Connect with us

WASANNI

Modric Zai Bar Real Madrid Bayan Rikici Da Zidane

Published

on

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Luca Modric, zai bar kungiyar a karshen wannan kakar da take kokarin karewa kamar yadda rahotanni suka bayyana sakamakon rashin jituwa da kociyan kungiyar, Zinadine Zidane.
Modric, wanda ya shafe shakru shida da rabi a Real Madrid ya bugawa kungiyar wasanni da dama kuma ya lashe kofuna daban daban tun bayan komawarsa kungiyar daga Tottenham dake kasar Ingila.
A kakar wasan data gabata ne dai aka bayyana cewa dan wasan, dan asalin kasar Crotia, ya amince zai koma kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan dake kasar Italiya sai dai daga baya Real Madrid ta hanashi tafiya a lokacin tsohon kociyan kungiyar Julian Lopetegui wanda kungiyar ta kora watanni hudu bayan yafara aikin koyar da ‘yan wasanta.
Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa Modric da Zidane sun samu sabani a filin daukar horo wanda hakan yasa yaga bazai iya cigaba da zaman kungiyar ba kuma tuni kungiyoyi irinsu Manchester United da Inter Millan suka fara zawarcinsa.
Sai dai duk da haka Modric yana cigaba da bugawa Real Madrid wasa amma kuma ana ganin wannan kakar wasan itace ta karshe a wajen dan wasan sakamakon kociyan kungiyar yana shirin siyan sababbin ‘yan wasan da yake ganin zasu taimaka masa.
Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai, Florentino Perez, ya bayyana cewa kungiyar zata kashe makudan kudade a kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa idan an bude domin kara karfin kungiyar bayan da kungiyar tayi abin kunya a bana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!