Connect with us

RAHOTANNI

Habu Sani Ya Canji Kwamishinan ‘Yan Sandan Bauchi Da Aka Tura Yaki Da Masu Garkuwa Da Mutane

Published

on

Shalkwatan Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta fitar da wani sanarwar da ke cewar ta yi sabon ango amma na Kwamishina wanda kuma shine CP Habu Sani inda ta ce shine ya sauyi CP Ali Aji Janga da aka tura Kaduna domin yaki da masu garkuwa da mutane.
A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da mai magana da yawun Shalkwatan DSP Kamal Datti Abubakar ya fitar a jiya, ya shaida cewar sabon Kwamishina ya zo jihar ne domin ci gaba da gudanar da aikin dan sanda na kare lafiya da rayuka hadi da dukiyar jama’an jihar.
Sanarwar ta Datti na cewa ne: “Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi tana farin cikin sanar da al’umma cewar Bauchi ta yi sabon Kwamishina wanda shine CP Habu Sani Ahmadu, (psc) wanda aka turo jihar Bauchi domin ya fara aiki a ranar Litinin (jiya) wanda ya amshi kujerar a hanun CP Ali Aji Janga wanda aka sauya masa wurin aiki a matsayin sabon Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna,” A cewar Datti.
Sanarwar ta shaida cewar sabon Kwamishinan dai yana da kwarewar da sanin aikin dan sanda a cikin kasa da wajen kasa wanda asalinsa ya fito ne daga karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto, “Ya yi digirinsa a fannin ilimi kan sanin yanayi (Geography) a jami’ar Usmanu DanFodiyyo da ke Sokoto a shekarar 1990,” Kamar yadda sanarwar ta ce.
Kamal Datti ya kuma bayyana cewar sabon Kwamishinan ya tsunduma cikin aikin dan sanda ne a matsayin Mataimakin Sufiritan (CASP), “Daga wannan lokacin ya taka mukamai daban-daban a ciki da wajen Nijeriya,”
Sanarwar ta ce nadi na karshe kafin wannan da aka yi wa CP Habu Sani shine Kwamishina mai kula da sashin kwararru masu aikin da kaifin basira (FIB) a shalkwatan hukumar da ke Abuja, daga bisani yanzu an tura shi jihar Bauchi a matsayin sabon Kwamishina.
Wakilinmu dai ya labarto cewar CP Habun ya amshi mulki ne a hanun CP Ali Janga wanda ya mika masa ragamar aiki a jiya, inda shi kuma Janga aka kai shi jihar Kaduna da nufin ya bayar da gudunmawarsa don yaki da masu garkuwa da mutane da fashi da makami musamman a babban hanyar Kaduna zuwa Abuja da suka addabi matafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!