Connect with us

LABARAI

DR. ZAINAB BAGUDU TA KADDAMAR DA SABON GIDAN MARAYU A ZURU

Published

on

Wakilanmu sun ruwaito mana cewa Mai Dakin Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta kaddamar da wani katafaren gidan marayu da gwamnatin jihar ta gina, mai suna Darul-Qur’an a cikin garin Zuru dake jihar ta Kebbi a ci gaba da irin jinkan mutane da ta jima take yi.
Nazari ya nuna cewa dalilin assasa ginin na sabon gidan marayun kuwa ya samo asali ne kusan shekaru biyu da suka gabata a yayin da Dr. Zainab Bagudu, wacce ake yi ma ta lakabi da Uwar Marayu, ta kai ziyarar musamman a garin na Zuru, inda ta ziyarci wani gidan marayun, har ta gano cewa mazaunin nasu ya yi mu su kadan. Gabanin assasa ginin, kamar yadda wakilanmu suka tabbatar mana cewa matar gwamnan ta fara ne da nusar da ma’aikatar walwalar mata da ci gaban al’umma, wacce dama ita ce ya kamata ta rika kula irin wadannan matsalolin.
Har ila yau kuma, ganin irin himma da kwazonta ya sanya wani bawan Allah mai suna Alhaji Samaila Fakai ya bayar da gudummawar fulotin fili, a yayin da matar gwamnan ta ba wa gwamnatin Jihar Kebbin shawarar gina gidan a kan zunzurutun kudi Naira Milyan 15, wanda aka yi amfani da shi wajen tabbatar da ginin da kuma dimbin kayayyakin da aka zuba a ciki.
A yayin da take mayar da jawabi, Matar Gwamnan kuma Khadimatud-Deen, Dakta Zainab ta fara ne da gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba wa Maigidan Gwamna Abubakar Atiku Bagudu damar jajircewa gami da tsayin dakar tabbatar an gudanar da aikin cikin nasara.
Ganau ya tabbatar wa wakilanmu cewa an dai kawata ginin da dakunan maza da mata, sannan kowane sashe yana da ban-daki guda biyu. Ya kara da cewa akwai kuma rijiyar burtsatsai, da injin wutar lantarki da dai sauransu.
A wajen taron kaddamar da Darul-Qur’an din dai marayun sun karanto wasu ayoyi daga cikin Alkur’ani mai tsarki, inda matar gwamnan ta karrama su da kyaututtuka da dama.
A nata jawabin kuwa, Kwaminishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma, Hajiya Dahara Bawa ta bayyana cewa tana matukar alfahri da gina a wannan gidan a karkashin jagorancinta. Don haka ta godewa matar gwamnan Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, bisa jagoranci nagari da take yi ta kuma yi fatan Allah ya saka mata.
A yayin jawabinsa na godiya, shugaban gidan marayun na Darul-Qur’an, Malam Umar Rabida ya bayyana cewa an samar da gidan marayun shekaru 18 da suka gabata kuma ba su taba samun tallafi daga gwamnati ba sai a wannan lokacin. Don haka ya godewa Gwamna da matarsa bisa wannan kulawa da suka yi wa marayu musamman a wannan wata na Ramadan.
Shi kuwa Sheikh Ja’afar Umar da ya kaddamar da bude gidan da hannayensa masu albarka, ya gabatar da karatun Alkur’ani yayin da Malama Safiya Abubakar ta gudanar da tafsiri.
Wakilanmu sun ce bayan nan ne tawagar matar gwamnan suka ziyarci Sarkin Zuru Alhaji Muhammad Sani Sami Gomo domin girmama shi da kuma samun tabarraki.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!