Connect with us

KASASHEN WAJE

Harin Bam Ya Jikkata Mutum 10 A Indiya

Published

on

Akalla mutum goma suka jikkata sakamakon wani harin bam da ya tashi a gabashin arewacin garin Assam na kasar Indiya. Lamarin ya auku ne a yau Laraba kamar yadda jami’an tsaron kasar suka tabbatar.

Jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa har ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin. Inda suka kara da cewa; “harin bam ne aka kai wa jami’an tsaro a yayin da suke gudanar da aikinsu a yankin.” Inji Deepak Kumar, Kwamishinan ‘yan Sandan Assam dake Guwahati.

An ta da bam din ne a titin Guwahati da misalin karfe 8 na dare agogon can. Inda ‘yan sanda biyu da farar hula takwas suka jikkata. Rahotanni sun tabbatar da cewa an sanya bam din ne a cikin wadansu motoci guda biyu.

Babban Ministan Assam Sarbananda Sonowal ya yi Allah-wadai da wannan harin. Inda ya nemi hukumomi da su tabbata sun kamo wadanda suke da hannu wajen kai wannan harin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!