Connect with us

KASASHEN WAJE

ANC Ta Sake Samun Nasara A Zaben Afrika Ta Kudu Da Karancin Rinjaye

Published

on

Jam’iyyar ANC a Afrika ta kudu ta sake nasarar lashe babban zaben Kasar da ya gudana cikin makon jiya, sai dai wannan ne mafi munin sakamako da ta taba samu a tarihi wanda ke da alaka da zarge-zargen rashawa da kuma nuna wariyar launin fata da ya dabaibaye gwamnatin mai ci.

Sakamakon dai ya nuna ANC ta samu Kasa da kashi 60 na kuri’un da aka kada, duk kuwa da matsayinta na wadda ta jagoranci Kasar tun bayan juyi-juya halin 1994 da ya kawo karshen tasirin farar fata a Kasar karkashin jagorancin Nelson Mandela. Sai dai duk da hakan ANC ta samu isasshen kujeru a majalisa da za su bai wa Shugaba Cyril Ramaphosa damar ci gaba da jagoranci Kasar har zuwa nan da shekaru 5 masu zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!