Connect with us

WASANNI

Atletico Madrid Ta Hakura Griezman Ya Koma Barcelona

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta fara hakura da dan wasanta Antonio Griezman, wanda ake rade radin cewa zai koma Barcelona bayan da aka bayyana cewa tattaunawa tayi nisa tsakanin dan wasan da Barcelona.

A kakar wasan data gabata dai dan wasan ya kusa komawa Barcelona kafin daga baya ya canja shawara dab da fara gasar cin kofin duniya inda ya bayyana cewa zai cigaba da zama a kungiyar tasa saboda an dakatar da kungiyar daga siyan ‘yan wasa sakamakon laifin da Fifa ta kama kungiyar dashi.

Sai dai a kwana kwanan nan maganar komawar dan wasan Barcelona ta sake zama sabuwa bayan da tuni wasu rahotanni suka bayyana cewa dan wasan ya gama Magana da shugabannin Barcelona akan albashin da zai dinga karba idan ya amince da komawa.

Dan wasan wanda yake da farashin fam miliyan 173 farashin nasa zai ragu daga daya ga watan Yuni zuwa 104 wanda hakan zaisa Barcelona ta koma domin ta sake gwadawa ko kungiyar da dan wasan yake zata hakura ta siyar da Griezman dan asalin kasar Faransa.

Dan wasan dai ya zura kwallaye 21 cikin wasanni 46 daya bugawa kungiyar kuma ya taimaka an zura kwallaye 10 a wannan kakar ta bana yayinda kuma a halin yanzu kungiyar tana mataki na biyu akan teburin laliga na bana.

Tuni dai kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta gama amincewa bazata kasance tare da dan wasan ba a kakar wasa mai zuwa kuma shugabannin kungiyar sun shirya tattaunawa akan dan wasan domin fara Magana da Barcelona.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!