Connect with us

Nahiyar Afirka

An Cimma Yarjejeniyar Kafa Gwamnati A Sudan

Published

on

Sojoji da kuma jagororin masu zanga-zangar neman sauyi a kasar Sudan sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin riko wadda za ta share tsawon shekaru uku kafin shirya sabbin zabubbuka a kasar. Janar Yasser Atta, memba a majalisar koli ta mulkin sojin kasar ne ya sanar da kulla wannan yarjejeniyar bayan share tsawon kwanaki ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

A lokacin wannan tattaunawa, wadansu sun bukaci amincewa da wa’adin shekaru 2 a matsayin na rikon kwarya, yayin da wasu suka bukaci shekaru 4, inda daga karshe aka amince da shekaru 3 a cewarsa.

Janar Atta ya ce, watanni shidan farko za su kasance na tattaunawa ne domin samar da zaman lafiya da kungiyoyin ‘yan tawaye da ke yammaci da kuma kudancin kasar. Hari wala yau yarjejeniyar ta amince da kafa majalisar dokoki ta rikon kwarya mai kujeru 300, kuma kashi 2 cikin uku na wakilan majalisar za su kasance wakilan masu zanga-zanga, yayin da sauran za su fito daga jam’iyyun siyasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!