Connect with us

Da dimi-diminsa

Kano: Kotu Ta Rushe Sabbin Sarakuna Nadin Ganduje

Published

on

A yau ne wata kotun jihar Kano da ke zama a Ungogo ta rushe sabbin Sarakunan da Gwamna Ganduje ya nada a qarshen makon da ya gabata.

A zaman kotun na ranar Larabar makon da ya gabata, Mai Shari’a Nasiru Saminu ya umurci dukkanin wadanda ke cikin kitimurmurar da su tsagaita daga daukar kowanne irin mataki har zuwa ranar 10 Ga watan Mayu yayin da kotu za ta saurari shari’ar.

Sai dai kuma, a ranar 10 Ga watan Mayun ne Gwamna Ganduje ya bijirewa umurnin kotun inda ya mika takarda daukar aiki ga sabbin sarakunan da gwamnatinsa ta samar.

Haka kuma a tsakankanin ranakun 11 da 12 ga watan Mayun Gwamnan ya mika sandar mulki ga sabbin sarakunan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!