Connect with us

RAHOTANNI

Mutum 70 Da Kamfanoni Bakwai Sun Rasa Kadarorinsu Ga Hukumar EFCC

Published

on

Akalla kadarori 214 ne da ke sassan kasar nan daban-daban mutane 70 da kamfanoni 7 suka mika mallakan su ga hukumar yaki da cin hanci da karban rashawa EFCC.
Kadarorin da hukumar ta EFCC ta sami nasarar kwatowa a tsakankanin shekarar 2015 da ta 2018, suna nan ne a Jihohin, Abuja, Lagos, Kaduna, Katsina, Jigawa, Kogi, Adamawa da Jihar Oyo.
Kimanin kadarori 179 daga cikin su, duk hukumar ta kwato su ne ta hanyar karbe mallakan su a bisa umurnin Kotuna, 35 daga cikin su tuni hukumar ta sami cikakken izinin mallakin su, biyu daga cikin su kuma masu su ne suka sallama wa hukumar a kashin kansu.
Wasu daga cikin ‘yan Nijeriyan da suka rasa kadarorin na su ga hukumar ta hanyar karban mallakan su a kotuna sun hada da, tsohuwar Ministar Mai, Diezani Alison-Madueke; da tsohon mai baiwa Shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki.
Sauran sun hada da, tsohon Minista, Iyorchia Ayu; da marigayi babban hafsan tsaro na kasa, Aled Badeh da tsohon babban hafsan dakarun sama na kasar nan, Aeya Marshal Adesola Amosu (mai ritaya).
Sauran sun hada da, tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose; tsohon Gwamnan Jihar Bauci, Isa Yuguda; Kanar Bello Fadile (mai ritaya); da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, da dai sauran su, duk sun rasa wasu kadarorin su a Kotuna zuwa ga hukumar ta EFCC.
A cewar rahotannin, jerin sunayen wadanda suka rasa kadarorin na su sun hada da, George Turner, wanda ya rasa kadarori har 17 da ke sassa daban-daban na Jihar Bayelsa, tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, da Garba Birnin-kudu, wanda kowane daya daga cikin su ya rasa kadarori 14 ga hukumar ta EFCC.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!