Connect with us

MAKALAR YAU

Falsafofi (2)

Published

on

Ubangiji A Zatinsa
Kowa daga cikinmu yana da irin sifar Ubangijin da ya ajiye a zuciyarsa dai-dai irin zurfin iliminsa. Sifar da mai ilimin sararin subhana (Cosmology) yake bawa Allah ta saba da wanda yake zaton duniya a tsaye take guri daya. Amma dai dukanmu babu wanda ya san Allah a hakikarsa, sai dai binciken da muke yi a cikin duhu.
Da yake dukanmu muna tsakanin yaudarar guri da lokaci (space and time illusion) babu wanda zai tunanin Allah ba tare da ya sanya shi a guri ko ya yi masa lokaci ba. To amma Allah yana nan tun kafin halittar guri da lokaci don haka babu wanda kenan yake tunanin Allah a yadda yake.
Immanuel Kant a littafinsa “Critikue of Pure Reason” ya bayyana cewa duk abin da ya wuce hankali to hankali ba zai iya tunaninsa ba. Tun da hankali yana cikin lokaci da guri to kenan babu mai iya tunanin Allah a yadda yake. Don haka Manzon Allah (saw) ya ce mu yi tunani akan halittun Allah domin idan muka yi akan Allahn sai mu halaka!
An ce Sayyidi Abubakar ne ya ce duk abin da ya zuciyarka ta raya maka game da Allah to ba shi ne Allahn ba. Masana ilimin Tauhidi (Theology) suna ganin hanya guda da zaka iya sifanta Allah to shi ne ka kore masa duk wata sifa da zuciyarka ta darsa maka. Wato idan Allah ya ce shi mai ji ne to kada ka taba dauka irin jin da halittu suke yi yake. Idan ya ce mai gani ne to ba irin ganin da muke yi bane.
Malaman Mu’utazila sun gane fadin da yake cikin rintsin sanin Allah. Kuma sun gane duk wanda zai bawa Allah wata sifa to irin siffofin halittu zai baShi. Don haka suka ce Allah bai da sifa ko daya. Ba wai suna musa siffofin Allah da suke cikin Alkur’ani ba ne, suna so su kaucewa auna sifar Allah da ta halitta ne, karshe kuma hakan ya karyata fadin Allah na “laisa ka mithlihi shai’u”

A Ina Ake Samo Farin Ciki?
Kowa daga cikinmu yana son farin ciki amma yan kadan ne suka fahimci yadda za su samu farin cikin. Wanda yake zaton yin aure da kyakkyawar mata, katon gida ko samun babban mukami shi ne hanyar farin ciki yana yaudarar kansa ne kawai. Na san wadanda suka auri masu kama da larabawa amma suka karo aure da mummuna! Na san masu mukamin da suke da-na-sanin hawa matakin da suke kai.
Soyayyar da ke tsakanin mace da namiji abar sha’awa ce kawai ga wanda ba da shi ake ba. Don haka muka fi son ganin fim din India fiye da yadda muke son zaman gida da iyali. Mafi yawan abin da yake cikin aure kuwa hakuri ne dai da ake gaya mana shi. Duk ko abin da ake cewa hakuri ne a cikinsa kai ka san wahala ce a baibaye da shi.
A cikin soyayya tun asali ba komai sai bakin cikin kishi da son kai yake janyowa. Wanda ya kira budurwarsa ya ji tana waya zai gaya maka bakin cikin da yake ciki ya ninka duk wani farin ciki da ya ke samu a lokacin da suke duk wayar awanni. Kullum cikin fargabar kada a kwace maka budurwa kake, karshe kuma bayan auren mafi yawan ma’aurata da-na-sanin wanda suka aura suke! Ina wani farin ciki a nan?
Wanda ya ke zaton katon gida ko wani mai cike da alatu shi ne farin ciki don bai shiga gurin ba ne. Masu tallace-tallace a kamfanoni suna yaudararmu da nuna mana katon gida hade da iyali suna dariya domin mu siyo kayansu. Amma kuma ba sa gaya mana cewa sati daya na farko kana gidan ya isa ka dena ganin kyansa. Kuma nawa ka sani a gidajen kasa sun fi na cikin “mansion” ko “billa” jin dadin rayuwa? Nawa ka sani ba su da ko daki biyu a gidajensu amma sun fi masu daki ashirin farin ciki?
Ba mu fahimci mene ne farin ciki ba don haka ba zamu iya samunsa ta hanyoyin da muke zato ba. Wanda yake dauka farin ciki wani mataki ne da ake zuwa don a sameshi to ya yaudari kansa da kansa. Wanda ya dauka farin ciki samun wasu abubuwa ne to ya yaudari kansa da kansa. A haka kuma mutane suke ci gaba da yaudarar kansu da kansu ba su sani ba.

Kimiyya Da Nazari
Ina zaton kuskure ne babba ka ce wani abu ba zai yiwu a Kimiyya ba ko ka karyata ba tare da gwaje-gwaje ba. Tarihi yai ta karyata har masana da suka dinga nuna cewar akwai wani abu da ba zai yiwu a Kimiyya ba. Har Albert Einstein da ya musa samuwar “Black Hole” karshe ko dadewa ba a yi ba amma waki’i ya karyata shi. Yanzu gashi har hotonsa ake cewa an dauko!
Kelbin, babban masanin Kimiyyar karni na 19, ya musanta yiwuwar tashin jirgin sama saboda yana ganin duk abin da yafi iska nauyi to ba zai iya tashi sama ba. Amma ai gashi kowa ya gane kuskurensa. Har cewa ya yi X-rays karya ce da aka hadawa jama’a don a raina musu hankali. Amma yanzu waye bai gane cewa shi ne ya yi kuskure ba?
Rutherford wanda ya gano tsakiyar “atom” shi ma haka ya ce ba zai yiwu a iya yin “atomic bomb” ba. Amma ba a dade ba zamani ya ci gyaransa. A yanzu “atomic bomb” din da ya karyata yiwuwar yinsa shi ne yake tsara siyasar duniya har ake haramtawa wasu yi!
Wadannan da na lissafa dukansu babu wanda sunansu bai yi kauri a kimiyya ba. Biyu daga cikinsu (Einstein da Rutherford) sunansu na cikin “periodic table” ta Chemistry. Dayan kuwa ko yau aka yi hasashen yanayi sai an fadi sunansa (Kelbin). To amma duk waki’i ya karyatasu. Bai kamata kai ma ka tsaya cewa kaza karyane ko kaza rainin hankali ba ne.
Wanda bai yarda da wani abu a Kimiyya ba zai iya bayyana hujjojin da za a buga a manyan madaba’o’i na duniya domin a karba ko a karyata gyaran da ya kawo. Dadin Kimiyya ita ce tana dauka kowa da matsayi daya. Ana tsaka da jin cewa babu kamar Issac Newton aka samu Albert Einstein. Duk kokarin da Einstein ya yi na ya rufe bakin su Heisenberg bai yiwu ba saboda Kimiyya ta kowa da kowa ce, ba mallakar mutum daya ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!