Connect with us

RAHOTANNI

CITAD A Bauchi Ta Horas Da Mata 40 Ilmin Kasuwanci A Kafofin Sadarwar Zamani

Published

on

Malam Ahmad Abdullahi Yakasai shine mukaddashin shugaban kungiyar ta CITAD a matakin kasa inda cikin jawabin sa ya bayyana cewa za a horas da matan yadda za su rika amfani da fasahar sadarwa irin ta zamani wajen inganta kasuwanci ta yanar gizo don tallata kayayyakin da suke sarrafawa. Horon zai ilmantar da su yadda za su kare kai daga cin zarafi ko zage zage ko muamala maras amfani ta hanyoyin sadarwa irin na zamani.

Don haka Ahmed Yakasai ya bayyana cewa hanyar sadarwa irin ta zamani wurine da mutane za su amfana a dukkan hidimomin su ya kuma kasance sun amfana ta hanyoyin kasuwanci da ilmantarwa. Saboda haka ne kungiyar ta CITAD ta shirya wannan taron bita inda za ta ilmantar da mutane da dama a karkashin wannan shiri don su amfana.

Wata wacce ta ci gajiyar shirin Aisha Ishak wacce mai larurar nakasa ce bata iya tafiya, ta bayyana cewa a yanzu tana karatu a kwalejin ilmi ta Kngere a Bauchi wannan don haka bitar za ta taimake ta wajen ganin ta samu nasara kan karatun ta da kuma shigar da kanta harkokin kasuwanci irin na zamani saboda kar ya kasance tana zaune ana ganin nakasar ta ya sat a zamo bata da amfani ga al’umma da kuma kanta.

Har wa yau wakilin mu ya zanta da Hauwa Abubakar daya daga cikin wadanda aka horas inda ta bayyana jin dadin ta, musamman ganin sama da mutane dubu suka nemi wannan dama ta samun horo amma sunan ta ya fita cikin kalilan da suka samu nasarar shiga. Don haka ta bayyana cewa za ta yi amfani da abin da ta koya wajen tallata kayan kasuwancin ta a yanar gizo musamman ganin tana sayar da kayan adon mata don haka ta ke ganin zata amfana da wannan horo da aka basu wajen fadada kasuwancin ta.

Mohammed Chiroma Hassan shine jami’in sadarwa na kungiyar ta CITAD a Bauchi ya bayyana cewa akwai hanyoyi da dama da mutane za su amfana ta fannin sadarwa irin ta zamani amma saboda mutane basu damu da yin rijista da hukumomin da suka dace ba basa samun shiga. Don haka ya bayyana cewa za su ci gaba da horas da mutane don ya zamanto sun amfana da hanyoyin sadarwa irin na zamani kamar su facebook da Twitter da makamanta su.

Saboda ta wannan hanyace za a kawar da hankulan mutane yin abin da bai dace ba ta kafofin sadarwa irin na zamani zuwa ga hanyoyin da za su amfana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!