Connect with us

WASANNI

Zidane Ya Bayyana Za A Yi Canje-canje A Real Madrid

Published

on

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane, ya bayyana cewa dole idan kakar wasa ta kare akwai canje-canje da zasu faru a kungiyar wanda zaisa wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar zasu bar kungiyar.
Real Madrid ta yi nasarar doke kungiyar Billareal daci 3-2 a wasan mako na 36 a gasar cin kofin La Liga da suka fafata a filin wasa na Santiago Bernabeu ranar Lahadi kuma Real Madrid ta ci kwallayen ne ta hannun dan wasa Jesus Ballejo da kuma Mariano Diaz da ya ci guda biyu, yayin da Billareal ta zare biyu ta hannun Gerard Moreno da kuma Jaume Costa.
A wasan farko da kungiyoyin biyu suka buga a gasar ta La Liga bana ranar 3 ga watan Janairu tashi suka yi 2-2 a lokacin tsohon kociyan kungiyar ta Real Madrid, Santiago Solari, wanda kungiyar ta kora.
Saura wasanni biyu a kammala gasar La Ligar shekarar nan, wadda Barcelona ta lashe kofin, kuma na 26 jumulla, inda Lionel Messi ya ci laliga ta 10 a kungiyar sai dai har yanzu Real Madrid tana nan a matakinta na uku da maki 68, ita kuwa Billareal ita ce ta 14 da maki 40.
Sauran wasannin da suka rage wa Real Madrid sun hada da zuwa gidan Sociedad ranar 12 ga watan Mayu da wasan karshe a filin wasa na Santiago Bernabeu da Real Betis ranar 19 ga watan nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!