Connect with us

RAHOTANNI

Dalibin Jami’ar Nsukka Ya Halaka Kansa Da Maganin Kwari

Published

on

Wani dalibi mai matakin karatu 400 a jami’ar Nijeriya da ke Nsukka (UNN) da ke tsangayar koyon yaren Turanci mai suna Chukwuemeka Akachi a ranar Litinin ne aka yi zargin ya kashe kansa da kansa kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.

Mai Magana da yawun Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Ebere Amaraizu shine ya tabbatar wa kamfanin dillacin labarai ta kasa aukuwar wannan lamarin a jiya, inda yake mai shaida lamarin da cewar abu ne mai ban haushi da takaici.

Amaraizu yake cewa, “Wani dalibin jami’ar UNN da ke matakin karatu na 400 a tsangayar koyon Engilishi a ranar Litinin ne ya kashe kansa.

“Binciken kan lamarin ‘yan sanda suka kaddamar domin tabbatar da musabbin lamarin,” Kamar yadda ya shaida.   

Wani ganau ya shaida cewar Akachi ya garzaya zuwa wani ginin da ba kai ga kammalawa ba da ke layin Sulliban a Nsukka inda ya samu kwalbar maganin kwari ya kwankwada domin ya kashe kansa amma da fari suma ya fara yi kamar yadda wanda ya ga lamarin ya shaida.

Ya shaida cewar marigayin dai ya samu agajin wadanda suke wucewa kan hanyar inda suka yi kokarin kaisa zuwa asibitin UNN domin samar masa da lafiya.

Daga bisani da jikin ya yi tsanani an kuma hanzarta da shi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Ituku da ke Ozalla a jihar Enugu, inda aka tabbatar da mutuwarsa a can a lokacin da likitoci suke duba shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!