Connect with us

RAHOTANNI

Hadaddiyar Kungiyar Musulmi Aa Legas Ta Fara Ziyatar Gidajen Yari Da Asibitoci

Published

on

Hadaddiyar kungiyar al’ummar Musulmi a jihar Legas mai suna Al-Birru Watta Awun a Nijeriya ta fara ziyarce-ziyarce gidajen yari da asibitocin da ke cikin garin Legas, wanda kungiyar ta saba yi a daidai wannan lokaci na watan azumin Ramadan na kowace shekara.

Kungiyar mai hedikwata a lamba 303 kan titin Brass a Marine Beach da ke Apapa ta jihar Legas,

shugabanta Malam Ahmed Ibirahim Agbomalu ya ce, su na gudanar da wannan ziyarce-ziyarce ne a duk shekara idan watan azumi ya kama domin bai wa ‘yan fursuna tallafin abinci da suturar sawa a duk fadin jihar.

Ya kara da cewa, ko a ranar Lahadin da ta wuce kungiyar ta kai irin wannan tallafi gidan yarin Badagiri da ke cikin garin Legas, inda ta kai tallafin kayan abinci, wadanda a ka kiyasta kudinsu ya kai sama da Naira miliyan daya.

Tawagar wannan kungiyar da ta gudanar da wadannan ziyarce-ziyarce a gidan yarin Badagiri sun hada da sarakunan al’ummar Hausawa mazauna garin Badagirin da ke Same Boda da shugabannin kungiyar ta Al-Birru Watta Awun da malamai da sauran wadansu Al’ummar Hausawa mazauna Legas.

Sakataren kungiyar Haruna Zubairu Haruna shi ne ya gabatar da malamai irinsu Malam Ahmed Zakariya da Sheikh Malam Ahmed, domin su gudanar da wa’azi ga ‘yan fursunan da kuma bayyana abubuwan da su ka wajaba a kan al’ummar Musulmi.

A jawabin daya daga cikin sarakunan da su ka rufa wa kungiyar baya a ziyara ta bayar da tallafin abinci ga mutanen da ke tsare a  gidan yarin Badagiri Sarkin Hausawan Same Boda, Mohammed Fesal Aliyu Maigilas ya cigaba dacewar wannan kungiyar ta koya masu tare da zaburar da su a kan hanyar gudanar da ayyukan alheri a cikin watan azumin Ramadan, sannan ya kara da kira ga masu hannu da shuni da su cigaba da tallafa wa wannan kungiyar domin ta cigaba da tafiya kafada da kafada a wajen gudanar da ayyukan alheri.

Da ya ke jawabinsa na farin cikin wannan ziyarar shugaban gidan yarin na Badagiri, Mr. Ittani John ya yiwa wannan kungiyar godiyar tare da shi albarka ga shuwagabannin kungiyar a game da wannan tallafin kayan abinci da su ka kawo wa wannan al’ummar a gidan yarinsa na Badagiri.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!