Connect with us

RAHOTANNI

Ba Mu Ji Dadin Yadda A Ka Gudanar Da Zaben Gwamnan Kano Ba

Published

on

Shugaban kungiyar ‘Kwankwasiyya Kyakkyawan Mataki’ a unguwar Alaba Rago, Alhaji Auwalu Idiris dan asalin Wangara ta karamar hukumar Gezawa da ke jihar Kano, wanda ya ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a unguwar Alaba ta cikin garin Legas ya bayyana cewar ba su ji dadin yadda a ka gudanar da zaben gwamna na 2019 a jihar Kano ba.

Alhaji Auwalu Wangara ya yi wannnan tsokaci ne a unguwar Alaba a Legas a lokacin  da kungiyar ta ke gudanar da dan kwarya-kwaryar taro na bayar da shawarwari a kan abubuwan da za su ciyar da kungiyar gaba a duk fadin jihar Legas da Nijeriya bakidaya.

Amma sai ya yi kira ga mambobin kungiyar da su rungumi kaddara tare da nuna ikilasin cewar haka Allah ya kaddaro mu su, sannan kuma su cigaba da zaunawa lafiya da sauran al’ummar jihar Kano tare da gudanar da addu’o’i na musamman, domin jihar Kano ta cigaba da zama lafiya.

Sai kuma ya umarci mambobin kungiyar su cigaba da hada kawunan junansu a kowane lokaci domin kungiyar ta samu cigaba mai dorewa a jihar Kano da Nijeriya bakidaya.

Da ya juya a kan rarraba masarautar Kano kashi biyar ta koma shiyya-shiyya kuwa ya  cigaba da cewa babu shakka idan a ka yi haka an samu cigaba a wani bangare, yayin da a wani bangare kuwa an samu akasin hakan.

A cewarsa  duk inda a ka nada wani sarki mai daraja kamar ta Sarkin Kano, wanda zai kula da wadansu hakimai na wasu kananan hukumomin yankinsa a nan an samu cigaba. Amma in ji shi “kafin hakan an tuntubi talakawa su na son hakan ko kuwa ba su so? Idan su na son haka, an yi daidai. Idan kuwa ba su son haka, to ka ga akwai matsaloli.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!