Connect with us

RAHOTANNI

’Yar Shekara 20 Mai Gani Garara-garara Ta Sami Sukolaship Din Kasar Katar

Published

on

Wata yarinya ‘yar shekaru 20, wacce kuma ta ke da lalurar gani garara-garara, mai suna Fatima Bala, ta sami lashe kyautar sukolaship daga kungiyar bayar da tallafi ta kasar Katar, jim kadan da kammala karanta wasu ayoyi daga cikin Alkur’ani Mai Girma, a wajen bukin rarraba Alkur’ani 100 na karatun makafi wanda kungiyar ta shirya a Sakkwato. Tun tana da shekaru shida ne, Fatima ta rasa ganinta a wani rikitaccen yanayi.
Da take magana da manema labarai, Fatima cewa ta yi, babban makasudin ta shi ne ta zama Likita, amma sabili da alin da ta tsinci kanta a ciki sai ta yanke shawarar ta karanci ko dai harshen Turanci ko kuma na Larabci a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkawato. Amma ba zan iya zama a cikin Jami’ar ba, saboda yanayin da nake a cikinsa. Ba ina da matsala da gani na ne ba kadai, ina ma da matsala da kafafuna. A kan hakan, ba na iya yin tafiya na wuri mai nisa, ka kuma san wasu Ajujuwan daukan karatun suna nesa ne da junansu da kuma dakunan kwanan dalibai.
“Na yi murna da samun wannan Skolaship din, domin na san za kuma su yi tunanin taimaka mani da sauran wasu abubuwan da za su saukake mani zama a dakunan kwanan daliban domin ci gaba da karatuna. Wannan kuma shi ne mafarki na, na sami taimakon da zai ba ni damar ci gaba da karatun nawa, domin a halin yanzun, takardun shaidar kammala karatun Sakandare ne kadai nake da su, ina kuma son na ci gaba.”
Shi ma da yake magana da manema labarai, babban Sakataren hukumar bayar da tallafin ta kasar ta Katar, a nan Nijeriya, Dakta Hamdi Muhammad, cewa ya yi, kungiyar bayar da tallafin za ta dauki nauyin ci gaba da karatun nata, bayan ta sami izinin shiga jami’ar a cikin kasar. A cewar shi, ita kungiyar ta su tana bayar da taimako ne a kan harkokin da suka shafi na Ilimi, domin tabbatar da kowa ya sami ilimi, musamman mutanan da suke da wata nakasa a tattare da su.
Ya ce, gidauniyar na su ta bayar da taimakon 10,000 ga sama da marayu 1000 da ke cikin Jihohi 15 na kasar nan, baya ga makarantu, Masallatai da rijiyoyin burtsatse da ta gina. Ya bayyana cewa, gidauniyar ta su za ta raba Kur’anan karatun makafin guda 1000 a wannan shekarar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!