Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Karin Haske Kan Lokacin Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi

Published

on

A ranar Talata ce a Abuja, gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin shirya yanda za a fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 30,000, kimanin wata guda da shugaban kasa Buhari ya sanya hannu a kan dokar. Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ne ya fadi hakan a sa’ilin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gidan Talabijin a kan ko yaushe ne za a fara biyan sabon mafi karancin albashin.

Ngige, bai bayyana karara ko a yaushe ne gwamnatin za ta fara biyan sabon mafi karancin albashin ba, amma dai ya ce za a biya ariya a duk lokacin da aka fara biyan sabon mafi karancin albashin. Ya ce, har yanzun akwai sauran matakan da suka kamata a bi tukunna kafin a fara biyan sabon mafi karancin albashin, duk da cewa an sanya hannu a kan dokar.

“Duk matakai ne da hukumar kula da albashi da kudaden alawus ya kamata ta yi aikinta a kansu kafin a fara biyan sabon mafi karancin albashin,” in ji Ministan. Ya ce, kwamitin da gwamnatin ta kafa ya kunshi Ministoci Bakwai ne, a inda shugabar ma’aikata na kasa, Winifred Oyo-Ita, take a zaman shugabar kwamitin. Ministan ya ce, kananan ma’aikata na can kasa wadanda suke aiki a gwamnati ko a kamfanoni masu zaman kansu su ne za su kwashi albashin Naira 30,000, kamar yanda dokar ta tanada.

Sai dai ya ce, ga ma’aikatan da albashin su yake sama da sabon mafi karancin albashin, za su sami kari ne a daidai matakan da suke a kai daga sama zuwa kasa. Ngige, ya kara da cewa, sauran hukumomin gwamnati za su fitar da takardun doka kwanan nan a kan karin da aka samu. A yanzun haka dai, shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Mista Ayuba Wabba, ya nuna damuwarsa a kan jan kafar da ake yi wajen fara aiwatar da dokar ta sabon mafi karancin albashin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!