Connect with us

LABARAI

An Saukaka Hanyar Neman Biza Ga Baki A Nijeriya

Published

on

Hukumar Kula da Shige da Ficen Kasa ta Nijeriya (NIS), ta kaddamar da wani sabon sauyi a tsarin neman takardar izinin shiga kasa (Biza) ga baki wadanda sukan nemi takardar a yayin da suka shigo Nijeriya nan take.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta NIS, DCI Sunday James a madadin shugaban hukumar, Muhammad Babandede, ta yi bayanin cewa a halin yanzu masu neman takardar izinin shiga kasa yayin da suka iso Nijeriya za su gabatar da bukatar yin hakan ne ta adireshen shafin intanet na hukumar.

“Daga ranar Litini 13 ga watan Mayun 2019, Hukumar NIS na sanar da jama’a cewa ta mayar da tsarin neman takardar izinin shiga kasa yayin da baki suka iso cikin kasa nan take zuwa shafin intanet. Kafin bullo da wannan sabon tsarin na neman takardar masu nema kan aika da bukatarsu ce ta adireshin imail ko kuma aikawa da takardar bukatarsu ga shugaban NIS domin neman amincewa, amma a halin yanzu da aka mayar da tsarin a shafin intanet, kawai ana bukatar masu neman takardar izinin su shiga shafin intanet na hukumar ta adireshinta na www.immigration.gob.ng inda za su gabatar da bukatarsu, su biya kudi tare da samun rasidin biya duk ta intanet,” in ji takardar sanarwar.

Takardar sanarwar ta kuma bayyana cewa shugaban NIS, Muhammad Babandede yana kira ga sahihan masu zuba jari daga waje su ci gajiyar wannan dama da aka ba su ta sabon tsarin neman izinin shiga Nijeriya nan take, kasancewar zai kara inganta sha’anin shige da ficen kasa, da tabbatar da gaskiya da rikon amana a tsarin, kamar yadda yake kunshe a tsarin manufar Gwamnatin Tarayya ta saukaka hada-hadar kasuwanci a cikin kasa Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!