Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Babu Wayewar Kan Wani Bil Adama Da Ta Fi Ta Wani

Published

on

A ranar Laraba 15 ga wata ne, aka bude babban taron tattaunawa kan wayewar kan Asiya a nan birnin Beijing, mai taken “cudanya a tsakanin nau’o’in wayewar kan Asiya da koyi da juna don raya makomar bil Adama ta bai daya”, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana ra’ayin kasar Sin kan yadda za a yi cudanya a tsakanin nau’o’in wayewar kan Asiya da na bil Adama da ma yin koyi da juna. Ya kuma jaddada cewa, akwai bambancin launin fata da harsuna a tsakanin bil Adam, amma babu wayewar kan bil Adama da ta fi wani. “Maganar banza ne, a ce wai kabila da wayewar kan wani ya fi na wasu, sannan hauka ne, wani ya ce zai canza ko kuma maye gurbin wayewar kan wasu.” Wannan ra’ayi ya samu amincewar shugabanni, jami’ai, kwararru, masana, wakilan kafofin watsa labarai na kasashe daban daban wadanda suka halarci taron matuka.
A cikin ‘yan kwanakin baya, da gangan wasu ‘yan siyasa na yammacin duniya suka fara kokarin gabatar da ra’ayin “Rigingimun wayewar kai”, har ma sun furta wasu maganganu banza cewa, wai babu shakka wayewar kai daban daban za su haifar da kiyayya ga juna. A wannan yanayin da ake ciki, an kira babban taron tattaunawa kan wayewar kan Asiya kamar yadda aka tsara, wanda Shugaba Xi ya gabatar yau shekaru biyar da suka wuce, kuma sassa daban daban sun yaba da wannan lamari.
Muddin ana bukatar samun zaman lafiya da kanciyar hankali da wadata da mu’ammala a tsakanin kasashen Asiya, to akwai bukatar karfin al’adu da wayewar kai, gami da karfin tattalin arziki da kimiyya da fasaha. Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a girmama juna da zaman daidai wa daida a tsakanin nau’o’in wayewar kai. Duk wani wayewar kai na da daraja, babu wanda ya fi wani. “Idan wayewar kan bil Adama ta kasance salo daya, to babu wani abin sha’awa ko kadan a duniyarmu.”
Wannan furuci na Shugaba Xi ya mayar da martani sosai ga kalaman banza ta wasu ‘yan siyasar yammacin duniya ke yi. Shi ma firaminitan kasar Malaysia ya nanata yayin da yake zantawa da kafofin watsa labarai, cewar Malaysia ba ta tsoron kasar Sin, saboda a cikin shekaru 2000 da ta yi cudanya da Sin, Sin ba ta taba mallaka ko mamaye Malaysia ba, ganin yadda Sin ke da ka’idojin kyautata wa makwabtanta da samun jituwa a tsakaninsu ko da yaushe.
“Ya kamata a mutunta juna da zaman daidai wa daida, a yi koyi da juna tare da bude kofa ga juna da yin hakuri da juna domin neman samun sabon ci gaba da zai dace da ci gaban zamani.” Wannan shi ne ra’ayoyin da shugaba Xi Jinping ya gabatar kan yadda kasashen Asiya da na duniya za su karfafa cudanyar al’adunsu da koyi da juna domin raya makomar Asiya da ta bil Adama ta bai daya. Haka kuma ya jaddada cewa, wayewar kai ta yi kama da duk wani nau’i mai rai, idan ba ta yi cudanya da wasu na dogon lokaci ba, to za ta tabarbare.


Tilas ne a raya al’adu ta hanyar yin mu’amala da juna da koya juna, abin da ya fi dacewa da dan Adam shi ne yin mu’amalar al’adu da juna. A shekarar 2018, al’ummar Sin miliyan 160 sun je yawon shakatawa a kasashen waje, kana Sin ta karbi masu yawon shakatawa daga kasashen waje miliyan 140. Karin Sinawa suna kara ganin al’adun kasashen waje daban daban, kana su ma ‘yan kasashen waje sun ga ci gaban da Sin ta samu a fannin tattalin arziki da kuma al’adun gargajiyarta.
A shekarar da ta gabata, shugaba Xi Jinping ya taba bayyana cewa, ya kamata a tsara tunanin zaman daidaito da koyi juna da yin shawarwari da fahimtar juna, da daidaita matsalar al’adu ta hanyar yin mu’amala da juna da koyi juna, a hannu guda kuma da kasancewa tare. A wannan shekara, ya gabatar da taswirar cimma wannan buri, ciki har da gudanar da ayyukan kare kayayyakin al’adu na Asiya, da gudanar da shirin fassara fitattun littattafan Asiya, da kuma shirin hadin gwiwar wasan kwaikwayo na Asiya, kana za a kara yin mu’amala a tsakanin matasa, da kungiyoyi masu zaman kansu, da kananan hukumomi, da kafofin watsa labaru da sauransu, da bullo da tsarin hadin gwiwa na masana, da kuma gudanar da shirin raya yawon shakatawa a Asiya da sauransu.
‘Muna fatan mu da kan mu za mu kara raya al’adun mu, da samar da sharadi ga raya al’adun sauran kasashen duniya, matakin da zai taimaka wajen raya al’adu iri daban daban a duniya baki daya’, kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana a jawabin da ya gabatar a yau Laraba, wanda wakilan kasa da kasa suka nuna amincewa da shi. Domin a ganinsu, kasar Sin ba kasa ba ce kawai, a kasa ce ta nahiyar Asiya da kuma duniya. Kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje da ba da gudummawa wajen raya al’adu yayin da take kokarin neman samun kyakkyawar makoma.

(Masu fassarawa: Kande Gao, Zainab Zhang, ma’aikatan sashen Hausa na CRI)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!