Connect with us

LABARAI

Ganduje Ya Bai Wa Wadanda Suka Kubuta Daga Hukuncin Kisa A Saudiyya Naira Miliyan Uku

Published

on

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, a yau Laraba ya bai wa wadanda suka kubuta daga hukuncin kisa a Saudiyya naira miliyan uku. Wadanda suka amfana daga kudin sun hada da Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar.

Ganduje ya bayyana wannan kyautar da ya yi ne a yayin da tawagar gwamnatin tarayya mika Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar ga gwamnan a gidan gwamnatin jihar.

‎Ganduje ya ce Zainab Aliyu wacce ta je Umurah kasar Saudiyya a shekarar 2018, an kama ta ne a Otel dinta a garin Madinah bisa zargin safarar kwaya zuwa kasar Saudiyya. Hakazalika, shima Ibrahim Abubakar, an kama shi ne a ranar da aka kama Zainab Aliyu bisa wannan zargin.

Gwamnan ya mika naira miliyan uku ga kowannensu, inda ya jinjinawa shugaban kasa Buhari bisa kokarin da ya yin a ceto rayukan ‘yan kasa guda biyu. Inda kuma ya yi kira ga jami’an tsaron da ke aiki a filin jirgin Malam Aminu Kano da su sanya ido sosai wajen ganin an magance irin wadannan matsalolin.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!