Connect with us

LABARAI

Boko Haram: Sojoji Sun Kubutar Da Mutum 54 A Jihar Borno

Published

on

Rundunar sojojin Nijeriya ta bayyana yadda dakaru a barikin 22 a karkashin Lafiya Dole; da ke aikin samar da tsaro a arewa maso gabas, tare da hadin gwiwa da yan sa kai, a kokarin karkade mayakan Boko Haram a kauyukan Ma’allasuwa da Yaga-Munye a jihar Borno. Wanda a ciki ta bayyana cewa ta tarwatsa maboyar yan kungiyar da ceto mata 29, kananan yara 25.

Rundunar ta bayyana hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar soji, Kanal Sagir Musa- wayewar garin jiya, wanda ya shaidar da cewa dakarun su sun samu wannan nasara ba tare da fafata wa da mayakan ba; yayin da maharan suka ji labarin zuwan sojojin ne shi ne sai suka ranta a na kare, lamarin da ya jawo suka bar mutane 54 wadanda suke garkuwa dasu, da jimawa.

Kanal Sagiru ya kara da cewa, adadin mutanen da rundunar ta kubutar din sun kunshi mata 29, sai kuma kananan yara 25, wadanda yanzu haka suke kula dasu tare da cewa nan gaba kadan zasu sada su da iyalan su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!