Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Sallamar So’

Published

on

Suna: Sallamar So
Tsara Labari: Jamilu Nafsin
Kamfani: Nuhu Mobietone
Shiryawa: Mustee Junior
Bada Umarni: Ali Nuhu
Jarumai: Sadik sani sadik, Ali nuhu, Tijjani asase, Rahma sadau, Ladidi fagge, Hajara usman, Bilkisu shema. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar.

A farkon fim din an nuna Mubeena (Rahma Sadau) ta shiga cikin dakin su wajen mahaifiyar ta (Hajara Usman) a inda mahaifiyar ta ke nuna jin dadin ta bisa zaman aikatau da suke yi a gidan su kawar Mubeena wadda ta dauko su daga cikin wahala ta dawo dasu nan gidan don su dinga yin aikatau. A daidai wannan lokacin ne Kubra ta shigo cikin dakin (Bilkisu Shema) ta kira Mubeena akan tazo tayi mata rakiya don zuwa filin saukar jirgi inda zasu taro masoyin ta Ahmad (Sadik Sani Sadik) bayan Kubra ta zauna a dakin ta sai Mubeena tayi mata kwalliya tana yaba kyawun da tayi gami da tabbatar mata cewar yau sai Ahmad ya yaba sosai da irin kyawun ta, hakan ne ya saka Kubra jin dadi har ta soma tunanin ga Ahmad ya dawo kuma ya furta kalmar so a gareta.
Amma abin takaicin sai gashi bayan dawowar Ahmad kowa yana murna da ganin sa amma sai Mubeena ta tsaya don ya yaba kwalliyar ta, amma bisa mamaki sai Ahmad bai yi mata kallon kirki ba ma, yazo shiga cikin gida ne yayi kicibus da Mubeena zata fito, hakan yasa ya bita ta da kallon tambaya. Tun daga wannan lokaci sai Kubra ta cusawa kanta damuwa akan rashin kulawar da Ahmad ya nuna mata, amma sai Mubeena ta rarrashe ta ta nuna mata komai zai daidai ta. Bayan anyi haka sai Mubeena taje hadawa Ahmad abinci, amma sai ya bukaci ta zauna su ci tare, sai hakan bai yiwa Kubra dadi ba duk da Mubeena din bata zauna sun ci ba. Bayan dan wani lokaci kuma sai Kubra ta soma jan sa a jiki don ta bayyana masa irin son da take yi masa, amma sai ya bukaci ta damo masa fura ta kawo masa, Kubra sai bata ji dadin hakan ba kuma sai ta tura Mubeena ta hada masa furar ta kai masa.
Tun daga sannan Ahmad ya fara bawa Mubeena wani matsayi a cikin zuciyar sa har ma ya tambayi sunan ta kuma ta fada masa.
Mubeena ta fita wajen wani saurayin ta wanda ya kawo mata takardar samun aiki a wani wajen sayar da abinci (restaurant) bayan ta dawo gida da murna sai suka hadu da Ahmad zai fita da motar sa, anan ya bukaci tazo ta raka shi unguwa kuma zai kai ta wajen sayar da abinci don ta kai musu takardar shaidar samun aikin da tayi. Haka dai Mubeena taje ta fadawa mahaifiyar ta sannan ta fito suka tafi, tun Ahmad yana jan Mubeena da hira tana no’kewa har ta saki jiki dashi suka dinga hira cikin nishadi.
A wannan lokacin ne Ahmad ya bukaci Mubeena ta zamo kamar abokiyar sa don ta dinga debe masa kewar abokin sa wanda yayi tafiya, amma sai Mubeena ta nuna masa hakan ba mai yiwuwa bane domin ‘yar uwar sa Kubra ce ta dace da samun wannan matsayin ba ita bace ba, nan take Ahmad ya nuna fushin sa akan shi ko zancen Kubra ba ya so ta sake yi masa. Bayan sun je wajen da Mubeena zata fara aiki sun fito sai suka je wajen sayar da kaya sukayi siyayya, daga nan kuma suka wuce gida, a kokarin shigar su gida ne Kubra ta gansu ta soma fushi, amma ganin Mubeena ta kawo mata kayan da Ahmad ya saya mata sai ta sauko daga fushin ta soma murna. Lokacin da Mubeena ta fara aiki a wajen sayar da abinci sai Ahmad ya samu damar kebewa da ita domin duk sanda zata fita shi yake kai ta kuma ya dauko ta idan lokacin dawowar ta yayi. Kubra duk ta soma lura da abinda ke faruwa amma bata nuna damuwar ta sosai ba saboda ganin Mubeena kawar ta ce kamar ba zata ci amanar ta ba. Sai kwatsam wata rana Kubra ta tashi da rashin lafiya, mahaifiyar ta Hajiya Maryam (Ladidi Fagge) ta bukaci Ahmad ya kai Kubra asibiti, nan take kuwa Ahmad ya dauke ta suka tafi, amma tun kafin su isa asibiti sai ya nemi alfarmar Kubra ta bashi izini ya shiga wani gidan cin abinci don gabatar da wani uzurin, Kubra batayi musu ba ta amince amma ko da ya bukaci tazo su shiga ciki tare sai taki amincewa, ta zauna a cikin mota. Da shigar Ahmad gidan sayar da abinci sai suka hadu da Mubeena suka fara hira cikin raha da nishadi, anan ne yake fada mata cewar Kubra ce bata da lafiya ya dauko ta don zuwa asibiti.
Mubeena ta nuna alhini gami da cewa su fito ta yiwa Kubra sannu, hakan ko akayi suka fito suna hira har ma Mubeena ta mance ta fito rike da kayan farantan da aka gama cin abinci, har sai da wani ma’aikacin wajen ya biyo ta ya karbi kayan hannun ta yana zolayar ta akan taga masoyi ta rude. A sanda suke wannan rahar ne Kubra ta bude mota ta fito tana kallon su cikin mamaki, daga bisani tayi fushi ta juya tayi tafiyar ta. Mubeena da Ahmad suka iso gaban motar amma bisa mamaki sai ba su ga Kubra ba, Mubeena ta soma tunanin ko fushi Kubra tayi ta koma gida, nan ta bukaci Ahmad akan yabi bayan ta, amma sai ya tubure yace babu inda zai je, haka suka tsaya a wajen suka cigaba da hirar su. Yayin da ita kuma Kubra ta dawo gidan su a cikin motar haya, ta sauka a fusace ta shige cikin gida.
Kubra na kai komo a cikin dakin ta ranta matukar bace, sai ga Mubeena ta dawo daga aiki ta shigo cikin dakin tana yi mata magana. Amma bisa mamaki sai Mubeena taga Kubra ta bita da mugun kallo gami da jan tsaki sannan ta juya ta fice daga cikin dakin, Mubeena tabi bayan ta da kallo cikin mamaki ba tare da ta sake yin magana ba. Kubra ta nufi wajen Ahmad ta soma tuhumar sa inda suka je shi da Mubeena amma sai yaji fada mata. Cikin dan lokaci kadan Kubra ta soma kokarin gyara halin ta, inda ta fara hadawa Ahmad abincin karin kumallo da kanta, har mahaifiyar Mubeena (Hajara Usman) ta fito tana mamakin hakan, yayin da itama mahaifiyar Kubra ta soma zolayar ta, a sannan ne Ahmad ya fito cikin shirin fita, Kubra ta nuna masa abincin sa amma sai ya nuna bazai ci ba, Mubeena ma ta fito daga cikin daki cikin shirin fita zuwa wajen aiki, nan take suka fita ita da Ahmad ya dauke ta a motar sa suka fice daga cikin gidan.
Ashe duk abinda ya faru na game da fitar su a mota duk ya faru ne akan idanun Kubra wadda ke can saman bene tana kallon su, ai kuwa sai ta fashe da kukan bakin ciki ta sauka kasa don zuwa wajen mahaifiyar ta Hajiya Maryam, nan take Hajiya Maryam ta rike ta tana tambayar ta abinda ke faruwa, amma sai Kubra ta kasa yin magana ta cigaba da rusa kuka, hakan ne ya tashi hankalin mahaifiyar ta ta rasa abinda yake yi mata dadi.
Mubeena da Ahmad suna tafe a cikin mota sai ya fahimci cewa tana cikin matsanan ciyar damuwa, amma ko da Ahmad ya tambaye ta abinda ke faruwa sai ta bayyana masa cewar bata jin dadin alakar dake tsananin shi da ita, domin hakan ya soma sauya kyakykyawar alakar dake tsakanin ta da kawar ta Kubra, don haka tana bukatar abotar su ta dakata haka, jin hakan ne yasa Ahmad yayi fushi kuma yaki bata goyon baya akan alfarmar da ta nema a wajen sa. Haka dai Mubeena ta sauka daga motar sa ranta a bace ta shige wajen aikin ta tana kuka.
Bayan Ahmad ya koma gida ne sai Hajiya Maryam wadda suke zaune suna hira tare da mahaifiyar Mubeena. Hajiya Maryam ta tsayar da Ahmad tana tambayar sa abinda ke tsakanin sa da Mubeena da kuma irin rashin kyautatawar da yayiwa Kubra, jin an soma wannan maganar ne yasa mahaifiyar Mubeena ta tashi ta basu waje, yayin da itama Kubra ta rutsa Ahmad tana gaya mishi cewar duk kwalliyar da take saboda shi take yi, amma sai ya bata hakuri ya nuna shifa sam ba ya ra’ayin ta, nan sukayi baram baram ran kowa cikin su ya baci.
Bayan Mubeena ta dawo daga wajen aiki sai mahaifiyar ta Hajara Usman ta nuna mata lallai ya zama dole ta rabu da Ahmad ta bar wa Kubra domin Kubra tayi musu dukkan halasci a rayuwa wanda ya dace su saka mata da alheri ba sharri ba. Mubeena ta amince da maganar mahaifiyar ta, a sannan ne kuma Ahmad ya kira wayar Mubeena ya nuna yana son ganin ta da gaggawa. Bayan Mubeena ta fita zuwa wajen sa ne ta nuna lallai ya rabu da ita yaje ga ‘yar uwarsa wadda tafi bukatar sa, jin hakan ne ya bata ran Ahmad cikin fushi ya nuna ya rabu da ita duk da yaso suyi rayuwa tare, ganin ya tafi ya bar ta ne sai hankalin ta ya tashi ta soma kuma tunanin halaccin da Kubra tayi musu tun suna zaune a gidan haya inda Mubeena ke soyayya da Haris (Ali Nuhu) sun gama cin burin zama miji da mata sun shaku sosai, amma sai yayan sa (Tijjani Asase) yaki yarda da zabin kanin sa Haris domin bayaso kanin sa ya auri ‘yar talakawa. Shi kuma Haris matsayin sa na mai biyayya ga yayan sa sai ya amince zai rabu da Mubeena kuma ya nemi alfarmar yayan sa akan ya tura shi can kasar waje don cigaba da zama acan. Yayan sa ya amince da hakan, nan take shima Haris yaje yayi bankwana da Mubeena suka rabu cikin rashin jin dadi. Rabuwar Haris da Mubeena babu jimawa ne aka kori su Mubeena daga gidan hayar da suke zaune, a sanda ake watso kayan su waje ne mahaifiyar Kubra wato Hajiya Maryam anzo wucewa da ita a mota sai taga hakan.
Nan take kuwa tazo ta dauki su Mubeena suka koma gidan su. Bayan Mubeena ta gama tunani ne sai ta dawo cikin gida a sanda Ahmad ya kwashe kayan sa yabar gidan duk da Kubra bataso tafiyar sa ba, amma bayan ya tafi sai ta fusata ta nuna lallai sai Mubeena da mahaifiyar ta suma sun bar gidan. Hakan kuwa akayi Mubeena da mahaifiyar ta suka bar gidan rayukan su duk a bace. Suna tafe akan hanya ne suka hadu da abokin Ahmad, bayan sun gaya masa abinda ke faruwa sai ya kira Ahmad, nan take Ahmad ya samar musu da wajen zama na dan wani lokaci, amma sai mahaifiyar Mubeena ta nuna tana so su sasanta da mahaifiyar Kubra saboda sun yi musu halaccin da bai kamata su butulce musu ba. Ahmad ya dauko mahaifiyar sa suka dunguma gaba daya suka je gidan su Kubra.
Cikin dan lokaci kadan mahaifiyar Ahmad ta fahimtar da mahaifiyar Kubra rashin dacewar auren Ahmad da Kubra tunda baya son ta kada ayi abinda za’a yi nadama. Jin hakan ne yasa Kubra da mahaifiyar ta suka fahimta kuma Kubra ta hakura da auren Ahmad ta bar wa Mubeena. Gaba daya suka sasanta kan su kuma Mubeena da mahaifiyar ta suka dawo suka cigaba da zama a gidan su Kubra.

Abubuwan Birgewa:
1- Jaruman sun yi kokari wajen isar da sakon labarin, musamman Bilkisu Shema wadda ta kasance sabuwar jaruma.
2- Wakar da akayi tsakanin Rahma Sadau da Ali Nuhu tayi dadi kuma ta nishadantar.
3- An samar da wurare masu kyau wadanda suka dace da labarin.

Kurakurai:
1- Kubra taje dakin su Mubeena ta bukaci ta shirya su je filin saukar jirgi don taro Ahmad, amma sai ba’a ga zuwan su can filin saukar jirgin ba, kawai sai ganin Ahmad aka yi ya dawo shi da abokin sa. Shin su Kubra canja shawara sukayi suka fasa zuwa? Ko kuma dama an yi maganar zuwan su filin jirgi ne don a nuna wa mai kallo cewa za’a yi ba’ko a gidan?
2- Lokacin da Kubra tayi fushi ta baro Ahmad a wajen sayar da abinci abinci, bayan ta fito daga motar tasi din da ta kawo ta gida babu mayafi a jikin ta, matsayin Kubra na musulma kuma bahaushiya, bai kamata ta fita daga gida babu mayafi a jikin ta ba, domin addini da al’adar ta basu bata damar yin hakan ba.
3- Ya kamata a nuna wa dan kallo alakar dake tsananin Ahmad da Kubra, domin an nuna su tamkar wa da ‘kanwa, to amma sai aka ga Kubra na nuna masa soyayya irin ta aure, idan kuma alaka ce ta ‘yan uwan taka to ya dace tun farko a nuna wa mai kallo hakan.
4- Lokacin da aka kori su Mubeena daga gidan da suka kama haya, shin ina mahaifiyar ta take a sanda ake yi musu watsi da kaya? Ya dace a gan su gaba daya a wajen, idan kuma unguwa mahaifiyar ta taje ya dace ko da baki ne ayi bayanin hakan.
5- An ga lokacin da Ahmad ya kwashe kayan sa daga gidan su Kubra yace zai tafi garin su, shin wacce irin alaka ce tsakanin sa da su Kubra wadda har tasa bayan dawowar sa daga kasar waje ya sauka a gidan su Kubra bai sauka a gidan su ba? Kuma wacce irin alaka ce tsakanin mahaifiyar Ahmad da mahaifiyar Kubra?

Karkarewa:
Labarin ya nishadantar, musamman ga ma’abota son kallon fim din soyayya, amma ya dace a fito da muhimmin sakon da ake son isarwa ga mai kallo.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!