai ba ne, illa mai biyayya kuma wanda bai taba cin amanar jam’iyya ba. Na je na nemi takarar gwamna a ka hani ni! Kai na je na nemi tsaya wa takarar sanata ma na ci, amma a ka hana ni tsayawa, a ka ba ni hakuri a ka ce na yi hakuri na yiwa jam’iyya biyayya. Na sake yin hakuri kuma na yiwa jam’iyya aiki.
Amma yau ba bu mukamin gwamnati, sannan na jam’iyya ma babu shi, domin yau kusan wata biyu kenan a zaben Mai Mala a matsayin gwamnan jihar Yobe, amma hau yau babu wanda ya zo ya ce zo a cika ma ka alkawari. Amma ba na cewa shugabanninmu ba su da alkawari, a’a, Ina kyautata zaton mantuwa ce, saboda ka san su al’amura idan su ka yi yawa. Don haka mu ke sake tunatar da shugabanninmu kamar shugaban kasa zuwa shi Asiwaju da sauran manyan shugabanninmu da shugaban jam’iyya Adams Oshiohmole da irinsu Rotimi Amaechi da sauran dattawan jam’iyya su tuna su cika alkawarinsu, domin alkawari abin tambaya ne, kuma cika alkawari ya na daya daga cikin abinda ya sa mutum ya ke zama kamili. Ian da tabbacin cewa shugabanninmu masu cika alkawari ne.
Sannan su sani fa wallahi kujera ya zama wajibi a ba wa wanda ya cancanta, domin shi Mai Mala bai yiwuwa ya na kan kujerar zababbiya ya sake hawa wata kujerar ta wannan ba sake wannan ba. Sai ya mika kama aiki ga wannan sabon sakatare sannan zai halarta. Kada su manta su je su bar shi ya cigaba, domin wani zai iya kai su kotu a cikin wadanda su ke nema. Duk da dai wannan ba shi ne a gabanmu ba. Kawai dai su tabbata ya mika aiki, kafin ya je ya karbi kujerar gwamna ta Yobe.
Za mu cigaba gobe in sha Allahu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!