Connect with us

KASUWANCI

Kyakkyawan Tsarin Gwamnatin Ya Sa Muka Fara Sarrafa Gas A Gida – LPG

Published

on

A yayin da kamfanin yin Silindar iskar Gas na LPG ya fara janye jikinsa daga Masana’antar mai ta Techno dake a jihar Legas, Mataimakiyar Shugaba na rukuninin kamfanin na LPG Uwargida Nkechi Obi, ta danganta janyewa a bisa kyakywan tsarin da Gwamnatin Tarayya ta samar a fannin.
Ta sanar da hakan ne a lokacin da take zagaywa da manema labarai masana’antar a ranar Lahadin data gaba, inda Obi ta danganta tsarin da Gwamnatin Tarayar ta samar na yin amfani da kayan cikin gida ne ya sanya kamfanin su ya zamar masa dole ya fice daga kamfanin mai Techno yadda suma kamfanin su zai fara gina nasa masana’antar ta sarrafa Silindar iskar gas a kasar nan.
Tace, “ Mun yake shawarar bayar da tamu gudunmawar na baiwa tsarin yin amfani da kayan cikin gida ta hanyar kafa masana’antar mu yadda zamu dinga sarrafa Silindar iskar gas don dauka yin amfani da kayan cikin gida.”
Taci gaba da cewa, “ Muna da babban burin daukaka kamfanin mu LPG yadda zai dace da Nijeriya.”
Ta kara da cewar, sarrafa Silindar iskar Gas a cikin gida Nijeriya zai habaka kara bukatar da ake da ita a cikin Nijeriya.
Acewar ta, rahoton kwananan fa ya fito daga kasuwa ya nuna cewar, yanayin Silindar kamfanin sarrafa Silindar iskar Gas naTechno Gas, har yanzu masu saye sunfi bukar ta saboda ingancin da take dashi da kuma fiye da wadanda ake shigowa dasu cikin kasar nan.
Ta sanar da cewar, Masana’antar zata dinga samar da kimanin Silindoji miliyan biyar duk shekara da za’a dinga turawa kasuwanni, inda ta kara da cewa, Kamfanin mai na Techno Oil zaiyi dukkan mai yuwa wajen ganin yan Nijeriya sunyi na’am da kamfaninnna LPG.
Ta bayyana cewar, yawan adadin Silindojin da za’a sarrafa zasu wuce bukatun yan Nijeriya da kasuwanin Afirka ta Gabas, a saboda hakan muna ganin babu kuma wata bukatar kara shigo da Silindoji Gas daga kasar waje.
Mataimakiyar Shugaban ta kuma nuna jin dadin ta ganin cewar, kamfanin kamfanin na TechnoGas ya cika dukkan sharuddan hukumomin dake sanya ido a fannin, harda na Hukumar kula da ingancin SON.
Da aka tambaye ta akan kalubalen da kamfanin ta yake fuskanta na sarrafa kaya a cikim Nijeriya, Mataimakiyar Shugaban tace, kalubalen yanada dama, inda tace amma saboda kishin kasa hakan ba zai gagare su cimma nasarar da suka sanya a gaba ba.
Obi tayi kira ga Gwamnatin Tarayya data dauki kwararan matakan da zasu hada shigo da Silinda marasa inganci cikin Nijeriya daga kasashen waje, musamman ganin cewar, sun kai kashi 95 busa dari na yadda ake rabar dasu a cikin kasar nan.
Acewar Obi, dole ne a yabawa Gwamnatin Jihar Legas saboda samar da kyakyawan yanayi data yi ga kamfanim mai na Techno don ya gudanar da aikin sa, inda kuma ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya samar da kyawawan tsare-tsare da zasu sanya a dinga zuba jari na cikin gida a fannin.
Obi wadda tana daya akan gaba wajen yin gangamin a rungumi yin girki da iskar gas a Nijeriya, tace, yin amfani da LPG zai taimaka wajen kare gurbatar muhalli kuma za’a dinga adana kudi tare da habaka tattalin arzikin Nijeiya.
Acewar ta kamfanin na mai na Techno ya shiga cikin dabarun hadaka din daukaka kamfanin na LPG ta hanyar yin amfani da daidaikun mutane da kuma cibiyoyi dake fadin kasar nan.
A karshe Obi tace, gidaje da dama dake cikin fadin Nijeriya, tuni sun fara yin amfani da LPGl maimakon yawan yin amfani da itace, Kwal da sauran hanyoyin yin girke-girke masu hadarin gaske.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!