Connect with us

KASUWANCI

Faduwar Danyen Mai Ya Shafi Dala Tiriliyan 1.9 Da Yakamata A Raba Wa Jihohi

Published

on

Sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya, hakan ya shafi kwamitin Asusun tarayya na rabar da kudi FAAC, ganin cewar, abinda da kwamitin ya rabar daga watan Janairu zuwa watan Maris na shekarar 2019 ya ragu zuwa dala tiriliyan 1.929 sabanin naira tiriliyan 1.938 ds kwamitin ya rabar a shekarar 2018, inda hakan ya kai kashi 0.45 na ragin ds aka samu.

Wannan bayannin yana kunshe ne a cikin bayanan kwanan nan na sabuntawar da Hukumar dake sanya ido akan Masana’antu NEITI.

Acewar rahoton, jimlar kudin da FAAC ya rabar a zango na daya na shekarar 2019 an kare ta akan sama da naira tiriliyan biyu da aka rabar da suka kai tsawon zanguna uku na biyu dana hudu a shekarar 2018.

A bisa fashin bakin da akayi rabar da kudin, ya nuna cewar, Gwamnatin Tarayya ta karbi naira biliyan 803.18 a zangon farkon wannan shekarar. Wannan ya kai kasa da kashi 1.18 na naira biliyan 812.8 da Gwamnatin Tarayya ta karba a cikin shekarar 2018 sama da kashi 46.2 fiye da naira biliyan 549.1 da aka rabar a shekarar 2017.

Har ima yau, a dogon faahin bakin da akayi ya nuna cewar, jihohi 36 sun raba naira biliyan 675.2 a zangon farko na wannan shekarar, inda hakan ya kai kashi 1.19, inda ya ragu akan naira biliyan 683.4 da aka rabarwa jihohi a zangon farko na shekarar 2018, amma ya haura kashi 48 bisa dari na naira biliyan 456 da aka rabar a zangon farko na shekarar 2017.

Daga sabuntarwar da akayi, naira biliyan 398.44 kacal aka rabarwa da kananan hukumomi a zangon farko na shekarar 2019, wanda ya haura kashi 1.28, idan aka kwatanta da naira biliyan 393.4 da aka rabar a zangon farko na shekarar 2018 da kuma kashi 47.8 sama da wanda aka rabar a farkon zangon shekarar 2017.

Bugu da kari, a bisa nazarin da Hukumar NEITI ta yi, ta danganta ragin da aka samu daga kwamitin na FAAC na rabar da kudin akan farashin na danyen mai

An samu raguwar farashin a watan Nuwambarsshekarar 2018.

Farashin na man sama da dala 80 na gangar mai a cikin watan Okutobar shekarar 2018, amma a watan Disambar 2018, sun ragu zuwa ganga 57.

Yawan faraahin man a zangon farko na shekarar 2019 ya kai ganga 63.17.

Yawan farashin man a shekarar 2018 ya kai ganga 71.06.

Sai dai, ya yi kasa a zango na farko a cikin watanni uku na shekarar 2019 kamar yadda yake a shekarar 2018.

A bisa nazarin da Hulumar ta NEITI yi na kwanan nan, ta yi hasashen ci gaba da samun karuwar rabawar na shekarar 2019 a bisa tsimayin da akayi na sarrafa danyen man da kuma farashin sa na cewar, zaici gaba da hawa.

Har ila yau, Hukumar ta NEITI a sabuntawar da tayi ta nuna cewar, kasafin kudi na wannan shekarar da tuni johohi 35 suka gabatar, bazasu wadaci jihohin ba harda wanda kwamtin na FAAC ya rabarwa da ko wacce jiha a shekarar 2017 da kuma shekarar 2018.

Bugu da kari, a cikin sabuntawar da Hukumar ta NEITI ya nuna cewar, jimlar kudin shiga daga kwamitin na FAAC da kuma wanda ake tarawa a cikin jihohin a shekarar 2017 da shekarar 2018 bazasu isa su biya bukatun kasafin kudi na shekarar 2019 na jihohi 28.

Acewar Hukumar NEITI, babu wata jiha da kudin da kwamitin na FAAC ya rabar a shekarar 2017 ko a shekarar 2018 da zsi wadaci kasafin kudin su na shekarar 2019, ind kuma wanda aka rabarwa da jihohin a shekarar 2017 ya kai na kasafin kudi na shekarar 2019 da ya kai daga kashi 2.25 bisa dari na jihiar Koros Ribas da kashi 43.1 bisa dari na jihar Yobe.

Har ila yau, wanda aka turawa jihohi a shekarar 2018, dana kasafin kudi na shekarar 2019 daga kashi 3.54 na jihar Koros Ribas da kashi 57.7 na jihar Yobe.

Hakan ya nuna a zahiri, babu wata jiha da zata iya zuba kudi a cikin kasafin kudn ta na shekarar 2019, kawai dan dogaro akan kudin da kwamtin na FAAC yake rabawar masu.

Gibin da kudin da aka samu a kwamitin na FAAC na kudin da yake rabawarwa, mafi yawancin jihohin sun dogara ne akan ciwo bashi don habaka kudaden shigar su na cikin gida na IGR.

Bugu da kari, Hukumar ta NEITI ta zayyana jihohi uku kacal dake da karfin kudin da suke tarawa a cikin gida da ya, jihohin sune, Legas, Ribas da kuma Ogun.

Har ila yau, Hukumar NEITI tace jihar Yobe itace jiha kadai da zata iya zuba kudi a cikin kasafin kudin ta na shekarar 2019 tare da wanda ta karba daga gun kwamitin na FAAC daga shekarar 2017 zuwa shekarar 2018.

Hukumar ta kuma zayyana jihohin Enugu, Kaduna, Delta, Yobe, Lagos, Kano, Nasarawa da Ribas a tsakanin jihohin da zasu iya zuba kudi a cikin kasafin kudinsu daga jimlar kudin shiga daga shekarar 2017 zuwa shekarar 2018.

Akan shiyar ta FAAC da take rabwarwa jihohi 36, Hukumar ta NEITI ta nuna akwai banbanci, alal misali, jihar Delta ta karbi kaso mai yawa da ya kai naira biliyan 55.19, inda jihar Osun ta karbi naira biliyan 5.11, inda hakan ya nuna ya kai kashi 980 na banbancin da aka samu

An kuma cire bashin naira biliyan 7.27 kai tsaye daga kudin da aka warewa jihar Osun, inda kuma jihar Koros Ribas aka cire mata kashi 53 daga kason da ake bata.

A bayanin na Hukumar ta NEITI na kwanan nan, ta gargadi matakan gwamnati na uku dake kasar nan dasu dinga lura da yadda suke kashe kudaden su da kuma kaucewa dogaro akan ribar mai don zubawa a cikin kasafin kudin su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!