Connect with us

LABARAI

Azumi: Gwamna Mai Jiran Gado Ya Umarci Mai Barin Gado Ya Biya Albashi A Bauchi

Published

on

Zababben gwamnan jihar Bauchi mai jiran gado, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya umarci gwamnan jihar mai barin gado, Alhaji Muhammad A. Abubakar, da ya gaggauta biyan albashin ma’aikata na watan Afrilun 2019, domin jama’ar jihar su samu sauki da faragar gudanar da harkokin Azumi cikin wadata da kwanciyar hankali.

Sanata Muhammad ya yi wannan umarni ne ta hanyar yin roko ga gwamnan mai ci a sakonsa na shigowar watan Azumi.

Kauran Bauchi, wanda a cikin sakon na barka da zagayo watar Ramadana da ya aike wa al’ummar jihar Bauchi domin yi mu su fatan alkairi na fara Azumin watan Ramadana cikin kwanciyar hankali da neman dacewa, ya kara da neman jama’ar jihar da su yi addu’a domin samun cigaba ga jihar da kasa bakidaya.

Zababben gwamnan jihar, wanda ya aike da wasikar taya murnar ta hanun kakakinsa, Ladan Salihu, ya kara da cewa, “zababben gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya na taya al’ummar Musulmi a jihar Bauchi murnar zagayowar watan Ramadana wata mai alfarma.

“Mu na godiya ga Allah (SWT) da ya sa mu ke daga cikin wadanda su ka shaidi wannan wata mai dumbin albarka da falala cikin koshin lafiya da wadatan rai.”

Sanarwar ta shaida cewar wannan watan Azumin wannan shekarar ya zo ne daf bayan kammala yakin neman zabe da kuma zaben shugabanni a kujeru daban-daban da jama’a su ka yi a fadin kasar nan.

Sanata Bala ya yi amfani da wannan damar wajen neman gwamnan jihar Bauchi mai barin gado da ya hanzarta biyan albashin ma’aikatan jihar na watan Afrilun da ya gabata, domin Musulmai su samu zarafin gudanar da ibadarsu cikin wadata da kwanciyar hankali.

“Sannan mu na rokon gwamnan jihar Bauchi, Mai girma Muhammad Abubakar da ya gaggauta biyan albashin ma’aikata domin al’ummar jihar su samu damar gudanar da Azumi cikin wadata musamman ma da yake jihar ta samu kasonta daga asusun gwamnatin tarayya,” kamar yadda ya shaida. Ya kara da neman addu’ar jama’ar jihar samun nasarar amsar mulki cikin ruwan sanyi.

“Daga karshe mu na rokon al’ummar Musulmai da cewar su yi amfani da wannan wata mai alfarma wajen kara hada kai da jawo juna a jika, kana su yi addu’a ta musamman domin cigaban jihar da kuma samun nasarar amsar mulki a ranar 29 ga Mayu cikin aminci da kwanciyar hankali,” a cewar sabon gwamnan jihar da ke jiran yin rantsuwar karbar amana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!